2027: An Yi Kira Ga Masu Mulki Da Su Rungumi Tafarkin Inganta Rayuwar Al’umma
Published: 7th, June 2025 GMT
Sun dora alhakin haka kan Shugabannin majalisar kasa wadanda sune suka yarda,da irin yadda lamuraran ke tafiya a majalisar.
Shugabnnin jam’iyyun adawa (PDP) da kuma (LP) sun zargi jam’iyya (APC) wadda take samar da matsala a jam’iyyun domin ta maida Nijeriya mai bin tafarkin jam’iyya daya.
Wannan ya bullo ne bayan da aka samu komawa ita jam’iyyar APC daga jam’iyyun adawa,ba domin komai ba sai saboda irin rigingimun cikin gida wadanda suka faru.
Wasu kafofin yada labarai sun bada rahoton cewa akwai ‘yan adawa fiye da 300 suka bar jam’iyyar PDP da sauran wasu jam’iyyun adawa zuwa APC tun dga shekarar 2023.
Yayin da dukkan sauya shekar siyasa abin ya faru ne a majalisun gwamnatin tarayya dana Jihohi, rushewar jam’yyar PDP da dukkannin abubuwanta zuwa APC a Jihar Delta,karkashin jagorancin gwamna Sheriff Oborebwori,wannan shi ne babban barin wata jam’iyyar siyasa zuwa wata wanda ana iya cewar ita ce ficewa daga jam’iyya da ta fi tayar da hankali.
Gwamann Jihar Akwa Ibom Umo Eno shi ma ana ta rade- raden cewar nan bada jimawa ba zai koma APC ,yayin dai lamarin ya kara kamari domin da akwai wsu manyan jiga- jigan da ake sa ran za su koma jam’iyya mai mulki.
Sai dai kuma maganganun da Shugaban jam’iyyar APC, Dakta Abdullahi Ganduje’ sun jawo ma shi caccaka dangane da hakan.
Shi ma Shugaban kasa Bola Tinubu bada dadewa ba a wani taron jam’iyyar,yace tsarin jam’iyya daya bai da kyau ga mulkin farar hula;amma kuma ba hawan ba saukar a wani babin na shi yace ana maraba da dk wanda yake son dawowa jam’iyyar, saboda ai tsarin mulki ne ya bada damar ‘yancin yin hakan.
Halin da ake ciki yanzu Nijeriya tafiyar da mulkin farar hula mai jam’iyyun siyasa da aka yi wa rajista 18.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Rikicin PDP: Tsagin Wike ya dakatar da Damagum
Rikicin jam’iyyar PDP ya ƙara tsananta bayan sakataren jam’iyyar na ƙasa, Sanata Samuel Anyanwu, ya sanar da dakatar da shugaban jam’iyyar na ƙasa, Ambasada Illiya Damagum.
Yayin da yake yi wa manema labarai jawabi a Abuja, Anyanwu, wanda yake ɗan tsagin Nyesom Wike, ya ce an dakatar da Damagum da wasu manyan jami’an jam’iyyar guda biyar saboda zargin rashin ƙwarewa, almundahana, da ƙin bin hukuncin kotu.
Kiristoci: Najeriya ba ta yadda da cin zarafin addini ba — Tinubu PDP ta dakatar da Anyanwu da wasu ’yan tsagin Wike“Mun yanke shawarar dakatar da shugaban jam’iyyar na ƙasa, Ambasada Ilya Damagum, saboda rashin ƙwarewa, almundahana, da ƙin mutunta hukuncin kotu,” in ji Anyanwu.
“An dakatar da shi na tsawon wata guda, kuma dole ne ya gurfana gaban kwamitin ladabtarwa.”
Anyanwu, ya kuma yaba da hukuncin kotu wanda ya soke babban taron jam’iyyar na ƙasa, inda ya bayyana cewa wannan nasara ce ga mambobin PDP baki ɗaya.
“Muna jinjina wa ɓangaren shari’a bisa wannan hukunci da ya nuna adawa da zalunci da rashin bin doka. Wannan nasara ce ga kowane ɗan jam’iyyar PDP,” in ji shi.
Sauran da aka dakatar sun haɗa da mai magana da yawun jam’iyyar na ƙasa, Debo Ologunagba; mataimakin shugaban jam’iyyar na Kudu, Taofeek Arapaja.
Akwai kuma sakataren kuɗi na ƙasa, Daniel Woyenguikoro; jagoran matasan jam’iyyar, Sulaiman Kadade da mataimakin sakataren jam’iyyar na ƙasa, Setonji Koshoedo.
Sanarwar Anyanwu, na zuwa ne bayan ɓangaren Damagum ya dakatar da shi da wasu magoya bayan Wike, lamarin da ya ƙara ba tsananta rikicin shugabanci a jam’iyyar PDP.
Anyanwu, ya kuma sanar da naɗa Alhaji Abdulrahman Mohammed, mataimakin shugaban jam’iyyar na yankin Arewa ta Tsakiya, a matsayin sabon muƙaddashin shugaban jam’iyyar.