Sojojin HKI Suna Ci Gaba Da Yi Wa Falasdinawa Kisan Kiyashi A Rannakun Bikin Babbar Salla
Published: 7th, June 2025 GMT
A rana ta biyu tabukuwan babbar salla, sojojin HKI suna ci gaba da yi wa Falasdinawa kisan kiyasahi da kuma rusa matsugunansu a yankin Gaza.
A yau Asabar kadai gwamman Falasdinawa ne su ka yi shahada a cikin sansanonin da Falasdinawa suke gudun hijira a cikinsu.
An sami shahidai 5 da kuma wasu mutane biyu da su ka jikkata a kusa da cibiyar rana kayan agaji a yammacin Rafah dake kudancin zirin Gaza.
A yammacin birnin Khan-Yunus kuwa wasu Faladinawa 12 ne su ka yi shahada, yayin da wasu 40 su ka jikkata saboda harin da ‘yan sayahoniyar su ka kai wa sansaninsu.
A arewacin Khan-Yunus kuwa, sojojin mamayar sun ruguza gidajen Falasdinawa da dama.
A kusa da cibiyar kiwon lafiya ta ” Majma’u -Shifa” dake yammacin birnin Gaza, adadin shahidai ya kai 7 wasu biyu kuwa su ka jikkata.
Daga lokacin da HKI ta shelanta yaki akan mutanen Gaza a 2023, adadin wadanda su ka yi shahada sun kai 54,677, yayin da wadanda su ka jikkata su ka kai 125,530.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
An Gudanar Da Bikin Mu’amalar Jama’a Da Al’adu A Tsakanin Sin Da Tsakiyar Asiya A Astana
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp