2025-09-17@23:30:27 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1194

«Lawal Uwais»:

    Kwamatin kananan hukumomi na majalisar dokokin jihar Jigawa ya bukaci ma’aikatar kananan hukumomi da ta karfafa matakan yiwa kananan hukumomin jihar 27 jagoranci akan sha’anin mulki da harkokin kudi domin inganta ayyukan su. Shugaban Kwamatin, Alhaji Aminu Zakari ya yi wannan kiran a karshen ziyarar kwanaki 3 da kwamatin ya yi a ma’aikatar kananan hukumomi...
    Gwamnatin Jigawa ta amince da sabon tsarin ka’idojin aiki domin aiwatar da shirin kula da lafiyar mata masu juna biyu, da jarirai da ƙananan yara kyauta a cibiyoyin lafiya na  jihar. Kwamishinan Yaɗa Labarai, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ya bayyana haka bayan zaman majalisar zartarwa da aka gudanar a gidan gwamnati Dutse. Ya ce ka’idojin...
    Gwamnatin Jihar Jigawa  ta amince da ƙarin kasafin kuɗi na Naira Biliyan 75 na shekarar 2025, ga gwamnatin jiha da kuma ƙananan hukumomi 27. Kwamishinan Yaɗa Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed ne ya bayyana haka jim kaɗan bayan zaman majalisar da aka gudanar a gidan gwamnati dake Dutse, babban...
    Gwamnatin  kasar Iran ta bayyana wasu abubuwan da bata amince da su ba, a jawabin bayan taro na musamman na kungiyar kasashen musulmi ta (OIC) wanda aka gudanar a birnin Doha na kasar Qatar a ranar litinin 15 gawatan Satumba da mukeciki. Sannan ta kara tabbatar da goyon bayanta ga gwagwarmayan da Falasdinawa suke yi...
    A daidaikun kasuwannin Abuja da wasu manyan birane na ƙasar nan, an bayyana yadda farashin doya ke ƙara hawa fiye da yadda ake tsammani.   Wannan na faruwa ne duk da cewa yanzu sabuwar doya ta fara shigowa kasuwa, bisa al’ada, a duk shekara fitowar sabuwar doya kan karya farashin wanda yake kasuwa. Sai dai...
    Gwamnatin Tarayya ta ce Najeriya na rasa sama da Dala Biliyan 10 duk shekara sakamakon asarar amfanin gona bayan girbi. Ministan Noma  Sanata Abubakar Kyari ne ya bayyana haka a wajen kaddamar da shirin Hanyar Inganta Noma da Kayayyakin Mire Rayuwa a Yankunan Karkara G.R.A.I.N a ƙaramar hukumar Birnin Kudu ta  Jihar Jigawa.  ...
    Hukumar Tace Fina-Finai da Dab’i ta Jihar Kano ta haramta shirya duk wata muƙabala tsakanin mawaƙan yabon Annabi (S.A.W), tare da gayyatar mawaƙa Usman Maidubun Isa da Shehi Mai Tajul’izzi su bayyana a gabanta. Hukumar ta kuma gayyaci mawaƙan ne tare da sauran waɗanda suka jagoranci muƙabalar da fitattun mawaƙan biyu suka yi ranar Litinin,...
      Cikin jadawalin GII na 2025, kasashe masu karanci da matsakaicin kudin shiga 17, sun taka rawar gani fiye da yadda aka yi hasashe, bisa matsayin ci gabansu, yayin da kasashen Afirka dake kudu da hamadar Sahara ke kan gaba, cikin kasashe mafiya samun ci gaban kirkire-kirkire, inda kasashen Afirka ta Kudu, da Senegal da...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Matakin hana malaman da ba su da rajista hawa mumbari a Neja yana ci gaba da yamutsa hazo a ciki da wajen jihar. Yayin da wasu suke ganin wannan mataki bai dace ba, wasu kuwa gani suke faduwa ta zo daidai da zama, wato matakin ya zo a...
    Babban daraktan kamfanin dillancin labaran kasar Qatar ya bayyana cewa taron gaggawa na kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC da ke tafe yana nuni da wani muhimmin sauyi na hadin kan kasashen larabawa da musulmi dangane da laifukan da ake aikatawa kan al’ummar Palastinu. A cewar Pars Today, dukkanin idanuwa a ranakun Lahadi da...
    “Sauran motocin da ke cikin ayarin, ciki har da wacce ke ɗauke da shugaban majalisar, da ƙyar suka iya tsayawa wanda tsakaninsu mitoci kaɗan ne daga wurin da haɗarin ya afku,” in ji wani ganau.   Majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa, an garzaya da jami’an ‘yansandan da suka samu raunuka zuwa babban asibitin Gumel...
    A yau Litinin ne tawagogin kasashen Sin da Amurka, suka sake tattaunawa a rana ta biyu, game da batutuwan tattalin arziki da cinikayya a birnin Madrid na kasar Sifaniya. A jiya Lahadi, sassan biyu sun gudanar da zaman farko ne a fadar Santa Cruz, inda ofishin ministan harkokin wajen kasar ta Sifaniya yake. A cewar...
    Rahoton rashin fahimtar da aka fara yadawar, ya biyo bayan taron kwamitin zaman lafiya da kwantar da tarzoma na jihar, wanda Darakta Janar ya jagoranta a ranar 4 ga watan Satumba.   Rashin fahimtar sahihin sakamakon taron ya sa wasu suka rahoto cewa, kwamitin ya dakatar da Malamai daga yin wa’azi.   Sanarwar ta kara...
    Lawal ya ƙara da cewa, ɗaukacin guraren da Jiragen Ruwa ke tsaya, akwai launin da kuma lamba da aka amince,manyan motocin za su rinƙa yin amfani da su, domin yin zirga-zirga  a Tashar ta Apapa. “Misali, a APMT, manyan motocin za su rinƙa yin amfani da lamba  001 mai ɗauke launin ruwan bula, inda kuma...
    Rundunar ‘yansandan jihar Adamawa ta ce ta ceto wasu yara biyar da ake zargin sato su aka yi, daga Maiduguri jihar Borno zuwa Adamawa. Kwamandan yankin na Mubi, ACP Marcos Mancha, a ranar 13 ga Satumba, 2025, a yayin da ya samu wasu bayanan sirri, ya jagoranci tawagarsa inda ya samu wasu yara biyar akan...
    Kona mutanen da suka rasa matsugunansu a cikin tantunansu, a cikin dare mai wahala ga zirin Gaza Da sanyin safiyar Lahadi 14 ga watan Satumban shekara ta 2025 jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra’ila suka ci gaba da kai munanan hare-haren bama-bamai a zirin Gaza, musamman birnin Gaza, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane da jikkata...
    Amurka ta bayyana cewa: Harin da Isra’ila ta kai wa Qatar ba ya barazana ga kawancenta haramtacciyar kasar Isra’ila da Amurka Sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya fada a ranar Asabar din nan cewa: Harin da haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai a Doha babban birnin kasar Qatar a makon jiya ba zai shafi dangantakar...
    Rundunar sojin Isra’ila ta ce ta yi nasarar korar Falasɗinawa sama da mutum 250,000 daga birnin Gaza tun bayan da suka fara zafafa kai hare-hare a yankin. Wannan dai na zuwa ne a yayin da jami’an Falasɗinu suka ce da dama sun gaza ficewa daga kudancin ƙasar saboda cunkoso. Najeriya ta daɗe tana fama da...
    Tsohon kwamandan dakarun IRGC na kasar Iran Mosen Razai ya bayyana cewa kasashen yanking abas ta tsakiya su saurari fadowar boma boman HKI a kan kasashensu idan sun ki daukar matakin hada kai da kuma samar da rundunar kawance don fuskantar haramtacciyar kasar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Rezayi yana fadar...
    A birnin Auckland, babban birnin kasar New Zealanda, dubban mutane sun fito tattaki da jerin gwano don goyon bayan al-ummar Falasdinu a gaza kan kissan kiyashin da HKI take wa mutanen gaza kimani shekaru biyu da suka gabata. Tashar talabejin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa, a jiya Asabar 13 ga watan Satumba...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya sanar da yiwuwar sake yin wani taro da babbar jami’ar kungiyar tarayyar Turai kan harkokin waje Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya sanar da yiwuwar sake ganawa da babbar jami’ar harkokin wajen kungiyar tarayyar turai Kaya Kalas. A cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin jiya...
    Ma’aikatar kula da cinikayya ta Sin ta sanar a yau Juma’a cewa, biyo bayan amincewar kasashen Sin da Amurka, He Lifeng, mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS kuma mataimakin firaministan kasar, zai jagoranci wata tawaga zuwa Spaniya daga ranar 14 zuwa 17 ga watan Satumba, domin tattaunawa da tawagar Amurka. A cewar ma’aikatar, bangarorin...
    Sanarwar ta ƙara da cewa, SABER wani shiri ne na shekaru biyar, wanda ya dogara da aiki, wanda Bankin Funiya ke tallafawa, wanda aka tsara shi cikin tsanaki domin wargaza shingayen faɗuwar jari, da zaburar da sana’o’i masu zaman kansu, da samar da ayyukan yi masu ɗorewa ga al’ummar Zamfara.   Za a raba Naira...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa; Bai kamata a ji tsoron tattaunawa ba saboda hanya ce ta jaddada zaman lafiya Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Ana gudanar da dukkan ayyukan diflomasiyya cikin cikakken hadin kai tare da hukumomin da abin ya shafa, kuma bisa takamaiman umarni da ayyuka. Ya...
    Limamin da ya jagoranci Sallar Juma’a a birnin Tehran ya gargadi kasashen Larabawa game da harin da gwamnatin mamayart Isra’ila ke kaiwa kan kasashe Limamin da ya jagoranci Sallar Juma’a a birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran Ayatullah Sayyid Ahmad Khatami, ya gargadi gwamnatocin kasashen Masar, Jordan, Bahrain da Saudiyya cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila za...
    A yayin da suka yi alƙawarin yin adawa da aiwatar da harajin, ƙungiyar ta ƙara da cewa: “Yajin aiki na kan tebur idan gwamnati ta yi ƙoƙarin watsi da wannan gargaɗi ta ci gaba da aiwatar da waɗannan manufofi. Don haka, TUC ta umarci dukkan kwamitocin jihohi, rassan ƙungiya, da tsarin ta a faɗin ƙasa...
    Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, ya sha alwashin dakile kafa kasar falasdinawa yayin da ya sanya hannu kan yarjejeniyar gaggauta ci gaba da ginin matsugunan yahudawa a yankin El, na yamma da kogin Jordan da Isra’ilan ta mamaye. A jiya Alhamis ne Netanyahu ya sanya hannu kan yarjejeniyar, duk da kashedin da sassan kasa da kasa suka jima...
    An samu ambaliyar ruwa a tituna da dama na tsakiyar Babban Birnin Tarayya Abuja sakamakon mamakon ruwan saman da aka tafka da safiyar Alhamis. Yankunan da ambaliya ta fi shafa sun hada da Asokoro, Guzape, Jabi, Kado da kuma Wuse. Wasu direbobi da suka zanta da Aminiya sun ce sun sha wahala wajen samun hanyar...
    “Gwamnatin Jihar Kaduna ta shirya tsaf domin ɗaukar matakin gaggawa kan kowanne yanayi da ka iya tasowa sakamakon wannan hasashen yanayi. An umurci KADSEMA da ta yi aiki tare da dukkan hukumomi masu ruwa da tsaki domin tabbatar da cikakken shiri. Ana roƙon jama’a da su bi dukkan umarnin kariya, su share magudanan ruwa, kuma...
    Rahotanni daga ma’aikatar kula da albarkatun ruwa ta kasar Sin, na cewa an kara wasu wurare hudu dake kasar Sin, cikin jerin muhimman wuraren ban ruwa na kasa da kasa ko WHIS. Wuraren sun hada da yankin ban ruwa na tafkin Chishan, da gonaki kan tuddai na kabilar Hani na Yuanyang, da madatsar ruwa ta...
    Rabi Laxmi Chitrakar, matar tsohon Firaministan Nepal, Jhalanath Khanal, ta rasu bayan masu zanga-zanga sun banka wa gidansu wuta a unguwar Dallu da ke birnin Kathmandu a ranar Talata. Bayanai sun ce masu zanga-zanga a ƙasar mai tsaunuka da ke fama da tashin hankali mafi muni cikin shekaru da dama sun tarfa matar tsohon firaministan...
    Babban Layin wutar lantarki na Najeriya ya sake faɗuwa. Wannan matsala ta haifar da katsewar wuta a wasu sassan ƙasar, wanda ya jefa masu amfani da lantarki cikin damuwa. Kotun Ghana ta ɗaure ’yan Najeriya 3 shekaru 96 saboda satar mota Mamakon ruwan sama ya hallaka mutum 3 a Zariya Bayanan da Hukumar Gudanar da...
    Babban Layin wutar lantarki na Najeriya ya sake faɗuwa. Wannan matsala ta haifar da katsewar wuta a wasu sassan ƙasar, wanda ya jefa masu amfani da lantarki cikin damuwa. Kotun Ghana ta ɗaure ’yan Najeriya 3 shekaru 96 saboda satar mota Mamakon ruwan sama ya hallaka mutum 3 a Zariya Bayanan da Hukumar Gudanar da...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ba da izinin bayar da wani kaso na kudaden Khumusi ga al’ummar Gaza A matsayin martani ga kuri’ar raba gardama kan halaccin bayar da wani kaso na kudaden Khumusi ga al’ummar Gaza da ake zalunta, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamene’i ya ba da izini na...
    “Jared Sacks” da “Zukiswa Wanner,” marubuta da masu fafutukar al’adu da ke zaune a Cape Town, sun rubuta a cikin wata kasida ga Al Jazeera mai taken “Me yasa za mu je Gaza tare da jiragen ruwa na ‘Sumoud’ na duniya?”: Mun tashi don ci gaba da bege. Rasa bege na nufin watsi da mutanen...
    An samu damar tattauna muhimman abubuwa a babban taron kamar hanyoyin zuba jari a jihohin Ogun da Zamfara na Nijeriya da kuma yankin Bungoma na ƙasar Kenya.   Manyan mambobin kwamitin sun tattauna damarmakin zuba jari a jihohin Ogun da Zamfara a Nijeriya yankin Bungoma na Kenya. A jawabin sa ga masu zuba hannun...
    Ya yi nuni da cewa, dokar za ta bukaci umarnin fara aiki daga ministan kudi kamun a fara.   Edun ya ce, dole ne gwamnati ta zauna tare da masu ruwa da tsaki domin wayar da kan jama’a kafin aiwatar da wannan sabuwar dokar harajin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni...
    Majalisar Dattawa ta sanar da cewa ba ta amince da buƙatar Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan mai wakiltar Kogi ta Tsakiya kan komawa bakin aiki, saboda har yanzu ba a kammala shari’ar dakatar da ita ba. Tun dai a ranar 8 ga watan Agustan bana ne Sanata Natasha ta rubuta wa majalisar wasiƙa, inda ta sanar da...
    Hukumomi sun shawarci jama’a su tabbatar da cewa gidajensu suna da tsaro da karko, tare da kaucewa gina gidaje a kan magudanan ruwa a wannan lokacin na damina. Hukumar Hasashen Yanayi ta Nijeriya (NiMet) ta yi gargaɗin cewa Kirikasamma na daga cikin wuraren da za a iya fuskantar ambaliyar ruwa a bana. Daga kanmu,...
    Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da jami’an Hukumar Kula da Man Fetur ta Nijeriya (NMDPRA), wakilan kungiyar kwadago ta Nijeriya NLC, shuwagabannin kamfanin ‘MRS Holdings Limited’ da kuma kungiyar ‘yan kasuwa ta kasa (TUC).   Da yake bayyana bude taron, Minista Dingyadi ya jaddada aniyar gwamnati na sulhu a tsakanin kungiyar da masu...
    Kwamitin ya kuma jaddada buƙatar wayar da kan jama’a da kamfen ɗin mutunta kai, da haɗa ɗabi’a mai kyau a cikin kundin karatu, da ɗaukar iyaye da ke taimaka wa ‘ya’yansu wajen magudi a matsayin masu laifi. Kwamitin ya gargadi cewa idan ba a ɗauki mataki cikin gaggawa ba, za a ci gaba da lalata...
    Adadin Falasdinawa da suka yi shahada suna da yawa a hare-haren da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan sassa daban-daban na Zirin Gaza a jiya Asabar Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila tana ci gaba da gwabza kazamin yakin da take yi a zirin Gaza a rana ta 701, lamarin da ya yi sanadiyar shahadan Falasdinawa da...
    A wani mataki na tallafawa kasuwanci tsakanin kasashen Afrika an kaddamar da wat kungiyar mai manufartallafawa kasuwanci tsakanin kasashen Afirka tare da saukaka ayyukan raya kasa da sarrafa albarkatun cikin gida. Bankin shigo da kayayyaki na Afirka ne ya kaddamar da kungiyar Don tallafawa kasuwanci, fitar da kayayyaki, da sarrafa albarkatun kasa a Afirka, wanda...
    Ƙungiyoyin makarantu da na addinin Musulunci a Jihar Gombe, sun roƙi gwamnatin jihar da ta sassauta dokar taƙaita hawa babur daga ƙarfe 7 na yamma zuwa 6 na safe, domin sauƙaƙa zirga-zirga yayin bukukuwan Mauludi. Shugaban ƙungiyar makarantun Islamiyya na Jihar, Alhaji Muhammadu Nuhu, ya ce yawancin masu zuwa wajen bukukuwan na amfani da babura...
    Dubban magoya bayan kungiyar Hizbullah ta kasar labanon ne suka gudanar da gagarumar zanga-zanar a cikin dare a birnin berut domin nuna adawa game da shirin Amurka da HKI na neman yan majalisar dokokin kasar su amince da batun kwance dammarar kungiyar hizbullah. Bukatar , wanda manzon musamman na Amurka tom barak  ya mika, da...
    Jam’iyyar APC reshen Jihar Jigawa ta gargaɗi mambobinta da su guji aikata rashin ladabi da halayen da ba su dace ba da za su iya kawo rabuwar kai a cikin jam’iyyar. A cikin wata sanarwa da sakataren jam’iyyar na jiha, Muhammad Dikuma Umar ya sanya wa hannu, APC ta nuna damuwa kan abin da ta...
    Wanda aka kama sunansa iro Garba mai shekaru 25 daga Zangwaye Fulani a ƙaramar hukumar Ajingi a Jihar Kano. Ya amsa cewa shi da wasu mutane huɗu sun yi garkuwa da mutane a Kano, Jigawa da Bauchi. An kuma samu rigunan sojoji guda uku a hannunsa. Kwamishinan ya ce ana ci gaba da ƙoƙarin kama...
    Yakin ya farkar da Sin da duniya baki daya, wanda ya zama tushen kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin a shekarar 1949, daga bisani kuma ya dora kasar bisa tafarkin zamani. Ga duniya, mulkin mallaka ya fara wargajewa. Kasashe da dama sannu a hankali suka fahimci cewa, in sun jajirce, za su samu ‘yancin kai. Tasirin...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, ta sake jaddada haramcin hawa babura daga ƙarfe 7 na dare zuwa 6 na safe, a wani mataki na tsaurara tsaro yayin bikin Mauludi a jihar. Kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya ce Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, CP Bello Yahaya, ya bayyana cewa dokar na da muhimmanci domin hana aikata...
    Mataimakin ministan harkokin wajen Iran mai kula da harkokin siyasa  ya bayyana halin da Iran take ciki kan sabon zagayen tattaunawa Mataimakin ministan harkokin wajen Iran mai kula da harkokin siyasa Majid Takht-Ravanchi ya tabbatar da cewa, ana musayar sakonni tsakanin Iran da Amurka ta hanyar masu shiga tsakani, yana mai cewa maido da zaman...