A yau Litinin 9 ga wata ne memban hukumar siyasa ta kwamitin kolin JKS, kana mataimakin firaministan kasar Sin He Lifeng, da jami’an bangaren Amurka, suka halarci taron farko na tattauna batutuwan tattalin arziki da cinikayya na Sin da Amurka, wanda aka kaddamar a birnin London dake kasar Birtaniya. (Zainab Zhang)

Daga kanmu, magana ta ƙare.

Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Wakilin Sin Ya Yi Kira A Yayyafa Ruwa Ga Rikicin Isra’ila Da Iran

Wakilin dindindin na kasar Sin a MDD ya yi kiran hada karfi da karfe a bangaren kasa da kasa don karfafa tattaunawa domin ganin an yayyafa ruwa ga rikicin Isra’ila da Iran.

Wakilin, Fu Cong ya ce, yayin da rikicin yake-yaken sojoji na Isra’ila da Iran ya shiga kwana na takwas, abin bakin ciki ne ganin yadda lamarin yake janyo asarar rayukan fararen hula da dama tare da lalata kayayyakin aiki a dukkan bangarorin biyu.

Ya kara da cewa, idan har wutar rikicin ta ci gaba da ruruwa, ba kawai bangarorin biyu ne za su tafka babbar asara ba, hatta sauran kasashen yankin lamarin zai yi musu mummunar illa.

Fu Cong, ya fada wa wani taron gaggawa na kwamitin sulhun MDD cewa, matakin da Isra’ila ta dauka ya saba wa dokokin duniya da ka’idojin huldar kasa da kasa, yana kuma kawo cikas ga ‘yancin kai da tsaron kasar Iran, tare da yin kafar ungulu ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin. Kuma ba tare da wata shakka ba, kasar Sin ta yi Allah wadai da hakan. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sin Ta Yi Matukar Allah Wadai Da Hare-Haren Da Amurka Ta Kaiwa Iran
  • CMG Ya Ja Hankulan Baki A Dandalin Tattaunawar Tattalin Arziki Na Kasa Da Kasa Na St. Petersburg Karo Na 28 
  • Yankin Taiwan Ya Yi Taron Bikin Bauta Na Kakan Gargajiyar Sin Fuxi
  • Wakilin Sin Ya Yi Kira A Yayyafa Ruwa Ga Rikicin Isra’ila Da Iran
  • Jakadan Sin Dake Amurka Ya Yi Jawabi A Gun Liyafar Da Kwamitin Kasa Mai Lura Da Kasuwancin Amurka Da Sin Ya Shirya
  • Matsayin Sin Na Bude Kofar Tattalin Arzikinta Ga Duniya Ba Zai Canza Ba
  • Zamfara Ta Zama Jiha Ta Farko Da Ta Ƙaddamar da Tsarin Ilimin Fasahar Zamani
  • Tinubu Zai Zaɓi Mataimakinsa Bayan Taron Jam’iyya – Fadar Shugaban Ƙasa 
  • Muna shawartar Trump kada ya shiga yaƙin Iran da Isra’ila — Birtaniya
  • Xi Ya Tattauna Da Shugaban Rasha Ta Wayar Tarho