Tsarin Jam’iyya Daya Ba Barazana Ba Ce Ga Tsarin Dimokuradiyyar Nijeriya – Gwamna Namadi
Published: 7th, June 2025 GMT
Yanzu mun yi hakan a kananan Hukumomi takwas,zuwa Lahadi mai zuwa,zamu je ta tare. Zamu ci gaba da yin hakan har zuwa watan Nuwamba wanda hakan zai sa mu kammala da kananan Hukumomi 27. Zuwa yanzu ana ganin amfanin abinda aka yi,a duk kananan Hukumomi da muka ziyarta. Ina ganin mun yi rawar gani kan muradai 12,amma kamar yadda na ce al’ummar Jigawa sune wadanda ya dace su yi bayani kan irin ayyukan alkhairi da ci gaban da muka yi a matsayinmu na gwamnati.
Da aka yi ma shi maganar ya ware kashi 30 cikin 100 saboda bangaren ilimi,cewa ya yi ai Jigawa Jiha ce da take da manoma. Domin kuwa kusan kashi 85 zuwa 90 na yawan al’ummar manoma ne. Duk wata gwamnatin da take bukatar bunkasa tattali arzikin Jigawa da kuma jin dadin zamantakewar al’ummarta dole ne ta maida hankali kan aikin noma. Fannin akin noma shi yake samar da kashi 46 cikin 100 kudaden shiga na gwamnati a shekara.Ina farin ciki na fadi hakan cewar abinda muke yi yayi matukar bunkasa tattalin arzikin Jihar Jigawa, Gaskiya daukar matakin yin hakan ko shakka babu ya bunkasa jin dadin rayuwra al’ummarmu. Maganar gaskiya tsarin ya rage yawan wadanda suke zuwa Birane daga Kauyuka a cikin Jihar. Matasa yanzu sun amince da harkar noma ita ce babbar lamarin kasuwanci amma ba irin noman da mutum zai noma saboda shi kadai ba.Shi yasa muka bada muhimmanci da maida hankali kan noma da komawa gona.
Shi kuma ilimi wani babban ginshikin ci gaban rayuwa ne, ta kowane al’umma na duniya,amma ba sai Jihar Jigawa kawai ba.Shi,yasa muke ganin da akwai muhimmanci da kuma bukatar mu ilimantar da al’ummar mu, saboda kuwa mun san da zarar mun ilimantar da su, musamman ma matasa,wadanda sune za su kasance Shugabannin gobe. Shi yasa lamarin ilimi ma shi ma muka bashi muhimmanci. Domin ai muna da tsare tsaren na lamarin daya shafi ilimin. A babban bangaren ilimin, mun kaddamar da tsarin da ya shafi kafar sadarwa ta zamani a ilmance,ba,abin ya tsaya a samar da ilimi ga al’ummar ba,abin ma yana taimaka mana kan lamarin rashin zuwa aiki na Malaman makaranta.
Bugu da kari an amfana da shi wajen horon su Malaman.Zuwa yanzu,mun haorar da fiye da Malaman makaranta12,a karkashin shi tsarin.
Hakanan ma mun bullo da tsari na rage yawan yaran da basu zuwa makaranta, shi yasa ma muka bullo da tsarin Tsangaya, saboda kuwa Hukuma ce wadda ta fara aiki.Abinda muke yi shi ne mu tabbatar da duk yara a Jihar Jigawa,wadanda basu zuwa makaranta, an dawo da su makaranta.Mun samu nasrara yin hakan.Tsarin Tsangaya ya amince da masu ruwa da tsaki za a koyar da abubuwa uku:lamarin kirga da kuma yakar jahilci na kwana biyu,ilimin addii na kwana uku,sai kuma ilimin koyon sana’a na kwana daya.Tsarin makaranta na Tsangaya zai bada dukkannin abubuwan da suka zama dole wadanda kuma za su taimakawa masu karatu wajen samar da ilimin fasaha da kuma koyon sana’oi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Sin: Katsalandan Cikin Harkokin Kamfani Da Netherlands Ta Yi Ya Kawo Tsaiko Ga Tsarin Masana’antu Da Samar Da Kayayyaki Na Duniya
Ya ce Sin tana maraba da kamfanonin dake fuskantar kalubale su tuntubi ma’aikatar ko hukumomi masu ruwa da tsaki, yana cewa, ma’aikatar za ta nazarci ainihin abubuwan dake faruwa da kuma bayar da damar fitar da kayayyaki ga wadanda suka cancanta. (Mai fassara: FMM)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA