Sallah: ’Yan sanda sun yi alƙawarin tabbatar da tsaro a Gombe
Published: 5th, June 2025 GMT
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, ta shirya tsare-tsaren tsaro domin ganin an yi Sallar Idi cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya.
Kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya bayyana cewa za a tura ’yan sanda da sauran jami’an tsaro zuwa filayen Idi, Masallatai, da wuraren taro domin kula da tsaro da zirga-zirgar jama’a.
Za a sanya ido sosai a manyan hanyoyi musamman waɗanda ke kai wa zuwa wuraren sallah, domin rage cunkoso da sauƙaƙa zirga-zirgar jama’a.
An ware ƙofofin shiga da fita a filayen Sallah domin a riƙa duba mutane da kayan da suke ɗauke da su.
Rundunar ta kuma roƙi jama’a da su bi waɗannan ƙa’idoji domin kauce wa jinkiri.
’Yan sandan sun gargaɗi mutane da ka da su ajiye motoci ba bisa ƙa’ida ba, sannan su kaucewa yin salla a tsakiyar hanya, ko toshe hanyoyin fita.
Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, ya roƙi mutane da su bayar da haɗin kai wajen bin doka, tare da kasancewa masu lura da duk wani abu da zai kawo barazana.
Ya kuma gargaɗi masu laifi da su guji duk wani abu da zai jawo tashin hankali a jihar.
Hakazalika, ya taya al’ummar Gombe murnar Sallar Idi, tare da tabbatar musu cewa ’yan sanda za su ci gaba da kare lafiyar jama’a domin a yi bukukuwan sallah cikin kwanciyar hankali.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Za a dauke wa jihohin Arewa maso Gabas wutar lantarki na tsawon kwana 4
Kamfanin Dakon Wutar Lantarki na Najeriya (TCN) ya sanar da cewa za a dauke wutar lantarki a ilahirin jihohin yankin Arewa maso Gabas guda shida na tsawon kwana hudu.
A cikin wata wasika da ya aike wa kamfanonin rarraba wutar lantarki da ke kula da jihohin shida, TCN ya ce yayin da a wasu jihohin wutar za ta dauke gaba daya, wasu yankunan kuwa karancin wutar za a samu a tsakanin kwanakin.
Jihohin da lamarin zai shafa sun hada da Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe, Taraba da Yobe.
Kotu ta yi fatali da bukatar Akpabio, ta umarce shi ya biya Natasha N100,000 DAGA LARABA: Dalilan Rashin Jituwa Tsakanin Marasa Lafiya Da Jami’an Kiwon LafiyaWasikar wacce ke dauke da sa hannun Jami’in Gudanarwa na Shiyyar Bauchi a TCN, Injiniya J.O Joseph, wacce aka aike wa daya daga cikin kamfanonin lantarkin, ta ce za a dauke wutar ne sakamakon saka babban layin dakon lantarki mai nauyin 330kV a karamar tashar lantarki da ke Bauchi.
Sanarwar ta kuma ce za a yi aikin gyaran ne daga tsakanin 10 zuwa 14 ga watan Yunin 2025.
Ta kara da cewa, “Yadda aikin zai kasance shi ne kamar haka; za a dauke wuta a layin Jos zuwa Gombe a tsawon wannan lokacin domin a samu damar saka manyan turakun dakon lantarki a sabuwar karamar tashar lantarki mai nauyin 330kV da ke Bauchi.
“Hakan na nufin ba za a sami wutar ba a garuruwan Damaturu, Molai, Yola da Jalingo, yayin da tashoshin lantarkin Gombe da Biu za su sami wutarsu ta cibiyar lantarki da ke Dadin Kowa, ita kuma karamar tashar lantarki da ke Baga Road za ta sami wutarta ne daga MEPP,” in ji sanarwar.