Yadda Rarrabuwar Kawunan Jam’iyyu Zai Iya Sauya Alkiblar Zaben 2027
Published: 7th, June 2025 GMT
A wasu lokuta, matsalolin suna fitowa kai tsaye sakamakon rashin fahimta daga mataki na kasa, wadada a wasu lokutan ba su da wata alaka da sakatariyar jam’iyyun da ke mataki na sama.
Ko a cikin jam’iyyar APC da ke mulki, akwai jayayya a cikin rassan jihohinta da ba su warware ba kuma suna barazanar ga damar jam’iyyar a jihohin da abin ya shafa.
Wasu masana harkokin siyasa sun bayyana cewa rarrabuwar kawunan ta samu ne sakamakon nuna iko tsakanin wasu mutane a wasu jihohi. Akwai batun wanda ke da iko da tsarin jam’iyyar shi ne shugaban jam’iyyar a jihar.
Yayin da wasu ke cewa wannan shi ne tushen da ya haifar da rarrabuwar kawuna da ke faruwa a cikin tsarin jam’iyyun a jihohi, inda jiga-jigan ‘yan siyasa ke ta kokarin mallakar masu ruwa da tsaki na jam’iyya ta yadda za sus amu damar kulawa da jam’iyyun a jihohinsu.
Masana harkikin siyasa na ganin cewa idan har abubuwa ba su Sanya ba, to za a fuskanci matsaloli a tsakanin mambobin jam’iyya a lokacin zaben fid da gwani, wanda hakan na iya shafar zaben 2027.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
An tattauna yadda za a inganta walwalar malamai a Gombe
Ƙungiyar Malaman Makarantu ta Najeriya (NUT) reshen Jihar Gombe, ta ziyarci shugaban ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomi na jihar, Barista Sani Ahmad Haruna, a ofishinsa da ke Gombe.
Shugaban ƙungiyar, wanda shi ne shugaban Ƙaramar Hukumar Gombe, ya bayyana cewa gwamnati da shugabannin ƙananan hukumomi za su ci gaba da yin duk mai yiwuwa wajen inganta walwalar malamai.
Tinubu ya janye dokar ta-ɓaci da ya sanya a Ribas Saudiyya ta saki ’yan Najeriya 3 da ta kama kan zargin safarar miyagun ƙwayoyiYa ce: “Ba za mu taɓa barin malamai su shiga cikin matsanancin hali ba. Za mu duba matsalolinsu domin tabbatar da walwalarsu da ci gaban ilimi a jihar.”
Sani, ya kuma yaba da yadda NUT ke tattaunawa cikin lumana da kawo shawarwari maimakon ɗaukar matakan da za su iya kawo tsaiko ga harkar ilimi.
A nasa jawabin, shugaban NUT na jihar ya ce sun kai ziyarar ne domin tattauna matsalolin da malamai ke fuskanta, musamman na makarantun firamare da ƙananun sakandare da ke ƙarƙashin kulawar ƙananan hukumomi.
Ya ƙara da cewa manufar NUT ita ce samar da fahimtar juna da haɗin kai tsakaninsu da shugabannin ƙananan hukumomi domin gano hanyoyin magance matsaloli cikin lumana.