2025-06-02@10:07:19 GMT
إجمالي نتائج البحث: 10
«yanka layyarsa»:
Abin da ake cewa Layya shi ne duk wata halastacciyar dabba da aka yanka domin neman kusanci ga Allah. Layya tana da asali a cikin Kur’ani da Hadisin Annabi (SAW). A cikin Kur’ani Allah (TWT) Yana cewa: “Ka yi Sallah ga Ubangijinka kuma ka yi yanka.” (Kausar: 2). A Hadisi kuwa Anas bin Malik (RA) ya ruwaito cewa: “Manzon Allah (SAW) ya yi layya da raguna biyu bakake, masu kahonni. Ya yanka su da hannunsa, ya yi bisimillah ya yi kabbara, ya kwantar da su ta gefen wuyansu” (Muslim ya ruwaito). Za a yi Huɗubar Ranar Arfa a harsunan Najeriya 3 Sojoji sun kashe ɗan ta’adda da aka sa ladar N100m a kansa a Borno Akwai Hadisai masu yawa...
Alkaluma daga hukumar lura da kudin musaya ta kasar Sin, sun nuna yadda kasar ta samu karuwar darajar cinikayyar waje ta fuskar hajoji da hidimomi, wadda a watan Afirilun da ya gabata ta kai kudin Sin yuan tiriliyan 4.37, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 606.8, karuwar da ta kai ta kaso 6 bisa dari a shekara. Alkaluman da hukumar ta fitar a Juma’ar nan, sun nuna karuwar darajar hajoji da hidimomi da Sin ta fitar ketare zuwa dala biliyan 326.5, yayin da darajar wadanda ta shigo da su ta kai dala biliyan 280.3, inda aka samu rarar dalar Amurka biliyan 46.2. (Mai fassara: Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin...
Kazalika ya kara da cewa, idan za a iya tunawa, Seyi ya kewaya kusan dukkanin jihohin Arewacin kasa nan tare da tallafa wa al’umma da kayan abinci da kudade, musamman a watan Ramadana da ya gabata. A karshe, Sanusi ya yi kira ga matasa maza da mata, kada su bari a bar su a baya a wannan tafiya, domin kuwa kungiya ta kowa da kowa ce, duk mai bukatar yin rajista; kofa a bude take, domin kuwa suna da ofisoshi a kowace jiha, ciki har da babban birnin tarayya Abuja da suke shirin bude kwanan nan ga masu bukatar shiga. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura...
Da safiyar yau Juma’a ne dai jami’an tsaron kasar Chadi su ka kai wani farmaki na kama tsohon fira minista kuma jagoran ‘yan hamayyar siyasar kasar Succès Masra. Jam’iyyar hamayya da Masra yake jagoranta, ta bayyana abinda jami’an tsaron su ka yi wa jagoran nata da cewa, garkuwa ce. Ita kuwa hukumar kasar ba ta fitar da wani bayani akan kamun Masra ba,wanda shi ne ya zo na uku a zaben shugaban kasar da aka gudanar a shekarar da ta gabata. A yayin wancan zaben dai shugaban ‘yan hamayyar siyasar ya riya cewa shi ne wanda ya lashe zaben,amma kuma daga baya ya amince da sakamakon da hukumar zabe ta sanar duk da cewa yana cike da kura-kurai kamar yadda...
Alkaluman hukumar kwastam ta kasar Sin sun nuna cewa a watan Afirilun bana, hada-hadar cinikayyar shige da ficen hajoji ta amfani da kudin kasar yuan ta karu da kaso 5.6 bisa dari. Alkaluman da hukumar ta fitar a Juma’ar nan sun nuna cewa, adadin hajojin da kasar Sin ta fitar ya karu da kaso 9.3 bisa dari a shekara zuwa yuan tiriliyan 2.27, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 314, yayin da adadin hajojin da kasar ta shigo da su daga waje ya karu da kaso 0.8 bisa dari a shekara zuwa kimanin yuan tiriliyan 1.57. Cikin watanni 4 na farkon shekarar bana, jimillar hajojin da Sin ta shigo da su, da wadanda ta fitar ketare a hada-hadar kudin kasar yuan sun...
Jam’iyyar Hamayyar siyasa ta “Chadema” a kasar Tanzania ta ki amincewa da matakin gwamnatin kasar na haramta mata shiga manyan zabukan da za a yi a watan Oktoba. Hukumar zaben kasar ta Tanzania ta zargi jam’iyyar Chameda’ da cewa ta ki amincewa ta rattaba hannu akan dokokin zabe, tana mai yin kira gare ta da ta girmama hukumar zaben kasar. A ranar Asabar din da ta gabata ne dai babbar jam’iyyar adawa ta kasar Tanzania ta kauracewa halartar taron da aka yi wanda ya kunshi dukkanin jam’iyyun siyasa da su ka rattaba hannu akan dokokin zabe. Rattaba hannu akan dokokin dai yana a matsayin daya daga cikin sharuddan shiga cikin zabe da jam’iyyu za su yi,kamar yadda Ramadhani Kalima, daraktan...
A jiya Asabar dubun dubatar ‘yan hamayyar siyasa su ka yi gangami a birnin Stanbul bayan da jam’iyyar “National Party” ta gayyace su, domin ci gaba da yin tir da kamun da aka yi wa Akram Imam Uglu wanda shi ne magajin garin na Stanbul. Shugagan jam’iyyar “Turkish National Party’ ta adawa, Uzgur Ozil ya bayyana cewa adadin wadanda su ka halarci gangamin sun kai miliyan 2.2. Daga cikin mahalarta gangamin da akwai mata da mahaifan Akram Ima wadanda su ka rika bayar da taken cewa za a ci gaba da yin gwgawarmaya ako’ina.” Tun da asubahin jiya Asabar ne dai mutane su ka fara yin tururuwa a cikin birnin na birnin Sitanbul suna dauke da tutocin turkiya da kuma...
Kasar Tunisiya ta shiga cikin sabuwar dambaruwar siyasa saboda yadda ake yi wa wasu fitattun ‘yan siyasa, lauyoyi da kuma ‘yan jarida 40 shari’a, bisa zargin cewa suna yi wa kasa makarkashiya. An jibge jami’an tsaro masu yawan gaske a bakin kotun, yayin da a wajenta kuma masu fafutuka suke bayar da taken nuna kin amincewa da shari’ar, suna bayar da taken; ‘Neman ‘ ‘yanci, da kuma zargin ma’aikatar shari’a da zama ‘yar koren gwamnati. Lauya a cikin kwamitin lauyoyi masu bayar da kariya ga wadanda ake yi wa shari’ar, Lamia Farhani ta bayyana cewa; Abin ban mamaki shi ne shugaban kasa wanda ya rantse zai kare shari’a, wanda kuma shi kwararre ne akan tsarin mulki shi ne na farkon...
Alkaluman da ma’aikatar cinikayya ta Sin ta fitar baya-bayan nan na cewa, a shekarar bara, darajar shige da ficen cinikayyar ba da hidimomi ta Sin ta kai kudin Sin RMB yuan triliyan 7.5, kwatankwacin dalar Amurka triliyan 1.034, wanda ya karu da kashi 14.4 cikin dari bisa makamancin lokaci na shekarar 2023, ma’aunin ya kai wani sabon matsayi a tarihi. Shugaban hukumar kula da cinikayyar ba da hidimomi ta cibiyar nazarin hadin gwiwar ciniki da tattalin arziki na kasa da kasa ta ma’aikatar kasuwanci ta kasar, Li Jun, ya bayyana cewa, al’adun Sin masu kayatarwa na ci gaba da jawo hankalin masu yawon bude ido su zo kasar Sin don yawon shakatawa, da alamar zai inganta habaka ma’aunin cinikayyar ba...
Sojojin kasar Iran sun nuna karfinsu a yankin Asiya ta kudu tare da itisayen da ta yi ta gudanarwa a cikin yan makonnin da suka gabata. Tare da nuna iya diblomasiyyar kasar tare da sauran kasashen yankin. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Rear Admiral Habibollah Sayyari mataimakin shugaban rundunar sojiji na kasar yana fadar haka. Ya kuma kara da cewa, iya diblomasiyyar kasar Iran a tsakanin kasashen yankin, ya tabbatar da karfin da kasar take da shi a fagen karfin soje. Kuma ta tabbatar da cewa zata iya kula da al-amuran tsarom da kuma tabbata shi a yankin. Sayyari yace an gudanar da atisayen na sojoji kimani rundunonin fiya da 100 inda suka yi musayar tunani...