2025-06-06@14:39:27 GMT
إجمالي نتائج البحث: 15
«kamar Ranar Arfa»:
Sanatocin Arewa sun bayyana alhini da jimami kan haɗarin mota da ya yi sanadin mutuwar wasu daga cikin ‘yan wasan Jihar Kano da ke dawowa daga Gasar Wasanni ta Kasa da aka kammala a Jihar Ogun. A cikin wata sanarwa da Shugaban ƙungiyar Sanatocin Arewa, Sanata Musa Yar’adua ya sanya wa hannu, ƙungiyar ta miƙa ta’aziyyarta ga iyalan mamatan da kuma Gwamnatin Kano, inda ya bayyana lamarin a matsayin babban rashi ga ƙasa baki ɗaya. ‘Yan Wasan Da Tauraruwar Ronaldo Da Messi Ta Hana Su Haskawa Gwamnatin Kano Ta Ba Iyalan Mamatan Wasanni Tallafin Naira Miliyan Ɗaya Kowane Sanata Yar’adua ya yi addu’ar Allah ya jikan waɗanda suka rasu, ya kuma bai wa waɗanda suka jikkata fatan samun sauƙi cikin...
Hukumomin ƙasar Saudiyya sun sanar cewa a bana za a gabatar wa mahajjata huɗubar Ranar a cikin harsuna uku na Najeriya. Harsunan Najeriya guda uku da za a gabatar da Huɗubar Ranar Arfa da su sun ne Hausa da Fulatanci da kuma Yarbaci. Harsunan huda uku na daga cikin karin harsunan duniya guda 34 da hukumomin Saudiyya suka sanar cewa za a gabatar da Huɗubar a cikinsu.
Habakar matsayi na kasafin kudi ya inganta a cikin 2024, ta hanyar habaka kudaden shiga. Gibin kasafin kudi ya ragu daga kashi 5.4 na kudin shiga a shekarar 2023 zuwa kashi 3.0 na kudin shiga a shekarar 2024, babban ci gaban da aka samu sakamakon karuwar kudaden shiga na daukacin tarayyar kasar, wanda ya karu daga naira tiriliyan 16.8 a shekarar 2023 (7.2 na kudaden shiga) zuwa kimanin naira tiriliyan 31.200. Rahoton ya kara da cewa hauhawar farashin kayayyaki ya tsaya tsayin daka amma ana sa ran zai fadi zuwa matsakaicin shekara da kashi 22.1 cikin 100 a shekarar 2025, yayin da tsayin daka mai tsayi ya tabbatar da amincin manufofin kudi tare da rage tsammanin hauhawar farashin kayayyaki. Ko...
Ya kara da cewa kungiyar dattawan Arewa ba za ta lamunci cin zarafin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba. Sai dai da take magana da LEADERSHIP, ACF ta bayyana cewa kungiyar ba za ta goyi bayan duk wani dan takarar shugaban kasa a bainar jama’a a zaben 2027 ba. Da yake magana ta wayar tarho a ranar Lahadi, sakataren yada labarai na ACF na kasa, Farfesa T.A. Muhammad Baba, wanda aka nemi ya yi tsokaci kan kalaman Baba-Ahmed, ya ce a matsayinsa na dattijo, Baba-Ahmed yana da ‘yancin bayyana ra’ayinsa. Mai magana da yawun ACF, duk da haka, kungiyar za ta bincika dukkan batutuwan tare da gabatar da su ga masu jefa kuri’a don su iya yin zabi...
Asusun bayar da lamuni na duniya ( IMF) ya yi gargadin cewa rashin tabbataci da Karin kudin harajin Amurka ya haddasa zai iya kawo tsaiko a cikin harkokin cinikiyya ta duniya. Sanarwar wacce babban jami’in ttatalin arziki na Asusun bayar da lamunin na duniya Pierre -Oliver-Gourinchas, ya bayyana ta kara da cewa; Za a iya samun karuwar hargitsi a cikin harkokin tattalin arzikin na duniya da dama yake fama da matsala. Jami’in ya yi bayani ne bayan sake yin hasashe akan ci gaban tattalin arzikin duniya, wanda aka fitar a cikin rahoto a ranar Talatar nan. Asusun bayar da lamunin ya yi hasashen cewa tattalin arzikin duniyar zai bunkasa da kaso 2.8 % a cikin 2025, da hakan yake nuni...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Wutar lantarki ta zama tamkar gwal a wasu sassan Arewacin Najeriya, inda a wasu yankuna aka ba da rahoton samun ta sa’o’i biyu kawai a rana, wasu kuma ba sa samun ko daidai da dakika ɗaya. Masu ƙananan sana’o’i suna kallon rayuwarsu da kasuwancinsu suna durƙushewa yayin da kayan sana’arsu suke lalacewa saboda rashin wuta. NAJERIYA A YAU: Matsayin Mataimakin Shugaban Ƙasa A Tsarin Mulkin Najeriya? DAGA LARABA: Dalilan Ɓaraka A Tsakanin Iyayen Riƙo Da Ƴaƴan Riƙo Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne a kan wannan matsala da yadda take taɓa rayuwar al’umma da hanyoyin magance ta. Domin sauke shirin, latsa nan
Jiragen yakin HKI HKI sun yi ruwan boma-bomai kan astin Al-Ahli, asbiti tilo da ya rage yake aiki a arewacin zirin Gaza, a safiyar yau Lahadi. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa jiragen yakin HKI sun wargaza bangaren ’emagencu’ bukatar kula na gaggawa a asbitin da kuma kofar shiga asbitin. Har’ila yau hare-haren sun lalata bangaren Iskar Oxigen na kula da wadanda suke bukatar kula mai tsanani a asbiti. Kuma sanadiyyar haka mutane da dama sun rasa rayukansu awannan bangaren daga ciki har da wani yaro dan shekara 12 wanda ya ji rauni a kai. Razan Al-Nahhas wani likita mai aiki a bangaren kula na gaggawa a asbitin ya fadawa kafafen yada labarai kan cewa wannan...

Babban Taron LEADERSHIP Karo Na 17: Tinubu Ya Kare Yadda Gwamnatinsa Ke Tafiyar Da Tsarin Rabon Arzikin Kasa
Mataimakin shugaban kasar wanda ya samu wakilcin Mai Ba Shugaban Kasa Shawara Na Musamman Kan Ayyuka Na Ofishin Mataimakin Shugaban Kasa, Aliyu Modibbo Umar ya ce, “Kalubalan Nijeriya ya ta’allaka a tsarin tarayyarmu,” in ji Shettima. “Ba batu ne na wai nawa ne kowace rukunin tarayya ke samu ba, magana ce ta yadda ake amfani da irin wadannan albarkatun.” “Ba kuma batu ne na cewa nawa ne kowace bangare ke samu ba, sai dai a yi batun yadda ake amfani da irin wadannan kayan.” Ya yaba wa LEADERSHIP bisa samar da wani dandali wanda “ba a samar da shi kadai don musayar ra’ayi ba sai don tsara manufofi masu ma’ana.” Ya kuma bayyana sauye-sauyen da ake yi a karkashin gwamnatin...
Shugaba Tinubu ya zanta da manema labarai bayan kammala Sallar Idi na karshen watan Ramadan a filin da aka gabatar da Sallar Idi na kasa a Abuja ranar Lahadi. Cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga ya fitar, shugaban ya bukaci ‘yan Nijeriya da kada su koma kan aikata abubuwan da su ba ta dace ba, a maimakon haka, ya bukace su da su dage wajen aiwatar da kyawawan dabi’un game da darusan da suka koya a watan Ramadan. A cikin hudubar da babban limamin masallacin kasa dake Abuja, Dakta Abdulkadir Salman Sholagberu, wanda ya jagoranci Sallar ya gabatar, ya jaddada bukatar Musulmi su ci gaba da gudanar da ibadar da suka koya a Azumin watan Ramadan,...
Shugaban Majalisar Dattawan Arewa (NEF), Farfesa Dahiru Ango Abdullahi Yakawada, ya yi murabus daga sarautar Magajin Rafin Zazzau. Farfesa Dahiru Ango Abdullahi ya yi murabus ne daga sarautar Magajin Rafin Zazzau saboda shekarunsa da suka ja. Hamas ta ɗora alhakin harin da Isra’ila ta kai a kan Amurka Majalisar Wakilai ta amince da ƙudirin dokar haraji Wakilinmu ya ruwaito cewa a yanzu ƙaninsa, Alhaji Shehu Abdullahi Yakawada ne zai gaje shi a wannan kujera ta hakimanci. Farfesa Ango Abdullahi yana ɗaya daga cikin mazan jiya da suka yi ragowa a Nijeriya. Farfesa Dahiru Ango Abdullahi ɗaya ne daga cikin dattawan da al’umma suke buƙata musamman a wannan zamani. Yana ɗaya daga cikin masu bayyana ra’ayin su a kowanne irin yanayi...
Kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya NUJ, FRCN Kaduna Chapel, ta jaddada kudirinta na inganta jin dadin mambobinta ta hanyar bullo da sabbin tsare-tsare da shirye-shiryen tallafi. Shugaban kungiyar, Kwamared Umar Adamu Sarikin Fada ne ya bayyana haka a lokacin rabon kayan abinci na Ramadan ga ‘yan kungiyar a Kaduna. Umar Adamu Sarikin Fada ya bayyana cewa shirin rabon kayayyakin na daga cikin dabarun da kungiyar ta keyi na dakile tasirin tabarbarewar tattalin arzikin kasar nan. Ya tabbatar da cewa sama da ‘yan uwa Musulmi dari da hamsin ne suka ci gajiyar shirin na watan Ramadan na bana, inda ya jaddada cewa su ma Kirista na kungiyar sun samu irin wannan tallafi a lokacin bukukuwan Kirsimeti na 2024. Shugaban ya kuma...
Sunana Aisha T. Bello daga Jihar Kaduna: Rashi ramadan basket nasa a kore saurayi saboda ‘yan mata sun maida ramadan basket dole. Shawara ta ga al’ummar musulmi duniya shi ne; mu yi amfani da wannan dama gun rokon Allah, saboda in Allah ya nuna mana wanan mu gani ba lallai bane mu ga wani watan Ramadan din ba, kuma mu sa kasar mu cikin addu’a Allah ya bamu dacewa. Sunana Abubakar Ahmad, daga Jihar Nassarawa: Ga me hali ya kan shiryawa gajiyayyu marasa hali, wanda kuma Allah bai hore masa ba ya shiga sahun wanda sai dai a dauka a basu su wadannan ba sa shirya komai face yawan salloli da addu’o’i da neman taimakon ubangiji Allah ya fitar...
LEADERSHIP Hausa ta labarto cewa, an tabbatar da sallamar Ari a matsayin Kwamishinan zaɓen jihar Adamawa bayan da Majalisar wakilai ta tarayya ta amince da buƙatar sallamarsa da shugaban ƙasa ya yi, biyo bayan zarginsa da aka yi da karya ƙa’idojin aiki da shigo da shakku yayin gudanar da aikin zaɓe da ayyana sakamakon zaɓe ba daidai ba, lamarin da har ya kai an gurfanar da shi a kotu. Ari ya nuna damuwarsa kan yadda hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) da kotun sauraron ƙararrakin zaɓe suka shafa wa idanunsu toka suka ƙi hango hujjojinsa da ya gabatar na kura-kuran da aka tafka a lokacin zaɓen. Hudu wanda ya ɗauki Alkur’ani mai girma yayin hirar, ya rantse da...
Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya tabbatar da naɗin Sarkin Yarbawan Funtuwa, Oba Alhaji Murtala Sani Adeleke a matsayin sabon Sarkin Yarbawan Jihohin Arewa 19 har da Abuja. Mataimakin Gwamnan JIhar Katsina, Malam Faruk Lawal Jobe ne ya tabbatar da naɗin a madadin gwamnan a lokacin da yake karɓar baƙuncin tawagar Sarakunan Yarbawan Arewa da suka miƙa masa takardar amincewarsu ga zaɓen Alhaji Murtala Sani Adeleke a matsayin sabon Sarkin Yarbawan Arewa a fadar gwamnati da ke Katsina. Ta kashe saurayinta saboda ya gaisa da tsohuwar abokiyar karatunsa Abba ya naɗa sabon Sakataren Gwamnatin Kano Gwamnan ya nuna matuƙar farin ciki da jinjina wa yadda aka gudanar da zaɓen shugabannin Majalisar Sarakunan Yarbawan na Arewa lami lafiya. Ya ce,...
Aston Villa na ɗaya daga cikin ƙungiyoyi da dama da ke son ɗauko ɗan wasan gaba na Manchester United Marcus Rashford, ɗan wasan mai shekaru 27 bai taka leda a United ba tun lokacin da babban kocin ƙungiyar Ruben Amorim ya ajiye shi a wasan Manchester derby a ranar 12 ga watan Disamba. Amorim ya ce a ranar Laraba yana jin ƙungiyarsa za ta fi kyau da Rashford a ciki, amma ɗan wasan bai cika ƙa’idojin da ya buƙata ba, wakilan Rashford sun gana da wasu manyan ƙungiyoyin Turai a cikin ‘yan makonnin da suka gabata a ƙoƙarinsu na ganin ya bar Manchester. Mece Ce Matsalar Manchester United? AC Milan Ta Kammala Ɗaukar Kyle Walker Daga Manchester City A Matsayin...