Tsadar Rayuwa: Yadda Al’umma Suka Yi Sallah Cikin Kunci
Published: 6th, June 2025 GMT
An gudanar da sallah ne bayan da Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III ya bayyana ranar Juma’a 06 ga Yuni a matsayin ranar 10 ga watan Zul-Hijja 1446 a matsayin ranar sallar layya kamar yadda ya bayyana a sanarwar da shugaban kwamitin lamurran addinin musulunci kana Wazirin Sakkwato, Farfesa Sambo Wali Junaid ya sanyawa hannu.
A ra’ayin jama’a da dama ba su da halin sayen dabbobin layya da za su yanka, wasu kuwa sun bayyana cewar ko da suna da halin yin layya to ba ita ce a gaban su ba domin a cewarsu za su shiga cikin gagarumar matsala a gidajen su domin mafi yawa ba su tanadi abincin da iyalansu za su ci ba don haka sayen abinci ne mafi muhimmanci.
Talakawa da daman gaske da kanana da matsakaitan ma’aikata da kananan ‘yan kasuwa sun shaidi sallar layya a wannan shekarar a halin da suke fatar kada Allah ya maimaita domin a ta bakin su ba a taba shaidar sallah a matsin tattalin arziki irin ta wannan shekarar ba.
Tashin gwauron- zabi da dabbobin layya suka yi, hauhawar farashin abinci, tsadar man fetur da halin kuncin da jama’a ke ciki duka abubuwa ne muhimmai da suka taru suka dabaibaye sallar ta hanyar hana mata karsashi.
Gagarumar matsalar tsaro ba dare ba rana daga Borno zuwa Sakkwato, tashin bama- bamai, garkuwa da mutane da kisan gillar da ‘yan ta’adda ke yi wa al’umma ba kakkautawa sun yi matukar tasiri wajen hanawa sallah karsashi.
Rahotanni sun tabbatar da cewar tsananin tsadar da dabbobin layya suka yi ya tilastawa jama’a da dama hakura da yin layya domin abincin da za su ci yana kokarin gagarar su wanda ya zama dalilin da ire-iren wadanda suka samu kudin layya to abinci suke siya wanda shine ya fi muhimmanci.
Auwal Balarabe wani matsakaicin ma’aikaci a Abuja ya bayyana cewar wannan layya ce ta farko a tarihin rayuwarsa da aka yi ba ya da halin yanka dabba wanda a cewarsa ya shiga cikin tarihin da ba zai manta ba a dalilin matsin rayuwa.
Wasu maigidanta a Kano sun bayyana cewar ba za su wahalar da kan su sayen ragon dubu 200 zuwa 250 ba, shanu kuwa sai dubu 500 zuwa miliyan daya don haka suka hakura suka zabi sayen kaji da nama.
Mabambantan al’umma sun bayyana halin rashin da aka fuskanta a wannan shekarar da hauhawar farashin raguna da sauran dabbobin layya ya tilastawa mutane da dama hada kudade domin yin hadakar layya ta hanyar sayen babbarn sa ko saniya wadanda suka kai adadin shekaru biyu na layya.
Wani magudanci Isna’il Abubakar a Sakkwato ya bayyana cewar ragon da ya saya a 2024 a dubu 150 a yanzu sai 260, don haka da shi da makwabta hudu sun hada dubu 800 domin sayen saniya su raba.
Bincike a mabambantan kasuwannin karar dabbobi ya nuna an samu karancin masu sayen raguna, shanu da sauran nau’ukan dabbobi sama da shekarun baya kamar yadda masu sayar da raguna a Abuja, Kano, Bauchi, Kaduna, Neja, Gusau, Sakkwato da Birnin- Kebbi suka bayyanawa manema labarai.
“Ba mu taba ganin sallar da jama’a suka kasa yin tururuwar zuwa sayen dabbobi ba irin wannan shekarar, ko kadan babu ko irin rabin hada-hadar da muka saba samu a shekarun baya.”
A cewar Hassan Mahe ko kadan kasuwar dabbobi a bana ta bambanta da saura domin babu kasuwa, kuma duk da tsadar abincin dabbobi, farashin ya karu ne a dalilin hana shigowa da su daga Nijar da gwamnatin kasar ta yi wanda a kan hakan farashin dabbobin ya ninka.
Baya ga wannan matsalar tsaro wadda ta ki ci ta ki cinyewa gagarumar matsala ce wadda ta hanawa bukin sallah armashi a yankuna da dama da ke fama da matsalar tsaro a kasar nan a dalilin hare- haren ta’addanci.
Haka ma dinbin al’ummar da ke tsugune a sansanin ‘yan gudun hijira ko kadan babu maganar kayatarwar shagalin sallah ko yin layya a wajen su, hasalima ranar sallah kan tuna masu da lokutan baya da suka yi sallah cikin walwala da farin ci a muhallansu kuma a cikin iyalan su.
Kayan abinci kamar shinkafa, masara, gero, dawa, wake, fulawa, man gyada, man-ja da nau’ukan tumatur, albasa, attarugu, tattasai da sauransu sun yi matukar tsada lamarin da tsadar a kullum sai gaba-gaba take yi wanda hakan ya taimaka wajen kara rage armashin sallah domin jama’a da dama ba su da wadatar sayen kayan bukatu.
Maigidanta da dama a tattanawarsu da LEADERSHIP Hausa sun bayyana fatar samun saukin al’amurra ta yadda dabbobi da kayan abinci da na bukatu za su sauko kasa akasin shekaru biyu da suka gabata zuwa yanzu da al’amurra suka tabarbare har jama’a suka shiga cikin kunci maras misaltuwa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: wannan shekarar dabbobin layya bayyana cewar sun bayyana
এছাড়াও পড়ুন:
An Kashe Wasu ‘Yan Bindiga 12, An Kwato Makamai A Katsina
Da take aiwatar da rahotannin sirri cikin gaggawa, rundunar hadin gwiwa da ta kunshi jami’an ‘yansandan Nijeriya, Sojoji, jami’an kula da jama’a na jihar, da ’yan banga na yankin sun bi sawun barayin da suka tsere zuwa Dutsen Falale da ke yankin Kurfi-Safana inda aka yi musayar wuta mai tsanani, wanda ya yi sanadin mutuwar ‘yan bindigar 12.
Sai dai kuma, yayin da yake yabawa wannan bajinta da jajircewa da jami’an tsaron suka yi, Dakta Mua’zu ya bayyana matukar alhininsa game da rasuwar wani dan banga mai suna Alhaji Danmalam wanda ya rasa ransa a fafatawar.
Bugu da kari, soja guda ya samu raunuka kuma a halin yanzu yana samun kulawa a Asibiti.
Alhaji Danmalam ya rasu ne sakamakon harbin bindiga a cibiyar kiwon lafiya ta matakin farko da ke Charanchi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp