Iran: Matakan Washington Na Hana ‘Yan Kasashen Musulmi Shiga Amurka Kiyayya Ce
Published: 7th, June 2025 GMT
Ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran, ta bayyana cewa; Matakin da Amurka ta dauka na kakaba takunkumin shiga Amurka akan wasu ‘yan kasa da kuma wasu kasashen musulmi yana nuni da yadda Amurkan take adawa da musulmi.
Haka nan kuma ma’aikatar harkokin wajen ta Iran ta ce; Daukin matakin hana wasu mutane yin tafiya saboda kasar da su ka fito, ko addininsu yana nuni ne da yadda Amekin take jin fifiko da kuma nuna wariya.
A karshe ma’aikatar harkokin wajen ta Iran ta yi kira ga MDD da sauran cibiyoyin kasa da kasa na shari’a da su dauki mataki karara kuma a fili akan abinda Amurka ta yi, da ya sabawa duk wani ma’auni na ‘yan adamtaka.
A ranar Alhamis din da ta gabata ne dai shugaban kasar Amurka Donald Trump ya rattaba hannu akan wata doka wacce ta hana ‘yan kasashe 12 shiga cikin Amurka, da kuma kafa tarnaki akan wasu ‘yan kasashen 7. Fadar White House ta Amurka ta bayyana wannan matakin da ta dauka akan cewa; manufarsa shi ne kare tsaron kasar Amurka.
Kasashen da takunkumin shiga Amurkan ya shafa sun hada Afghanistan, Myanmar, Chadi, DRC, Equatorial Guinea, Eritria, Iran, Libya, Somaliya, Sudan da Yemen.
Su kuwa wadanda aka yi msu tarnaki ,sun kunshi Brundi, Cuba, Laos, Saliyo, Togo, Turkimanestan da kuma Venezuela.
Shugaban na kasar Amurka ya kuma kara da cewa; Abu ne mai yiyuwa anan gaba a kara shigar da wasu kasashen.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Ce; Iran Ba Zata Bar Tace Sinadarin Uranium Ba
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya jaddada cewa: Iran ba za ta iya watsi da shirinta na inganta sinadarin Uranium ba
Ministan harkokin wajen na Iran ya fada a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Fox News cewa: Har yanzu ba a dakatar da inganta sinadarin Uranium ba a Iran, duk da irin barnar da aka mata bayan hare-haren da Amurka ta yi mata mai tsanani.
A cikin wata hira da gidan talabijin na Fox News, Araqchi ya ce, “Shin shirin inganta sinadarin Uranium a Iran ya dawo? Shin har yanzu wannan shirin yana ci gaba, ko kuwa barnar da aka yi ta yi tsanani har ta kai ga dakatar da shi gaba daya?” Ya ce: “Ba a dakatar da shi ba, duk da cewa barnar ta yi muni da yawa, amma ba shakka ba za a iya yin watsi da Shirin inganta sinadarin Uranium ba, domin wannan nasara ce ta masana kimiyyar Iran, kuma a halin yanzu abin alfahari ne ga kasar, kuma inganta sinadarin Uranium yana da matukar muhimmanci a gare ta.”
Ministan harkokin wajen na Iran ya kara da cewa: “Iran ba zata taba matsawa wajen inganta sinadarin uranium da kashi 90 cikin dari ba. Iran ta himmatu wajen tabbatar da samar da makamashin Uranium kasa da kashi 5% domin samar da makamashin nukiliya. Kuma tana inganta sinadarin na Uranium zuwa kashi 20% saboda tana da injin binciken TRR.”