Rundunar ‘Yan Sanda A Kano Ta Haramta Bukukuwan Hawan Sallah A Kano
Published: 4th, June 2025 GMT
Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta jaddada haramcin gudanar da hawan Durbar na shagulgulan Babbar Sallah.
Wannan sanarwar na cikin wata takarda da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya sanya wa hannu, kuma aka rabawa manema labarai a Kano.
Sanarwar ta bayyana cewa an sanya wannan doka ne bisa rahotannin sirri da ke nuna cewa wasu bata-gari da masu daukar nauyinsu na shirin amfani da hawan Durbar domin tayar da hankali da barazana ga tsaro da doka a jihar.
Rundunar ta taba sanya irin wannan haramci a lokacin bukukuwan Sallah ƙarama da suka gabata, kuma an yanke shawarar ci gaba da dokar har zuwa Sallah Babba.
Sanarwar ta ƙara da cewa rundunar ta ɗauki matakan kariya tun kafin lokaci domin tabbatar da zaman lafiya da tsaron rayuka da dukiyoyi a fadin jihar.
“An shawarci masu ibada da su kasance masu bin doka da oda tare da gudanar da bukukuwan cikin lumana. Rundunar ta fitar da wasu ƙa’idojin tsaro da suka haɗa da: hawan doki wato (Kilisa),da tseren motoci ko tuki cikin ganganci da hatsari, da mallakar bindiga ko wani makami ba bisa ka’ida ba ko nuna su a fili, da kuma ɗaukar kaya marasa amfani ko masu haɗari da ka iya jawo shakku ko firgici.
Rundunar ta shawarci iyaye da su ja kunnen ‘ya’yansu, su guji shiga cikin ayyukan bata-gari ko baragurbi.
Rundunar ta kuna sha alwashin aiwatar da doka ba tare da rangwame ba.
Abdullahi Jalaluddeen
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Durbar Rundunar ta
এছাড়াও পড়ুন:
Lakurawa Sun Sanya Dokar Hana Sayar Da Shanu A Kebbi
Yanzu haka fargaba ta karaɗe yankin, yayin da jama’a ke roƙon gwamnati da hukumomin tsaro su tashi tsaye domin kawo ƙarshen wannan matsala da ta dabaibaye rayuwarsu da amfanin gonarsu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp