Turkiya: Akwai Fatan Yiyuwar A Dakatar Da Yaki Tsakanin Rasha Da Ukiraniya
Published: 3rd, June 2025 GMT
Ofishin shugaban kasar Turkiya, ya bayyana fatan cewa tattaunawar da ake yi a tsakanin Rasha da Ukiraniya a birnin Istanbul, za ta kai ga tsayar da tsagaita budewa juna wuta wanda kuma zai ga, kawo karshen yakin baki daya.
Ofishin shugaban kasar Turkiya ya bayyana haka a yau Talata, ta kuma kara da cewa,; Tattaunawar da aka gudanar a jiya Litinin a tsakanin Rasha da Ukiraniya a kuma fadar shugaban kasar Turkiyya dake birnin Istanbul tana cike da fata na tsayar da yakin.
Kamfanin dilalncin labarun “Sputnik” na kasar rasha ya ambato majiyar fadar shugaban kasar ta Turkiya tana cewa; Shakka babu duk wata tattaunawa da bangarori za su zauna akan teburi, tana tattare da kyakkyawan fata, a dalilin haka, da akwai kyakkyawar fatan kai wa ga daina yaki.
Dama dai tun a jiya Litinin ne ministan harkokin wajen Turkiya, Hakan Fidan ya yi fatan ganin tattaunawar ta kai ga sakamakon da ake nema a cikin kankanen lokaci.
A nashi bangaren, jagoran tawagar Rasha a wajen tattaunawar Vladimir Medinsky ya fada wa taron manema labaru kan cewa; Rasha ta gabatar da tata mahangar a kan yadda take ganin ya kamata a kawo karshen yakin.”
Haka nan kuma ya ce, sun gabatarwa da Turkiya mahangar mai bangarori biyu, ta farko ita ce, yadda za a shimfida zaman lafiya maidorewa, ta biyu kuma kan yadda za a tsayar da wutar yaki.”
An fara bude tattaunawa tsakanin Rasha da Ukiraniya ne, a ranar 16 ga watan Mayun da ya gabata, wanda ya kai ga cimma matsaya a kan wasu batutuwa da su ka hada da musayar fursunoni.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Rasha da Ukiraniya shugaban kasar
এছাড়াও পড়ুন:
Jami’an Kasashen Rasha, China, Iran Sun Gudanar Da Taron Hadin Gwiwa A Tehran
Kasashen Iran, Rasha, da China sun gudanar da wani taro a birnin Tehran, inda suka tattauna batutuwan da suka shafi Shirin Iran na nukiliya da kuma dage takunkumin da aka kakaba mata.
Taron kasashen ya tabbatar da aniyarsu ta ci gaba da yin hadin gwiwa da tuntubar juna a cikin lokuta masu zuwa.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya bayar da rahoton cewa, a wannan Talata 22 ga watan Yuli 2025, aka gudanar da taron tawagogin kasashen uku.
Mahalarta taron a karkashin inuwar ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran, sun tabbatar da aniyar kasashensu na ci gaba da yin hadin gwiwa tare da yin musayar ra’ayi kan batutuwan da suka shafi yarjejeniyar nukiliyar.
Sun kuma jaddada muhimmancin ci gaba da wannan shawarwari domin biyan muradun kasashen uku wajen tinkarar manufofin kasashen yamma, musamman takunkuman Amurka.
Tawagogin sun amince su ci gaba da bude hanyoyin karfafa alakokinsu da kuma ci gaba da gudanar da taruka a nan gaba a matakai daban-daban a cikin makonni masu zuwa, a wani bangare na abin da suka bayyana da “kokarin hadin gwiwa na tallafawa zaman lafiyar yankin da inganta hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare.”