Aminiya:
2025-11-02@12:30:16 GMT

Isra’ila ta ƙwace jirgin ruwa a hanyar kai agaji Gaza

Published: 9th, June 2025 GMT

Sojojin Isra’ila sun ƙwace wani jirgi da ke ɗauke da kayan tallafi mai suna Madleen wanda ke kan hanyara a zuwa Gaza, sannan suka karkata akalar shi zuwa Isra’ila.

A wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Wajen Isra’ilan ta fitar da tsakar daren Lahadi ta bayyana cewa za a mayar da masu fafutukar da ke cikin jirgin zuwa ƙasashensu.

Sojoji sun kashe wani kwamandan ’yan ta’adda a Yobe Zai fi kyau Tinubu ya mayar da hankali kan ’yan Nijeriya ba Zaɓen 2027 ba — ACF

Sanarwa da aka wallafa a X, ma’aikatar ta ce jirgin yana “kan hanyarsa zuwa gaɓar tekun Isra’ila” kuma “ana sa ran fasinjojin za su koma ƙasashensu.”

Ƙungiyar Freedom Flotilla Coalition ta ce sojojin Isra’ila sun “yi garkuwa” da masu fafutukar da ke cikin jirgin na Madleen, ciki har da Greta Thunberg, ’yar kasar Sweden da ke hankoron kare muhalli.

Tun da farko, sojojin ruwan Isra’ila sun shiga jirgin na Madleen a cikin tekun ƙasa da ƙasa, a cewar ƙungiyar, wadda ta kuma ce an katse sadarwa da jirgin.

Hotunan kai tsaye da aka nuna a baya sun nuna jiragen ruwa na Isra’ila sun kewaye jirgin, inda sojoji suke umartar masu fafutukar da ke cikin jirgin su ɗaga hannayensu sama.

‘Yar Majalisar Tarayyar Faransa ‘yar asalin Falasɗinu, Rima Hassan, ta ce an kunna ƙararrawa a cikin jirgin na Madleen bayan da jiragen sama marasa matuƙa suka fesa wani farin ruwa a jirgin.

Babbar Jami’a ta Musamman ta Majalisar Dinkin Duniya, Francesca Albanese, ta tabbatar da cewa an ga jiragen sama marasa matuƙa guda biyu a sama, tana bayyana su da cewa “waɗanda ke da hatsari.”

Ma’aikatar Harkokin Wajen Isra’ila ta ce sojojin ruwa sun umarci jirgin Madleen da ya sauya hanya saboda kusancinsa da abin da suka kira “yankin da ba a shiga.”

Jirgin Madleen, wanda yake da tsawon mita 18, ya fara tafiya zuwa Gaza a ranar 1 ga watan Yuni daga tashar jirgin ruwa ta San Giovanni Li Cuti a Catania, Sicily, a matsayin wani ɓangare na sabon shirin da ƙungiyar Freedom Flotilla Coalition ta shirya don karya takunkumin Isra’ila da isar da tallafi zuwa Gaza.

Jimillar mutane 12 ne ke cikin jirgin, ciki har da masu fafutuka 11 da kuma ɗan jarida guda ɗaya.

A cewar masu shirya tafiyar, jirgin yana ɗauke da kayayyakin tallafi masu matukar muhimmanci ga mutanen Gaza, ciki har da madarar jarirai, da fulawa, da shinkafa, da maganin jarirai, da kayayyakin tsafta na mata, da kayan tace ruwa, da magunguna , sandunan guragu, da kuma kayan taimakon yara masu nakasa.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Isra ila Isra ila sun

এছাড়াও পড়ুন:

Kasar Sin Ce Ke Da Sama Da Rabin Muhimman Makaloli Na Duniya

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Bunkasar Fannin Kirkire-Kirkiren Fasahohi Na Sin Alheri Ne Ga Dukkanin Duniya Ba Barazana Ba October 30, 2025 Daga Birnin Sin Sin Za Ta Harba Kumbon Shenzhou-21 October 30, 2025 Daga Birnin Sin Xi Jinping: Sin Da Amurka Za Su Iya Hada Kai Don Sauke Nauyin Dake Wuyansu Na Manyan Kasashe Da Daukar Ainihin Matakai October 30, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Hamas ta musanta zargin Amurka na cewa tana sace kayan agaji a Gaza
  •  Gaza: Daga Tsagaita Wuta Zuwa Yanzu Fiye Da Mutane 200 Ne Su Ka Yi Shahada
  • ‘An Kashe Masu Zanga-zanga Akalla 500 a Tanzania’
  • Jerin Gwarazan Taurarinmu
  • ’Yan bindiga sun sace fasinjoji a cikin motocin bas a Kogi
  • HKI Na Ci Gaba Keta Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta A Gaza Inda Take Kashe Falasdinawa
  • NPA Da Ƙungiyar Injiniyoyi Ta Yi Haɗaka Don Bunƙasa Tashoshin Jiragen Ruwa
  • Borno ta fara fitar da kayan robobi zuwa ƙasashen waje – Zulum
  • Kasar Sin Ce Ke Da Sama Da Rabin Muhimman Makaloli Na Duniya
  • Gaza: hare-haren Isra’ila sun kashe mutane 100 Cikin Kwanaki Biyu