Mun gurfanar da mutum 29 a kotu kan zargin kashe DPO a Kano – ’Yan sanda
Published: 6th, June 2025 GMT
Rundunar ’Yan Sanda ta jihar Kano ta ce ta gurfanar da mutum 29 da ta kama bisa zarginsu da hannu a kashe DPO na garin Rano da ke jihar, CSP Baba Ali da sauran laifuffuka.
Kakakin rundunar a jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ranar Alhamis, inda ya ce an gurfanar da su ne a gaban kotun majistare mai lamba 20 da ke Nomansland a Kano.
Gurfanarwar dai ta biyo bayan kammala bincike kan kisan wanda ya ja hankalin mutane a ciki da wajen jihar.
NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Suka Fara Bacewa Yayin Bukukuwan Sallah Sojoji sun dakile hare-haren ‘Yan Boko Haram biyu a BornoKiyawa ya ce 14 daga cikin mutanen, da suka hada da Bala Yusuf, Bala Mohammed, Abdulrashid Ibrahim, Abdullahi Salisu Kere, Sadiq Buhari, Yunusa Adamu, Musa Minkaila, Mamuda Mohammed, Ismail Mamuda, Usman Shu’aibu, Musa Hassan Black, Abdulrashid Munkail, Umar Ado Nadada da Sabitu Abubakar, dukkansu ’yan asalin karamar hukumar ta Ranon ne, kuma ana zarginsu da aikata kisan kai da sauran laifuffuka.
Sauran laifuffukan da ake zargin nasu da su sun hada da hadin baki, tayar da zaune tsaye, kone-kone, ketare iyaka, jikkatawa da kuma sata.
Ragowar mutum 15 din kuma wadanda su ma aka dauki bayansu a lokacin bincike ana zarginsu da hadin baki da tayar da zaune tsaye da kuma iza wutar rikici kan kisan DPOn da kuma lalata gini.
Rahotanni dai sun bayyana yadda aka kasha marigayi CSP Baba Ali a Rano, bayan mutanen gari sun zarge shi da hannu a kashe wani wanda aka tsare a ofishin ’yan sanda.
“Rundunarmu tana ba mutane tabbacin cewa za a yi adalci a wannan shari’ar, sannan tana godiya kan sakonnin ta’aziyya da addu’o’i da taimako da kuma fahimta da hadin kan da mutane suka bayar a lokacin da ake binciken,” in ji sanarwar.
Kiyawa ya kuma ce duk da an fara shari’ar wadanda suka zo hannu, rundunar ta sha alwashin gani ta ci gaba da farautar duk ragowar masu hannu a cikin aika-aikar domin ganin su ma sun girbi abin da suka shuka.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Ana zargin mace da kashe ’yar uwarta a kan N800 din barkono
Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Ondo ta tabbatar da kama wata mata mai suna Iluyemi Bosede bisa zargin kashe yayarta, Tewogboye Omowumi, a Akure, babban birnin jihar.
A cewar sanarwar da Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, Olayinka Ayanlade, ya fitar a ranar Talata, ya ce lamarin ya faru ne a ranar shida ga Satumba, 2025, bayan wata sa’insa da ta kaure tsakanin matar da marigayiyar kan Naira 800.
Tun Tinubu yana Gwamna ba abin da ya fi shahara da shi kamar tara haraji – Adebayo DAGA LARABA: Dalilan Tashin Farashin Doya A Wasu Kasuwannin NajeriyaJami’in ya bayyana cewa Bosede ta ture ’yar uwarta har ta faɗi ƙasa, lamarin da ya haifar da mutuwarta.
Ya ce, “Binciken farko ya nuna cewa Iluyemi Bosede ta je wurin yayar tata, Tewogboye Omowumi mai shekaru 35, domin karbar bashinta na N800 na kudin tumatir da barkono. Sai dai tankiyar da ta fara a matsayin ƙaramin sabani ta rikide zuwa tashin hankali, inda ake zargin Bosede ta riƙe kayan marigayiyar har ta faɗi ƙasa.”
“Abin takaici, duk da an garzaya da marigayiyar asibiti don samun kulawar gaggawa, likitoci sun tabbatar da mutuwarta tun kafin a fara ba ta taimako. Wannan lamari ya nuna yadda ƙaramin sabani zai iya rikidewa zuwa mummunar husuma idan ba a magance shi cikin lumana ba.”
Bayan faruwar lamarin, rundunar ta ce ta kama wadda ake zargi kuma tana tsare da ita a halin yanzu, yayin da bincike ke ci gaba.
Rundunar ta kuma tabbatar da cewa za a gurfanar da wadda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike, domin ta girbi abin da ta shuka.