Jami’an Tsaro Sun Ceto Mutane 11 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Katsina
Published: 9th, June 2025 GMT
Ya ce dukkan wadanda aka sacen, da suka hada da mata 9 da maza 2, an kubutar da su ba tare da wani rauni ba.
PPROn ya bayyana cewa, a halin yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike don ganowa tare da cafke ‘yan bindigar da suka tsere, inda rundunar ‘yansandan ta sha alwashin ci gaba da matsa lamba kan masu aikata laifuka a jihar.
ceto mutane 11 da aka yi garkuwa da su a Katsina
Rundunar ‘yansandan jihar Katsina tare da hadin gwiwar wasu jami’an tsaro sun yi nasarar ceto mutane 11 daga hannun masu garkuwa da mutane a daren Lahadi 8 ga watan Yuni 2025.
Wannan nasarar an sameta ne da misalin karfe 10:30 na dare a hanyar kauyen Danmusa zuwa Mara Dangeza a karamar hukumar Danmusa biyo bayan wani sintiri da rundunar hadin gwiwa ta jami’an tsaro ke yi a hanyar.
Tawagar ta hada da jami’an ‘yansanda, jami’an tsaro na farin kaya (DSS), Operation Sharan Daji, da hukumar kula da al’umma ta jihar Katsina (KSCWC), da kuma ‘yan banga na yankin.
A cewar wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar (PPRO), DSP Abubakar Sadiq Aliyu, ya fitar, ta ce rundunar tsaron ta ci karo da wasu gungun ‘yan bindiga da ke yunkurin tserewa da wadanda suka sace daga sassa daban-daban na jihar.
Aliyu ya bayyana cewa, an yi musayar wuta, wanda ya tilastawa ‘yan bindigar tserewa tare da barin wadanda suka yi garkuwa da su a dajin.
Ya ce dukkan wadanda aka sacen, da suka hada da mata 9 da maza 2, an kubutar da su ba tare da wani rauni ba.
PPROn ya bayyana cewa, a halin yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike don ganowa tare da cafke ‘yan bindigar da suka tsere, inda rundunar ‘yansandan ta sha alwashin ci gaba da matsa lamba kan masu aikata laifuka a jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Gidauniyar IRM Da KADCHMA, Ta Ƙaddamar Da Inshorar Lafiya Kyauta Ga Mutane 200 A Kaduna
Da yake kaddamar da shirin, Darakta Janar na IRM, Alhaji Anas Muhammad, ya ce an kirkiro da shirin ne domin karfafa zaman lafiya da hadin kai ta hanyar tallafa wa Musulmai da Kiristoci ta bangaren samar da kiwon lafiya da bayar da tallafin kayan abinci da jari.
Ya ce: “Kalubalen lafiya ba sa bambance addini ko kabila, don haka bama bambantawa wajen bayar da tallafin. in sha Allah zamu ci gaba da aiwatar da irin wannan shiri a fadin jihar Kaduna baki daya.”
A nasa jawabin, Shugaban hukumar KADCHMA, Malam Abubakar Hassan, ya bayyana cewa wannan hadin gwiwa tana nuna muhimmancin dangantaka tsakanin gwamnati da kungiyoyi masu zaman kansu wajen cimma dorewar tsarin inshorar lafiya ga kowa.
Ya kara da cewa kaddamar da inshorar lafiya kyauta na shekara guda babban ci gaba ne a cikin gyaran fannin lafiya da ake gudanarwa a jihar, inda ya yaba da kokarin gidauniyar IRM wajen tallafawa rayuwar al’ummar Kaduna – Musulmai da Kiristoci.
Wasu daga cikin wadanda suka amfana da shirin daga Kungiyar Kiristoci ta Nijeriya (CAN) reshen Kaduna da kuma kungiyar ci gaba ta Darikar Tijjaniyya ta jihar Kaduna sun bayyana farin ciki da godiya ga gidauniyar da kuma gwamnatin jihar, inda suka ce inshorar lafiya kyauta za ta rage musu nauyin kashe kudin magani tare da karfafa hadin kai a tsakanin al’umma da samar da zaman lafiya.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA