NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Fara Sana’a Ba Tare Da Jari Ba
Published: 9th, June 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Fara sana’a na cikin manyan jerin kalubalen da ’ƴan Najeriya suke fuskanta sakamakon wasu dalilai wadanda suka hada da rashin ilimi, ko Rashin wanda zai ba su shawara ko kuma, uwa uba, rashin jari.
Wasu bayanai da Hukumar Ƙididdiga Ta Kasa – NBS – ta fitar sun nuna cewa fiye da kashi 40 cikin 100 na matasan Najeriya suna sha’awar fara sana’a, amma sun kasa saboda rashin jari.
Haka kuma, wani bincike da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya gudanar ya nuna cewa kashi 65 cikin 100 na matasa masu so su fara kasuwanci suna fuskantar babbar tangarda wajen samun jari daga bankuna ko hukumomin gwamnati.
Shin ko akwai wata hanya da matasa za su bi su fara sana’a ko da ba su da jari?
NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Suka Fara Bacewa Yayin Bukukuwan Sallah DAGA LARABA: Dalilan Tashin Farashin Kayan Miya Gabanin Bikin SallahWannan shine batun da shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai.
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Dabarun kasuwanci jari
এছাড়াও পড়ুন:
Makarantun Kano Za Su Fara Hutun Ƙarshen Zango A Ranar Juma’a – Gwamnati
Kwamishinan Ilimi na Jihar, Dokta Ali Haruna Makoda, ya buƙaci iyaye da su tabbatar da cewa ‘ya’yansu sun koma makaranta a kan lokaci.
Ya yi gargaɗin cewa duk ɗalibin da ya makara wajen dawowa makaranta zai iya fuskantar hukunci.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp