Ana Ci Gaba Da Samun Rudani Yayin Da INEC Ta Jinkirta Rajistar Sabbin Jam’iyyu
Published: 7th, June 2025 GMT
Wani Lauya Okere Kingdom Nnamdi, wanda ya gabatar da takardu don samun rajistar Jam’iyyar Mutanen Kasa (PPP) a ranar 28 ga Maris, 2025, ya ce bayan wata daya sai INEC ta bayyana cewa ba ta bude adireshin fara yin rajistar sabbin jam’iyyun siyasa.
Jami’an INEC da suka yi magana kan lamarin, sun musanta zarge-zargen.
“Hukumar ta amsa wa masu nema. Ba daidai ba ne a zargi INEC da jinkirin amsa bukatun yin sabbin rajistar. Za a bude Shafin intanet dazarar an kammala duk wani aikace-aikacen da suka cika ka’ida,” in ji wani babban jami’in hukuman.
Mai magana da yawun INEC, Rotimi Oyekanmi, ya sake jaddada cewa kungiyoyin siyasa dole ne su bi doka da oda na tsarin mulkin kasa kafin a yi musu rajista.
“Dole ne INEC ta tabbatar da cewa an bin doka. An bayyana ka’idojin, kuma har idan mai nema bai cika su ba, to ba za a iya masa rajistar ba har sai ya cika,” in ji shi.
Wani mai sharhi kan harkokin shari’a ya bayyana cewa jinkirin aiwatar da rajistar na iya kawo cikas ga shirin zabe, musamman ganin cewa ana sa ran fara zaben fid da gwani na jam’iyya a tsakiyar 2026.
Tsohon shugaban kungiyar siyasa ta kasa da kasa, Farfesa Adele Jinadu ya ce, “Idan masu nema sun bi ka’idojin kundin tsarin mulki da na zabe, babu wata kuntatawa ga rajistar jam’iyya a karkashin tsarin jam’iyyu masu yawa.”
Dakta Dauda Garuba na cibiyar ci gaban dimokiradiyya (CDD) ya kara da cewa, “Idan aka bai wa jam’iyyu damar gudanar da aikinsu cikin ‘yanci da zaman kansu, da yawa daga cikin kalubalen da muke fuskanta a yau ba za su taso ba.”
A ranar 6 ga Maris 2025 ne, majalisar wakilai ta amince da karatu na biyu kan kudirin dokar da ke neman canza rajistar da tsarin kula da jam’iyyun siyasa daga INEC zuwa wani sabon hukuma mai zaman kanta.
Kudirin hadin gwiwa tsakanin shugaban majalisan, Abbas Tajudeen da dan majalisa, Marcus Onobun, wannan kudurin na bayar da shawarar kafa kotun kula da takaddama tsakanin jam’iyyu don warware rikici cikin gida da rikice-rikicen tsakanin jam’iyyun.
An tura kudirin zuwa kwamitocin da ke kula da al’amuran zabe da kuma jam’iyyun siyasa don kara dubawa.
Duk da karuwar kiraye-kiraye na shiga harkokin siyasa, masu nazari da yawa na ganin cewa lokaci na kurewa ga sabbin jam’iyyun wajrn yi musu rajista yadda ya kamata da kuma shirya su kafin zaben 2027.
Shugaban jam’iyyar AA, Barrister Kenneth Udeze ya yi gargadin cewa, “Bai kamata a yi rajistar kowace jam’iyya ba kasa da watanni 12 kafin zabe. Bisa fatan gudanar da zaben fid da gwani na jam’iyyun a tsakiyar 2026, lokaci na kara kuantowa.
A halin yanzu, Nijeriya na da jam’iyyun siyasa 19 da aka tabbatar da rajistarsu, daga cikin 91 bayan INEC ta cire rajistar jam’iyya 74 a shekarar 2020 bisa ga rashin kwazonsu. Jam’iyyun da suka rage sun hada da APC, PDP, LP, NNPP, SDP, ADC, da sauransu.
Irin su, jam’iyyar matasa (YP) da jam’iyyar Boot (BP) sun sake samun rajista ta hanyar hukuncin kotu, wanda ya nuna yiwuwar kalubale na shari’a nan gaba idan INEC ta ci gaba da jinkirin rajista.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: jam iyyun siyasa
এছাড়াও পড়ুন:
Dan Wasan Gaban Chelsea, Murdyk Ka Iya Shafe Shekaru 4 Ba Tare Da Ya Buga Wasa Ba
Murdyk ya halarci wasan karshe na gasar cin kofin Uefa Conference League da Chelsea ta doke Real Betis a watan da ya gabata, amma kuma ba a cikin tawagar Chelsea ba, a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba, FA ta ce “Za mu iya tabbatar da cewa an tuhumi Mykhailo Mudryk da laifin keta dokar hana kara kuzari, ta hanyar amfani da wani abu da aka haramta, wanda kuma ya sabawa doka ta 3 da 4 a kundin dokokin FA na hana kara kuzari.
Zuwa yanzu Chelsea ba ta ce komai ba dangane da tuhumar da akeyiwa Murdyk amma a watan Disamba ta ce, ta na fatan dan wasan nata yayi nasara duba da cewa “Mykhailo ya tabbatar da cewa bai taba yin amfani da haramtattun abubuwa da gangan ba” tace a cikin sanarwar, a karkashin dokokin FA, yan wasa sunada yancin bukatar ayi masu gwaji na biyu bayan an samu tabbacin amfani da kwayoyi masu kara kuzari a gwajin farko, amma idan gwajin na biyu ya zo daidai da na farko to za a yanke masu hukunci.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp