Leadership News Hausa:
2025-07-24@03:29:54 GMT

Wajibi A Mayar Da Hankali Kan ‘Yancin Yara

Published: 6th, June 2025 GMT

Wajibi A Mayar Da Hankali Kan ‘Yancin Yara

Yawan Yaran da ba su zuwa makarantun boko a Nijeria wadanda suka kai kimanin su miliyan 18.3, hakan ya nuna cewa, wannan adadin na Yaran, kusan daidai yake da yawan alumomin da ke a kasashen Norway, Singapore, da Cuba.

Wannan ba wai batu ne, na matsalar da ake fuskanta a bangaren ilimin boko kadai ba, domin matsala ce, da ke bukatar a ayyana dokar ta baci tare da samar da daukin da ya kamata daga bangaren gwamnati da kuma sauran alomomin kasar.

Misali, wata kungiya mai kare rajin Yara, mai zaman kanta da ake kira da, Sabe the Children ta bayyana cewa, sama da Yara1,600 a shekarar 2014, aka sace a makarantun su, wadanda sace su din, ya zama tamkar, an dana masu wani tarkon mutuwa ne.

Kazalika, wani rahoto Daraktan Asusun tallafawa kannan Yara na UNICEF, da ke gudanar da aikinsa a kasar nan Dakta Tushar Raney a bayyana cewa, a shekarar 2023 kacal, a daukacin fadain Nijeriya, an tilasta garkame makarantu da suka kai adadin 439.

A wani lokacin rashin zabi ne, ke tilastawa wasu iyayen jefa rayuwar ‘ya’yansu, a cikin hatsari domin ‘ya’yan na su, samu ilimin zamani, wanda idan ba su samu ilimin ba, rayuwarsu, za ta kasance a cikin kangin jahilci, duba da cewa, kowanne dan kasa, na da hakkin a bai wa rayuwarsa kariya.

Bugu da kari, kalubalen rashin samun abinci mai gina jiki a tsakanin yaran kasar, na daga cikin abinda ya kara zama wata babbar annoba.

Ganin cewa, a kasar akwai yara kanana miliyan 5.4 da shekarun su suka fara daga watanni 0 zuwa watanni 59 da ke ci gaba da fuskantar kalubalen karancin abinci wadanda adadinsu ya karu zuwa kaso 23 cikin dari, hakan ya sanya, a nan gaba, Nijeriya za ta iya yin rashin samun karin alumma.

Rashin samun abinci mai gina jiki a tsakanin kananan yara hakan ya dashishe su, daga saurin fahintar ilimi tare da jefa rayuwarsu, a cikin kangin talauci da kuma rashin samun ci gaba.

Hakazalika, wasu alkaluman da UNICEF ta fitar sun bayyna cewa, a fadin duniya, an dora Nijeriya kan sikelin kasar da ta kai mataki na uku, wajen yiwa ‘ya’ya mata masu kananna shekaru aure, inda kasar ta kasance, tana da ‘ya’ya mata da suka kai miliyan 23.6 da aka yi masu are, suan da shekaru 18 da kuma wasun su, da suka kai sama da miliyan 10, da aka yi masu aure, su na da shekaru 15.

Irin wannan auren na wuri, ya janyo tauye hakkin irin wadannan ‘ya’yan mata, damar samun ilimin boko, wanda hakan ya kasance, tamkar take masu ‘yancin su ne, na rayuwa.

Hukumar kididdiga ta kasa NBS a cikin wani rahoto da ta fitar ta ce, akwai kuma batun sanya kananna yara aikin bauta, inda a Nijeriya, a 2022 ake kiyasta cewa, akwai yara sama da miliyan 24 da suke yin irin wannan aikin na kangin bauta, ciki har da wasu yara miliyan 14.3 da ake sanya wa, yin ayyuka masu hatsari.

Yaran suna yin aikin ne, a gurare da ban da ban da suka hada da, inda ake hakar ma’adanai da kuma a wasu masana’antu, inda ake biyansu, kudade, ‘yan kalilan.

Sai dai, a kwanukan baya, gwamnatin tarayya ta samar da wani shiri na samar da ilimin boko, inda ta zuba sama da Naira biliyan 263 a asusaun samar da ilimi na bai daya wato UBEC, amma wasu tsaiko da ake samu a shirin, hakan na ci gaba da janyo jinkirin yin aikin gadan-gadan.

Hakazalika, shugaban kasa Bola Tinubu, ya aminci da a yi amfani da asusun na UBEC, musamman domin a bunkasa ilimi a kasar a sama da jihohi 30, amma sai dai, shirin baya tafiya, yadda ya kamata.

Bugu da kari, daukin da ma’aikatar kula da walwalar mata da walwalar a karkashin ministar ma’aikatar Imaan Sulaiman-Ibrahim, ta samar da wani kyakyawan tsari na bai wa kananan yara kariya.

Misali, an karawa ma’aikatar karin kasafin kudi da ya dara sama da kaso 1000 a cikin dari, musamman domin a tabbatar da ana bai wa yaran kasar kariyar da ta kamata.

Sai dai, samar da daukin abu ne, dake bukatar a hada karfi da karfe, a tsakanin matakan gwamnati uku na kasar nan da kuma daukin sauran alumomin kasar.

Abin da Nijeriya ke bukata shi ne, kula da walwala da jin dadin yara tare da kuma samar masu da tsaron rayuwar su.

Kazalika, ya zama wajibi gwamnatin tarayya kafa cibiyoyin ilimi domin a samar da kariyar ta tsaro a shiyoyin kasa, musamman ta hanyar tura jami’an tsaro, domin su bai wa makarantu kariya.

Dole ne kuma gwamnatocin jihohi su tabbatar da sun samar da kudaden a cikin shirin ilimin, wanda hakan zai dakile duk wani jinkiri da ake samu, na wanzar da shirin.

Bugu da kari, ya sama wajibi gwamnati ta samar da kyawawan shirye-shiye na tallafawa iyaye wajen tsamo su, daga halin talaucin da ke addabar su

Ya kamata malaman addinai, su mayar da hankali wajen yin gangamin kan abubuwa da ke sanya wa, ake take wa kananan yara ‘yanci.

Hazalika, akwai bukatar a kara mayar da hankali, wajen kara horas da jami’an tsaro tare da samar masu da wadatattun kudade domin su rinka hukunta duk wanda ya take ‘yancin yara.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: rashin samun

এছাড়াও পড়ুন:

An kaddamar Da Wani Shiri Na Ba ‘Yan Mata 200,000 Tallafin Audugar Mata A Kano

An shawarci mata da su daina amfani da tsumma ko soson katifa, da takarda a lokacin al’adar su don inganta tsafta da rigakafin matsalolin lafiya.

 

Jami’ar tallafawa masu kula da tsaftar jinin haila a jihar Kano (MH-NoW) Amina Sabiu Musa ta yi wannan kiran ne a lokacin wani taron karawa juna sani na tsaftar jinin haila ga kwararrun ‘yan jarida da masu fada a ji a shafukan sada zumunta da aka gudanar a Kano.

 

A cewarta, shirin na MH-NoW ya shafi ‘yan mata da mata masu shekaru 10 zuwa 24 su 200,000 da nufin magance matsalar talaucin kudin sayen audugar mata a fadin Najeriya.

 

Ta bayyana cewa shirin wanda Population Services International (PSI) Nigeria ta aiwatar, zai hada da masu raba kayan aikin tsaftar muhalli da za a sake amfani da su don taimakawa wajen rage radadin talauci a wannan banagen.

 

“Ana gudanar da aikin a wasu jahohin Najeriya, tare da mai da hankali kan dalibai da mata matasa a al’ummomi 15 dake fadin kananan hukumomin Ghari, Tsanyawa, da Nasarawa a Kano,” in ji Amina.

 

Shima da yake jawabi a wajen taron, mataimakin daraktan bincike da kididdiga na ma’aikatar mata, yara da masu bukata ta musamman ta jihar Kano, Alhaji Zubair Abdulmumin Zubair ya bukaci iyaye da su ba da fifiko ga tsaftar jinin haila ta hanyar samar da kayan tsafta da kuma jagoranci mai kyau ga ‘ya’yansu mata.

 

Ya nuna damuwarsa kan rahotannin da ke cewa dalibai mata da yawa ba sa zuwa makaranta a lokutansu sakamakon rashin samun kayayyakin tsaftar muhalli da kuma rashin audugar mata a lokacin al’ada.

 

Ya yi kira ga maza, iyaye, maza da mata da duk masu ruwa da tsaki da su yi watsi da tatsuniyoyi masu cutarwa game da jinin haila tare da tallafawa ilimin haila.

 

“Dole ne kuma a ilmantar da maza game da jinin haila don su fahimci sauyin yanayi da yanayin da mata ke fuskanta a lokacin al’ada,”

 

Wasu daga cikin mahalarta taron da suka zanta da gidan rediyon Najeriya Aminu Abdullahi da Hannatu Sulaiman Abba da kuma Maimuna O. Yusuf sun bayyana taron da ya dace.

 

A matsayinsu na masu yada labarai, sun yi alkawarin ba da horo ga wasu kuma za su yi amfani da dandamali daban-daban na don Magana akan haila.

 

 

Gidan Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa taron bitar ya samu halartar dimbin mahalarta.

 

Khadija Aliyu

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • UNICEF Ya Bukaci Jihar Kano Ta Bai Wa Yara Muhimmanci A Kasafin Kudi
  • Tinubu Ba Zai Taɓa Tauye ’Yancin Kafafen Yaɗa Labarai Ba, In ji Ministan Yaɗa Labarai
  • Shugaban Amurka Trump Ya Bukaci Gurfanar Da Tsohon Shugaban Amurka Barack Obama A gaban Kuliya
  • DAGA LARABA: Abubuwan da ya kamata yara su yi yayin hutun makaranta
  • Natasha za ta sake komawa kotu kan hana ta shiga harabar majalisa
  • Karin Maganar Sinawa: Koyar Da Su Ya Fi Bayar Da Kifi
  • UNICEF na zargin Gwamnatin Nijeriya da cin zarafin ƙananan yara
  • Ana Iya Samun Masu Samar Da Kayayyaki Iri-Iri Cikin Awa Daya A Kasar Sin
  • An kaddamar Da Wani Shiri Na Ba ‘Yan Mata 200,000 Tallafin Audugar Mata A Kano
  • Gwamnatin Kano Ta Maida Gidan Marayu Zuwa Cibiyar Gyaran Mata Masu Shaye