Ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi ya sanar da cewa, nan da kwanaki masu zuwa Iran za ta mayar da amsa kan shawarar da Amurka ta gabatar kan shirin nukiliyar kasar na zaman lafiya.

A cewarsa, shawara da Amurka ta gabatar tana bukatar zurfafa bincike.

M. Araghchi, ya bayyana hakan ne ziyarar da yake a birnin Beirut, na kasar Lebanon inda ya jaddada cewa, amsar da Iran za ta mayar zata kasance bisa tsarin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da manufofinmu da kuma kare muradun al’ummar Iran.

Ya nanata cewa inganta makamashin Uranium tamkar “jan layi” ne ga Iran, yana mai cewa Tehran ba ta bukatar neman izini daga kowa don ci gaba da ayyukanta da suka dace da shari’a kuma halaliyarta.

Ya ce inganta sinadarin Uranium ya zama abin alfahari ga al’ummar Iran kuma wannan nasara ta ilimi ta samo asali ne daga kokari da basirar masana kimiyyar Iran, kuma ba abu ne mai sauki da za a yi watsi da ita.

Araghchi ya kuma tunatar da cewa, Iran ta ta sha wahala sosai fiye sakamakon shekaru 20 na takunkumin tattalin arziki mai tsanani da Amurka ta kakaba, da kuma kisan wasu masana kimiyyar nukiliyarta tun farkon shekarun 2010, wanda jami’an gwamnatin Isra’ila suka shirya.

Ministan harkokin wajen na Iran ya kara da cewa sama da Iraniyawa miliyan daya ne ke bukatar magunguna da cibiyar bincike ta Tehran ta samar, don haka ci gaba da sarrafa sinadarin Uranium a Iran ya zama wajibi.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Saudiyya Ta Saki ‘Yan Nijeriya 3 Da Ta Kama Bisa Kuskuren Safarar Ƙwayoyi

Hukumar NDLEA ta bayyana cewa wata ƙungiyar masu safarar miyagun ƙwayoyi ce a filin jirgin sama na Kano ta boye jakunkunan ƙwayoyi a cikin kayan matafiyan.

An kama shugaban ƙungiyar, Ali Abubakar Mohammed (wanda aka fi sani da Bello Karama), tare da wasu abokan aikinsa.

Hukumar ta ce mutanen ukun ba su da laifi kuma an zalunce su ne kawai.

An saki su ne bayan bincike da kuma ƙoƙarin diflomasiyya na tsawon makonni.

Lamarin ya tayar da hankali kan tsaro a filayen jirgin sama a Nijeriya da yadda masu aikata laifuka ke amfani da fasinjoji marasa laifi.

Hukumar ta ce za a ɗauki ƙarin matakai don hana faruwar irin wannan lamari.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kwara ETF Ya Dauki Nauyin Karatun Fitattun Dalibai A Matakin Sakandare
  • Guterres: Jerin Shawarwarin Da Sin Ta Gabatar Sun Cika Ka’idar Kundin Tsarin Majalisar Dinkin Duniya
  • Saudiyya Ta Saki ‘Yan Nijeriya 3 Da Aka Yi Wa Sharrin Safarar Ƙwayoyi
  • Saudiyya Ta Saki ‘Yan Nijeriya 3 Da Ta Kama Bisa Kuskuren Safarar Ƙwayoyi
  • Shawarwarin Sin: Ingantattun Hanyoyi Masu Sauki Na Warware Sabani
  • Shawarar Inganta Jagorancin Duniya Ta Haifar Da Damar Wanzar Da Daidaito Da Adalci
  • Tawagar Yan Wasan Damben Gargajiya Ta Iran Ta Zama Zakara A Damben Ta Duniya
  • Taron Doha: Daga matakin Allawadai zuwa matakan kalubalantar laifukan Isra’ila
  • Ministan Tsaron Kasar venezuela Ya Gargadi Amurka Dangane Da Kokarin Juyin Mulki A Kasar
  • Pezeshkian: Ya kamata kasashen musulmi su yanke alaka da gwamnatin sahyoniya tare da kiyaye hadin kai