Saudiya Ta Yi Amfani Da Fasahar AI Don Sauwaka Ayukan Hajjin Shekara ta 2025
Published: 6th, June 2025 GMT
Gwamnatin kasar Saudiya ta yi amfani da fasahar kirkirarren tunani ko (AI) don sauwakawa kanta da kuma mahajjata a hajjin wannan shekara ta 2025, kama daga kula da cinkoson mutane, kiyaye lafiyar mahajjata da haka kuma ta kyautata ayyukan mahajjata a cikin nutsuwa da rashin damuwa.
Jaridar ArabNews ta kasar Saudiya ta bayyana cewa tare da wannan fasahar ta kula da zafin dukkan wuraren da mahajjata zuwa zuwa da kuma hana cinkoson mutane a kewayen Kaaba da sauran wurare.
Jami’I mai kula da bangaren kirkirerren fasaha wato AI na aikin Ajjin bana ya shaidawa Jaridar ArabNews kan cewa sun kirkiro abubuwa da dama don sawwaka aikin hajji ga mahajjata da kuma khidimomin da kasar saudiyya take yiwa mahajjata, Ya ce an yi amfani da wannan fasahar a masallacin Madina da kuma na dakin nKaaba.
Ya ce jami’an shige da fice na kasar Saudiya suna amfani da kayakin aiki na zama a ayyukansu . sannan suna aikin bincike da kansu a tashoshin jiragen sa 11 a kasashen 7 a duniya, inda suke tabbatar da cewa mahajjaci ya cancanci ya je aikin hajji tun daga kasarsu kafin ya shiga jirgi.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
An rufe masana’antu 1,724 bisa rashin bin dokokin aiki a Guinea
Gwamnatin ƙasar Guinea ta rufe wasu sassan kamfanoni guda 1,724 sakamakon kama su da laifin ƙin bin dokokin hukuma, yayin da aka janye kayayyakin da suke sarrafawa daga kasuwa.
Sanarwar na zuwa ne ƙarƙashin ma’aikatar kasuwanci a ƙasar, tana mai cewa an ɗauki matakin ne don kare lafiyar masu sayen kayayyakin da kuma tabbatar da kare muhalli, da kuma tilasta musu biyayya ga dokokin tafiyar da kamfanoni.
Ma’aikatar kasuwanci ta ƙasar ta ce ba shakka wannan mataki zai zama tamkar hannunka mai sanda ga sauran kamfanoni da ke tafiyar da ayyukansu ba dai-dai ba.
Da yake magana shugaban ƙungiyar masu sayen kayayyaki na ƙasar, Ousmane Keita, ya ce tun shekaru sama da uku suke ta wannan kiraye-kiraye, amma ba a sami damar daukar mataki ba sai yanzu.
NAJERIYA A YAU: Yadda tsadar taki ke hana noman masara da shinkafa An wajabta wa ɗaliban firamare mallakar lambar NIN a BauchiA cewar sa ba shakka wannan matakin zai sassauta yadda kamfanonin ke wasa da aikinsu da kuma jefa rayukan jama’a cikin hadari.
Bayanai sun ce a yanzu gwamnati zata mayar da hankali wajen sayawa kamfanonin da ke sarrafa ruwan sha idanun ganin muhimmancinsa ga lafiyar dan Adam.