Wasu Jiragen Ruwa Na Ceto Da Jin Kai Sun Tashi Daga Tunisiya Zuwa Gabar Ruwan Gaza
Published: 9th, June 2025 GMT
Jiragen ruwan wadanda aka bai wa sunan: “Jajurcewa” za su tashi ne daga Tunisiya jim kadan bayan da sojojin HKI su ka hana wani jirgin ruwan dake dauke da masu fafutuka daga kasashen turai,isa gabar ruwan Gaza.
Jirgin ruwan na ” Jajurcewa’ zai bi ta ruwan Libiya, sannan Masar daga can kuma ya nufi gabar ruwan Gaza.
Jiragen ruwan dai suna dauke da masu fafutuka 7,000 daga kasashen Tunisiya, Moroko, Aljariya, Murtaniya, da Libiya.
Kwamitin kasa da kasa domin karya killace Gaza, wanda ya shirya wannan tafiyar, ya kuma yi wani kiran ga ‘yan fafutuka a duniya da su shirya wasu tafiye-tafiyen ta ruwa zuwa Gaza, domin kawo karshen killace yankin da aka yi tun 2007.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Yan Nijeriya Na Ɗanɗana Kuɗarsu Kan Jinkirta Cire Tallafin Mai – Sarki Sanusi
“A lokacin, mun yi lissafin adadi a Babban Bankin. Na tashi na kafa sharuda bisa ga ka’idodi, inda na ce a cire tallafin yau. Farashin kaya zai tashi daga kashi 11 zuwa kashi 13, zan rage shi a cikin shekara guda. Ba za mu samu hauhawar farashin kaya na kusan kashi 30 ba,” in ji shi.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA