2025-11-05@15:28:57 GMT
إجمالي نتائج البحث: 8752
«Kwale kwale»:
Zulum Ya Raba Motocin Sintiri 63 Don Yaki da Laifuffuka A Maiduguri Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya mika motocin sintiri 63 ga hukumomin tsaro da kuma Rundunar Hadin Gwiwa ta Farar Hula (CJTF) da ke aiki a Maiduguri da kewaye. Daga cikin motocin 63, an ba da motocin 30 ga sassa daban-daban na...
Haka kuma, daga ranar 10 ga watan Nuwamba, kasar Sin za ta soke matakin da ta dauka a kan wasu kamfanonin Amurka a cikin jerin kamfanoni marasa aminci da ta sanar a ranar 4 ga Maris na wannan shekara, kamar yadda wani mai magana da yawun ma’aikatar ya bayyana a cikin wata sanarwa. ...
Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya raba wa hukumomin tsaro da rundunar haɗin gwiwa ta CJTF kyautar motoci 63 don inganta tsaro a Maiduguri. Daga cikin motocin, an bai wa rundunar CJTF guda 30, jami’an tsaro 16, ƙungiyoyin tsaro 10, mafarauta shida, sannan aka bai wa hukumar NAPTIP guda ɗaya. Abba ya yaba...
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yaba wa rundunar sojin Najeriya da sauran jami’an tsaro bisa daƙile hare-haren ’yan bindiga a wasu sassan jihar. Mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar. Kocin Super Eagle ya lashi takobin lashe kofin nahiyar Afirka Mamdani...
Jami’an Rundunar ’Yan Sandan Jihar Edo sun kama wata mata mai suna Chioma Success mai shekaru 27, bisa zargin kitsa garkuwa da kanta don karɓar kuɗin fansa daga mijinta. An kuma kama wasu mutum biyu da ake zargin sun taimaka mata wajen aikata laifin, wato Martins Chidozie mai shekaru 23 da Osita Godfrey mai shekaru...
Kungiyoyin agaji da dama na kasashen duniya sun yi gargadin cewa tallafin da ake bai wa yankin Gaza bai isa ba kusan wata guda bayan da aka fara aiki da yarjejeniyar tsagaita wuta, yayin da yankin ke ci gaba da fuskantar matsalar abinci da matsugunai yayin da hunturu ke gabatowa. A cikin wata sanarwa da...
China ta yi alkawarin ci gaba da tallafawa Najeriya bayan barazanar da Amurka ta yi na janye tallafi da kuma daukar matakin soja kan kasar da ke Yammacin Afirka saboda zargin cewa ana cin zarafin Kiristoci. A kwanan nan ne Shugaban Amurka Donald Trump ya yi ikirarin cewa Kiristoci na fuskantar “barazana” a Najeriya, yana...
Ya ƙara da cewa wannan mataki wani ɓangare ne na gyaran tattalin arziƙi da kuma dawo da amincewa ga tsarin kwangilolin gwamnati. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai ECOWAS Ta Ƙaryata Iƙirarin Trump Kan Kisan Kiristoci A Nijeriya November 5, 2025 Da ɗumi-ɗuminsa Tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Ya Rasu Yana Da Shekaru...
Zohran Mamdani ya lashe zaben Magajin Garin birni mafi girma a Amurka wato New York, kuma zai zama Musulmi na farko a tarihi da ya taɓa shugabantar birnin. Mamdani, mai shekara 34 kuma dan jam’iyyar Democrat mai ra’ayin gurguzu, ya samu nasara bayan ya motsa masu ra’ayin sauyi a cikin birnin da ma fadin ƙasar,...
Daga Khadijah Aliyu An fara shirye-shirye gudanar da taron shekara-shekara karo na 2 da bikin shigar da sabbin mambobi na Ƙungiyar Masana Harkokin Yada Labarai ta Najeriya (SNB), bayan an kaddamar da Kwamitin Shirya Taron (LOC) a Kano. An tsara gudanar da taron ne daga ranar 20 zuwa 21 ga watan Nuwamban 2025. Shugaban Ƙungiyar,...
Kungiyar Likitoci Mata ta Najeriya (MWAN) reshen Jihar Gombe, tare da hadin gwiwar Hukumar Ci gaba ta Arewa maso Gabas (NEDC), za su gudanar da gwaji kyauta na gano cutar sankarar nono da ta mahaifa ga mata fiye da 500 cikin tsawon kwanaki uku. Wakiliyar kungiyar MWAN, Dr. Hauwa Saurayi, ce ta bayyana haka a...
Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kwara ta ceto mutane uku da aka yi garkuwa da su ba tare da wata illa ba, a kauyen Igbonla. A cikin wata sanarwa da Jami’ar Hulɗa da Jama’a ta rundunar, SP Adetoun Ejinre-Adeyemi, ta fitar, ta ce rundunar ta samu kiran gaggawa cewa wasu ’yan bindiga sun kutsa cikin...
Wasu da ake zargin ‘yan bindiga sun kai hari kan ayarin dan majalisar tarayya mai wakiltar Mazabar Agwara/Borgu a Jihar Neja, Honarabul Jafaru Mohammed Ali. Rahotanni sun bayyana cewa harin ya faru ne a jiya, a kauyen Kubul, kan hanyar Agwara zuwa Babana, a cikin Karamar Hukumar Borgu, yayin da dan majalisar ke hanyarsa ta...
Gwamnatin Jihar Nasarawa ta ce ta samu amincewar gwamnatin tarayya domin gina sabbin gada biyu na sama da kuma ta karkashin kasa (under-pass) a yankin Mararaba da ke Karamar Hukumar Karu. Babban Mataimaki na Musamman ga Gwamna Abdullahi Sule kan Harkokin Jama’a, Mr. Peter Ahemba, ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da...
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya jinjinawa rundunar Sojojin Najeriya da sauran hukumomin tsaro bisa gaggawar daukar mataki kan hare-haren ‘yan bindiga da suka faru a wasu sassan jihar. Gwamnan ya yi wannan yabo ne a lokacin da Babban Hafsan Runduna ta 1, wato GOC 1 Division da ke Kaduna, Major Janar Abubakar...
Kwamishinan Habbaka kiyon Dabbobi na Jihar Kano, Dr. Aliyu Isa Aliyu, ya fara ziyarar wayar da kan jama’a kan muhimmancin zaman lafiya tsakanin manoma da makiyaya a kananan hukumomin Ajingi da Dawakin Tofa. Ziyarar ta yi daidai da shirin gwamnati na kaucewa rikici, musamman sakamakon yuwuwar shigowar makiyaya daga Jamhuriyar Nijar cikin jihar. A Ajingi,...
Shugaban Juyin Juya Halin Musulunci Ayatollah Seyyed Ali Khamenei ya ce sabanin da ke tsakanin Iran da Amurka “babban abu ne” kuma ya samo asali ne daga rikicin muradun kasa, yana mai gargadin cewa hadin gwiwa da Amurka zai yiwu ne kawai idan ta kawo karshen goyon bayan da take bai wa Isra’ila, ta janye...
Rahotanni sun nuna cewa shugaban kungiyar gwagwarmaya ta Hamas Musa abu marzuk ya shaidawa gidan talabijin din Aljazeera cewa sun yi watsi da batun tura dakarun tabbatar da zaman lafiya zuwa yankin Gaza wadanda zasu yi aiki a madadin sojojin mamayar Isra’ila Yace ba zamu taba amincewa da aikewa da sojojin da za su zama...
An yi musayar yawu a zauren Majalisar Dattawa a ranar Talata yayin da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin da Shugaban Majalisar, Sanata Godswill Akpabio, kan zargin Shugaban Amurka, Donald Trump, na yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Najeriya. Zaman majalisar ya biyo bayan sanarwar Trump da ke bayyana Najeriya a matsayin “Ƙasa Mai...
Dakta Bukar ya bayyana wannan hadin gwiwar a matsayin abu mai muhimmanci wanda yazo a kan gaba wajen karfafa wayar da kan jama’a game da rawar da sahihan bayanai suke takawa wajen tsara ci gaba da samar da manufofi masu tushe , da dorewar cigaban kasa. Dakta Bukar, ya jaddada muhimmancin hadin gwiwa da...
Ƙungiyar Tarayyar Turai ta EU ta ce ta fahimci cewa ba addini ne kaɗai ke haifar da rikice-rikice a Najeriya ba. Jaridar Vanguwar ta ruwaito wata sanarwa da mai magana da yawun ƙungiyar kan harkokin ƙasashen ƙetare, Anouar El Anouni ya fitar, yana cewa ƙungiyar EU na jajanta wa mutanen da rikicin ya rutsa da...
Cibiyar kandagarki da dakile cututtuka masu yaduwa ta Sin (CDC) ta fara kwas din horon fasahar gwaje-gwaje a kasashen waje a ranar 3 ga wata a hedkwatar CDC ta Afirka. Masana daga gwamnatocin Sin da Afirka da fannin kiwon lafiya, da kuma dalibai 30 daga kasashen Afirka 16, sun halarci bikin bude horon. An...
Shahararren ɗan wasan tseren motoci, Jenson Button, ya bayyana cewa gasar tseren Bahrain na sa’o’i takwas da za a gudanar a ƙarshen mako, ita ce za ta zama ta ƙarshe da zai yi a wasannin ƙwararru na tseren motoci. Button ɗan asalin kasar Birtaniya, wanda yake da shekaru 45, ya shafe shekaru biyu da suka...
Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta bayyana cewa ta sallami jami’anta fiye da 100 a tsakanin shekarar 2024 zuwa 2025, a wani yunƙuri na aiwatar da gyare-gyare a cikin hukumar. Cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata, DSS ta ce jimillar jami’ai 115 ta sallama daga aiki saboda dalilai daban-daban da suka...
Shahararren ɗan wasan tseren motoci, Jenson Button, ya bayyana cewa gasar tseren Bahrain na sa’o’i takwas da za a gudanar a ƙarshen mako, ita ce za ta zama ta ƙarshe da zai yi a wasannin ƙwararru na tseren motoci. Button ɗan asalin kasar Birtaniya, wanda yake da shekaru 45, ya shafe shekaru biyu da suka...
Daga Shamsuddeen Mannir Atiku Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta amince da dokar kafa Hukumar Fasahar Sadarwa da Tattalin Arzikin na Zamani ta Jihar Kaduna, wacce za ta taimaka wajen ƙarfafa tsarin fasaha na jihar da inganta gasa a fannin tattalin arziki. Dokar mai taken “Kaduna State Information Technology and Digital Economy Agency and for Related...
Sin Na Goyon Bayan Najeriya Wajen Jagorantar Al’ummarta Zuwa Hawa Turbar Neman Ci Gaba Daidai Da Yanayin Kasar
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta yi tsokaci game da matakin Amurka na sanya Najeriya cikin jerin kasashen da ake da damuwa a kansu, inda ta jaddada matsayin Sin na matukar goyon bayan gwamnatin Najeriya, wajen jagorantar al’ummarta zuwa turbar neman ci gaba bisa yanayin da kasar ke ciki. A ’yan kwanakin...
Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Yusuf Maitama Tuggar, ya gargaɗi Shugaban Amurka Donald Trump, kan kada ya ƙirƙiri wata Sudan ɗin a Najeriya bayan zargin da ya yi na cewa ana yi wa Kiristoci kisan kiyashi a ƙasar. Mista Tuggar, wanda ya yi jawabi a taron manema labarai a birnin Berlin tare da takwaransa na ƙasar...
Sanata Ali Ndume ya ce jahiltar halin da Najeriya ke ciki ne ya sa Shugaban Amurka Donald Trump ya yi iƙirarin cewa ana kisan Kiristoci a ƙasar. Ndume, wanda ke wakiltar mazabar Borno ta Kudu a Majalisar Dattawa, ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Arise...
Shugaban Jam’iyyar APC a Jihar Kano, Yarima Abdullahi Abbas, ya bayyana cewa, jam’iyyarsa za ta yi duk mai yiwuwa don tabbatar da cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jam’iyyar NNPP bai dawo kan mulki ba a babban zaben 2027. A cikin wani gajeren faifan bidiyo da ke yawo a Facebook, an ga Abbas yana jawabi...
A yau Talata ne firaministan Sin Li Qiang, ya gana da kakakin majalisar wakilan tarayyar Najeriya Tajudeen Abbas, wanda ya isa birnin Shanghai don halartar baje kolin CIIE karo na takwas. Yayin zantawarsu, Li Qiang ya bayyana aniyar kasar Sin ta karfafa salon wanzar da ci gaba bisa manyan tsare-tsare tare da Najeriya, da zage...
Dan wasan gaban Paris Saint-Germain (PSG) ɗan asalin ƙasar Faransa, Ousmane Dembele, zai kasance cikin tawagar da za ta fafata da Bayern Munich a wasan Champions League da za a buga yau Talata. Dembele, wanda ya zura ƙwallo a wasan da PSG ta doke Bayern Munich da ci 2–0 a gasar Club World Cup zagaye...
Majalisar Wakilai ta dakatar da zamanta na tsawon mako guda, sakamakon zanga-zangar da wasu ’yan kwangila suka gudanar a ƙofar shiga ginin majalisar dokoki ta ƙasa da ke Abuja, saboda rashin biyan kuɗaɗen ayyukan da suka kammala tun shekarar 2024. Rahotanni sun ce ’yan kwangilar sun yi dandazo ne a ƙofar shiga majalisar a ranar...
Kakakin Dakarun Kare Juyin Juya Halin Mususluni na bayyana yaƙin kwanaki 12 kan Iran ya tabbatar da cewa ba za a taɓa amincewa da Amurka ba Kakakin Rundunar Tsaron Juyin Juya Halin Musulunci (IRGC) ya tabbatar da cewa: Yakin kwanaki 12 da aka yi da Iran ya nuna rashin amana ga masu yanke shawara na...
Shugaban Majalisar Dokokin Lebanon ya bayyana cewa; Gwagwarmaya ta tilastawa gwamnatin mamayar Isra’ila rashin girke sojojinta a kan iyakar da ke tsakanin Isra’ila da Lebanon Kakakin Majalisar Dokokin Lebanon Nabih Berri ya tabbatar da cewa: “Gwagwarmaya ta yi cikakken biyayya ga sharuɗɗan yarjejeniyar tsagaita wuta, kuma sojojin Lebanon sun tura sojoji da jami’ai sama da...
Ana Tattara Gawawwakin Mutanen Da Mayakan Rapid Support Forces Suka Kashe A Arewacin Kordofan Na Sudan
Ana ci gaba da tattara gawarwakin mutane da mayakan kungiyar Rapid Support Forces ta Dakarun Kai DaukinGaggawa suka kashe a jihar Arewacin Kordofan na kasar Sudan. Kungiyar Likitoci na Kasar Sudan ya ruwaito cewa: Ana ci gaba da tattara gawawwakin mutane a Arewacin Kordofan, bayan da mayakan Rappid Support Forces suka farma yankunan a kokarin...
Wata Babbar Kotu da ke zamanta a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo, ta sahale wa jam’iyyar PDP gudanar da babban taronta na ƙasa da aka tsara gudanarwa a ranar 15 da 16 ga watan Nuwamba, 2025, a filin wasa na Lekan Salami, Adamasingba. A hukuncin da kotun ta yanke, ta umarci jami’an jam’iyyar da wakilanta...
Yayin da yake gabatar da motocin, Gwamna Zulum ya sake nanata kudirin gwamnatinsa na samar da tallafin kayayyaki ga jami’an tsaro a kowane lokaci. Ya jaddada cewa, tsaro wani bangare ne na muhimman abubuwan da gwamnatinsa ta sa a gaba. Zulum ya kuma yaba wa Shugaba Bola Tinubu da jami’an tsaro kan kokarin...
Ƙasar China ta soki abin da ta kira yunƙurin Shugaban Amurka Donald Trump na yin katsalandan cikin harkokin cikin gida na Najeriya, inda ta bayyana cikakken goyon bayanta ga gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar, Mao Ning, ce ta bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a ranar Talata, a matsayin...
KADUNA TA ZAMA JIHAR FARKO A NIJERIYA DA TA AIWATAR DA SHIRIN SAMAR DA ABINCIN MAI GINA JIKI GA YARA – UNICEF
KADUNA TA ZAMA JIHAR FARKO A NIJERIYA DA TA AIWATAR DA SHIRIN SAMAR DA ABINCIN MAI GINA JIKI GA YARA – UNICE Daga Abdullahi Shettima. Hukumar Asusun kula da yara kananan yara ta majalisar dinkin duniya (UNICEF) ta jinjinawa gwamnatin jihar Kaduna bisa zama jihar farko a Nijeriya da ta amince kuma fara aiwatar da...
Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, Ayatollah Seyyed Ali Khamenei, ya bayyana cewa rikicin da ke tsakanin Tehran da Washington ya samo asali ne daga muradun jama’a, yana mai gargadin cewa duk wani hadin gwiwa da Amurka za a iya cimma shi ne kawai idan ta kawo karshen goyon bayan da take bai wa...
Ya ƙara da cewa yana cikin farin ciki ganin yadda Gwamna Douye Diri ya fice daga jam’iyyar, inda ya ce, “Shi da Makinde sun taɓa cewa ba za su bari a lalata PDP ba ko a jawo ta ƙasa, amma ga su yanzu; su ne suka faɗi ƙasa.” ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Kalaman...
A Tanzaniyaan rantsar da Shugabar kasar Samia Suluhu Hassan a wa’adinta na biyu bayan ta lashe zaben da ya haifar da mummunar zanga-zanga a fadin kasar. An ayyana Samia, wacce ta hau mulki a shekarar 2021 bayan mutuwar magabacinta, a matsayin wacce ta lashe zaben da aka gudanar a makon da ya gabata da kashi...
Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya (ICC) ta nuna damuwa kan rahotannin baya-bayan nan na “kasha kashe, fyade, da sauran laifuka” da Rundunar Taimakon Gaggawa (RSF) ta aikata a yankin El-Fasher, na Sudan, tana gargadin cewa wadannan ayyukan na iya zama “laifukan yaki da cin zarafin bil’adama.” “Irin wadannan ayyuka, idan aka tabbatar da su,...
Natasha ta bayyana dakatar da ita a matsayin mataki wanda ba na doka ba, tana mai cewa hakan ya nuna yadda tsoro da barazanar siyasa ke rinjayar halayen jami’an gwamnati. An dakatar da Sanata Natasha a watan Maris saboda zargin da ya shafi Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, amma ta koma kujerarta a watan Satumba...
Jami’an tsaro sun kama wani mutum da wayoyin sata guda 17 da kuma kudi a wurin taron sauyin shkear Gwamna Douye Diri daga Jam’iyyar PDP zuwa APC. A ranar taron, Gwamna Diri tare da yawancin ’yan majalisar dokokin jihar Bayelsa sun sanar da ficewarsu daga jam’iyyar PDP zuwa APC, a gaban Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim...
Ya kuma tunatar da cewa Nijeriya da Amurka na da kyakkyawar alaƙa tun da daɗewa, don haka bai kamata wannan sabuwar dambarwa ta lalata dangantakar ƙasashen biyu ba. Obi ya ce dole ne a yi amfani da diflomasiyya da tattaunawa wajen shawo kan matsalar. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Natasha Ta Zargi Akpabio Da...
Sarakunan gargajiya, lauyoyi da jami’an gwamnati sun koka bisa yawaitar kananan ’yan mata da ke daukar ciki da kuma zubar da ciki ba bisa ƙa’ida ba, a sansanonin ’yan gudun hijira da ke Maiduguri, Jihar Borno. Lamarin ya fito fili ne a wani taron tattaunawa na kwanaki biyu da ƙungiyar Grassroots Researchers Association (GRA) ta shirya...
Rashin aikin yi na daya daga cikin manyan kalubalen da najeriya ke fuskanta a wannan lokaci, musamman la’akari da yanda ake cigaba da samun matasa dake da karfi a jika amma babu aikin yi. Hukumar kididdiga ta kasa ta fitar da bayanan dake baiyana cewa rashin aikin yi ya karu a najeriya da kaso 5.3...
Prime ministan kasar sudan Kamil idris yayi gargadin cewa aikewa da dakarun tabbatar da zaman lafiya na kasashen waje a kasar Sudan zai kara ruruta wutar rikicin ne da kuma keta yancin kasar, kuma kalaman nasa suna cewa ne bayan rahoton da aka fitar game da cin zarafin dan Adam da aka yi a El-fasher...