Aminiya:
2025-07-23@22:57:45 GMT

Gwamnan Akwa Ibom ya sauya sheƙa daga PDP zuwa APC

Published: 6th, June 2025 GMT

Gwamna Umo Eno na Jihar Akwa Ibom, ya fice daga jam’iyyar PDP tare da sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC.

Ya bayyana hakan ne a hukumance a ranar Juma’a a gidan gwamnatin jihar da ke Uyo, babban birnin jihar.

Tinubu ba zai canza Kashim a matsayin mataimakinsa ba a 2027 – APC Mun gurfanar da mutum 29 a kotu kan zargin kashe DPO a Kano – ’Yan sanda

Wannan mataki ya biyo bayan wasu kwanaki da ya shafe yana nuna sha’awarsa na sauya sheƙa.

A wani taron jama’a da aka gudanar a Ikot Abasi, ya ce: “Lokaci ya yi da za mu motsa” domin a haɗa kai da Gwamnatin Tarayya da jam’iyyar APC ke jagoranta.

Gwamnan ya ce ya ɗauki wannan mataki ne bayan shafe watanni uku yana tattaunawa da manyan mutane da masu ruwa da tsaki a jihar.

Ya nuna godiyarsa ga PDP saboda goyon bayan da suka ba shi, amma yanzu lokaci ya yi da zai ci gaba da tafiya gaba.

Ya bayyana cewa yana matuƙar ƙaunar Shugaba Bola Tinubu, kuma yana ganin Jihar Akwa Ibom za ta fi amfana idan tana aiki kafaɗa da kafaɗa da Gwamnatin Tarayya.

Gwamna Eno, ya sha alwashin cewa zai ci gaba da yi wa mutanen jihar aiki tuƙuru, ko daga wacce jam’iyya yake.

“Na kammala ganawa da jama’a a matsayin wanda kuka zaɓa, kuma na yanke shawarar komawa jam’iyyar APC,” in ji shi.

Gwamnonin jam’iyyar APC ne suka tarbe shi, ciki har da Gwamnan Jihar Imo kuma shugaban ƙungiyar gwamnonin APC, Hope Uzodimma; Bassey Otu na Jihar Kuros Riba; Babajide Sanwo-Olu na Jihar Legas; da Dapo Abiodun na Jihar Ogun.

Sauran da suka halarta sun haɗa da Gwamna Sheriff Oborevwori na Delta, Monday Okpebholo na Edo, da Francis Nwifuru na Jihar Ebonyi.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: gwamna Sauya Sheƙa Siyasa jam iyyar APC

এছাড়াও পড়ুন:

Ƙwallon Mata: Nijeriya Ta Kai Wasan Ƙarshe Bayan Doke Afrika Ta Kudu

Yar wasan gaba ta Nijeriya, Chinwendu Alozie, ce ta tabbatar da nasara da kwallon da ta jefa kafin tashi daga wasan. Wannan nasara ta ba wa tawagar ta Justin Madugu damar kaiwa wasan ƙarshe na gasar.

 

Yanzu haka, Super Falcons za su kara da ƙasar da za ta yi nasara tsakanin Moroko, wacce ke masaukin baki, da Ghana, a wasan da za a buga daga baya a

yau Talata.

 

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamna Namadi Ya Amince Da Nadin Sabbin Sakatarori Guda Takwas
  • UNICEF Ya Bukaci Jihar Kano Ta Bai Wa Yara Muhimmanci A Kasafin Kudi
  • Gwamna Namadi Ya Sanya Hannu Kan Dokar Kafa Hukumar Hisba Ta Jihar Jigawa
  • Majalisar Dokokin Jihar Jigawa Ta Kai Ziyarar Gani Da Ido Kirikasamma
  • Ƙwallon Mata: Nijeriya Ta Kai Wasan Ƙarshe Bayan Doke Afrika Ta Kudu
  • Mutum 16 sun mutu a haɗarin jirgin sama a Bangladesh
  • PSC Ta Amince Da Ɗaga Darajar Jami’an ‘Yan Sanda 12 Daga Matakin CP Zuwa AIG, Da Sauransu
  • Gwamna Namadi Ya Jinjinawa Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Bisa Ayyukan Raya Kasa
  • Gwamna Radda Da Makarrabansa Na Samun Kulawa A Asibiti Bayan Hatsarin Mota A Hanyar Daura
  • Mataimakiyar Shugaban Majalisar Dinkin Duniya Ta Jinjinawa Gwamnan Kano Bisa Ayyukan Cigaban Jihar