Hatsarin Mota Ya Yi Ajalin Mutane 9 A Jigawa
Published: 9th, June 2025 GMT
Mutane tara ne suka rasa rayukansu a wani mummunan hatsarin mota da ya afku a kauyen Kyaramma da ke karamar hukumar Ringim a jihar JIgawa. A cewar rundunar ‘yansandan jihar Jigawa, hatsarin wanda ya afku a ranar Asabar da ta gabata da misalin karfe 2 na rana, ya rutsa da wasu motoci kirar Golf 3 saloon guda biyu tare da jikkata wasu da dama.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: wadanda suka
এছাড়াও পড়ুন:
A Kalla Falasdinawa 10 Yunwa Ta Kashe A Gaza A Cikin Sa’o’i 24
Ma’aikatar kiwon lafiya ta Gaza ta sanar da cewa a cikin sa’o’i 24 da su ka gabata adadin falasdinawan da su ka yi shahada saboda yunwa sun kai 10.
Daga lokacin da HKI ta fara amfani da yunwa a matsayin makamin yaki,adadin falasdinawan da su ka yi shahada sun kai 111.
Wannan adadin yana nuni da yadda rashin abinci ya tsananta a cikin yankin na Gaza saboda yadda Isra’ila ta killace yankin ta hana a shigar da abinci a ciki.
A gefe daya, HKI tana ci gaba da kashe Falasdinawa ta hanyar yi musu kisan kiyashi, da a yau kadai fiye da mutane 80 ne su ka yi shahada. Mafi yawancin wadanda su ka yi shahada a cikin sa’oin nan na baya suna a unguwannin Tallul-Hawa, da Deir-Balah. Haka nan kuma ‘yan sahayoniyar sun kai wasu hare-haren a sansanin ‘yan hijira dake Mukhayyam-Shadhi.
Kungiyoyin kasa da kasa suna ta ci gaba da yin kira da a bude iyakokin Gaza domin a shigar da kayan abinci, sai dai babu faruwar hakan.
A cikin zirin Gaza dai, mutane suna faduwa suna somewa, wani lokaci mutuwa saboda yunwa, ba kuma babba babu yaro.
Mafi yawancin mutanen da suke mutuwa dai kananan yara ne, jarirai da matasa.