Aminiya:
2025-07-23@22:41:51 GMT

Gobara ta tashi a otal ɗin da ke ɗauke da Alhazan Najeriya 480 a Makkah

Published: 7th, June 2025 GMT

Gobara ta tashi a otal ɗin Imaratus Sanan da ke birnin Makkah a ƙasar Saudiyya, inda sama da alhazan Najeriya 48 suka sauka yayin aikin Hajjin shekarar 2025.

Otal ɗin yana unguwar Sharamansur a birnin Makkah.

Magidanci ya shiga hannu kan kashe matarsa mai juna biyu da duka

Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), ta tabbatar da cewa dukkanin alhazan sun tsira kuma babu wanda ya ji rauni.

A cewar NAHCON, hukumomin gaggawa na Saudiyya da ma’aikatan otal ɗin sun gaggauta kashe wutar kafin ta bazu.

Shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Usman, ya ziyarci otal ɗin tare da wasu jami’an hukumar domin duba halin da ake ciki.

Ya bayar da umarnin a kwashe alhazan zuwa wani sabon otal cikin gaggawa, sannan ya yi alƙawarin tallafa musu.

“Muna gode wa Allah da babu rai da ya salwanta,” in ji shi.

Ya ce NAHCON za ta yi aiki da sauran masu ruwa da tsaki domin tabbatar da cewa mahajjatan sun samu kulawa ta musamman.

“An riga an duba sabon wajen da za a sauke su, kuma an fara shirye-shiryen sauya wajen. NAHCON ta kuma yaba da saurin kai taimako da hukumomin Saudiyya da ma’aikatan otal ɗin suka yi.”

Wasu daga cikin mahajjatan sun shaida wa Aminiya cewa gobarar ta tashi ne da misalin ƙarfe 12 na ranar Asabar, a lokacin da mafi yawan su ke Mina wajen gudanar da jifar shaiɗan, ɗaya daga cikin manyan ayyukan aikin Hajji.

NAHCON ta ce za ta ci gaba da sanar da al’umma yayin da ake ciki da zarar ta samu sabbin bayanai.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Gobara Najeriya Saudiyya

এছাড়াও পড়ুন:

 Netanyahu: Ba Za Mu Daina Yakin Gaza Ba

Fira ministan HKI wanda kotun duniya ta manyan laifuka take nem ruwa a jallo ya bayyana cewa; Babu yadda za su tsayar da yakin Gaza, matukar kungiyar Hamas ba ta mika wuya baki day aba.

Benjemine Netanyahu ya kuma ce; A lokacin da Hamas za ta mika makamanta ne, shi ne za mu yi tunanin ko za mu bude mata hanyar ficewa daga Gaza, da kuma dakatar da yaki.

A gefe daya tashar talabijin din CNN ta ambato wata majiya ta gwamnatin Amurka tana cewa; Amurka ta gargadi kungiyar Hamas akan cewa, hakurinta ya kusa karewa akan batun tsagaita wuta, tare da neman kungiyar ta gwagwarmaya ta bayar da jawabi a cikin gaggawa kafin makwanni biyu masu zuwa.

Tashar talabijin din CNN din ta kuma bayyana cewa;  Amurkan ta bai wa Hamas lamunin cewa Isra’ila ba za ta shiga cikin tattaunawar kawo karshen yaki ba a tsawon lokacin dakatar da yaki da zai dauki kwanaki 60.

Sai dai kuma majiyar ta fada wa tashar talabijin din CNN cewa, Amurkan za ya janye wannan lamunin idan har kungiyar ta Hamas ba bayar da jawabi a cikin sauri ba.

 Sai dai kuma masu bin diddigin abubuwan da suke faruwa sun bayyana cewa; HKI ce ummul-haba’isin tsaikon da ake samu a tsagaita wutar yakin ba kungiyar gwgawarmaya ta Hamas ba.

A nata gefen kungiyar Hamas ta ce, a mataki na baidaya kungiyar tana son ganin an tsagaita wuta, duk da cewa jagorancin kungiyar na Gaza ne zai yanke hukunci na karshe.Khalilul Hayya wanda ya bayyana hakan ya kara da cewa; Jagororin Hamas na cikin gida ne ke da alhakin aiwatar da duk wani mataki na tsagaita wuta, don haka su ne za su bayyana mataki na karshe.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  •  Iraki Ta Yi Watsi Da Bukatar Amurka Akan Dakarun Sa Kai Na” Hashdus-sha’abi”
  • Tinubu na amfani da ƙarfin mulki wajen tsoratar da ’yan adawa — Sule Lamido
  • DAGA LARABA: Abubuwan da ya kamata yara su yi yayin hutun makaranta
  • Majalisar Dattawa ta sahale wa Tinubu karɓo rancen $21bn a ƙetare
  •  Netanyahu: Ba Za Mu Daina Yakin Gaza Ba
  • NAJERIYA A YAU: Yadda tsadar taki ke hana noman masara da shinkafa
  • An kaddamar Da Wani Shiri Na Ba ‘Yan Mata 200,000 Tallafin Audugar Mata A Kano
  • MDD Ta Gargaɗi Isra’ila Kan Tilasta Wa Al’ummar Deir al-Balah Na Gaza Tashi
  • Hukumar Kashe Gobara Ta Jihar Kwara Ta Taimaka Wajen Hana Lalacewar Wani Bene A Ilorin
  • Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Ce; Iran Ba Zata Bar Tace Sinadarin Uranium Ba