Fiye Da Falasdinawa 90 Ne Su Ka Yi Shahada A Cikin Sa’o’i 24 Da Su Ka Gabata
Published: 8th, June 2025 GMT
Rahotanni daga Gaza sun ambaci cewa a cikin sa’o’i 24 da su ka gabata adadin Falasdinawan da su ka yi shahada sun kai 91. Mafi yawancin shahidan dai sun kwanta dama ne sanadiyyar hare-haren da sojojin HKI su ka kai musu a wuraren da aka ware na raba kayan agaji da ‘Yan Sahayoniya da Amurkawa suke tafiyar da su.
Bugu da kari, sojojin Amurka da suke a mashigar “Natasrim” sun ce; sun yi amfani da hayakin mai burkono akan fararen hulan Falasdinawa da suke gogoriyon samun abinci.
A yammacin Rafaha dake kudancin Gaza, Falasdinawa 4 ne su ka yi shahada a wurin raba kayan agaji yayin da wasu 70 su ka jikkata.
Tashar talabijin din ‘almaydin’ ta bayar da labarin dake cewa; Wani Bafalasdine guda daya ya yi shahada sanadiyyar bude masa wuta da sojojin mamaya su ka yi a mashigar “Natsrim” a yayin da yake kokarin isa inda zai sami abinci.
Shaidun ganin ido sun ce sojojin Amurka da suke a cikin wurin raba kayan agajin dake kudancin ” Natsarim” sun yi amfani da hayaki mai borkono akan fararen hula, da hakan ya sa da dama daga cikinsu su ka shake. An dauki da dama daga cikinsu zuwa asibitocin “Shuhada’ul-Aqsa’ da kuma “Audah” dake sansanin ‘yan hijira na Nusairat.
Dama dai kungiyar Hamas ta bayyana cewa; cibiyoyin raba kayan agaji da HKI da Amurka suke tafiyar da shi, ya zama wani tarko ne na kashe Falasdinawa. Kungiyoyin kasa da kasa da su ka hada da MDD sun ki amincewa da su yi aiki a karkashin Amurka da HKI wajen raba kayan agajin saboda sun ce, yana da manufa ta soja da kuma korar Falasdinawa daga gidajensu.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Bokoharam Ta Kashe Sojojin Kamaru Ta Hanyar Amfani Da Jirgin Sama Maras Matuki
Majiyar tsaron kasar ta Kamaru sanar da cewa, da dama daga cikin sojojin kasar sun rasa rayukansu sanadiyyar wani hari da kungiyar Bokoharam ta kai musu ta hanyar amfani da manyan bindigogi da kuma jirgin sama maras matuki akan iyaka da Najeriya.
Majiyar ta ce an kai harin ne a yankin Sagami dake kusa da tafkin Chadi a gundumar Logun mai iyaka da kasar Najeriya.
Ita dai kungiyar Bokoharam ta addabi kasashen Najeriya, Kamaru da kuma jamhuriyar Nijar. Yankun arewacin kasar ta Kamaru ya fara fuskantar kai hare-hare daga wannan kungiyar ne tun a 2014 wanda kuma har yanzu yana ci gaba da faruwa daga lokaci zuwa lokaci.