Gwamnatin Tarayya Na Yunkurin Rage Dala Biliyan 1.5 Da Ake Kashewa Wajen Shigo Da Madara
Published: 6th, June 2025 GMT
Domin shawo kan wannan matsalar, ministan ya zayyana kokarin da ake yi a karkashin dabarun bunkasa kiwon dabbobi na kasa, wanda ya mayar da hankali kan ginshikai guda 10 da suka hada da bunkasa kimar dabbobi, inganta kiwo, kiwon lafiyar dabbobi, samar da kudi, sauya salon kiwo da karfafawa matasa da mata gwiwa kan dogaro da kai.
Maiha ya yi tunin cewa zuwa yanzu ma’aikatar ta samu cimma wasu nasarori da suka hada da yin rajistar nau’in kiwo guda takwas, “na farko a cikin shekaru 48” da kuma samar da wani shiri na kasa kan albarkatun halittun dabbobi tare da hadin gwiwar FAO.
“Dabbobinmu na cikin gida suna samar da lita 1-2 na madara a kullun, idan aka kwatanta da na waje a karkashin gudanarwa da kuma tsarin kiwon lafiya domin shawo kan wanan gibin, dole ne mu tashi tsaye mu magance wannan matsalar,” ya shaida.
Ministan ya kuma bayyana yadda ake zuba jari a fannin kiwon lafiyar dabbobi, gami da fadada samar da alluran rigakafin a Cibiyar Nazarin Dabbobi ta Kasa (NBRI) daga allurai miliyan 120 zuwa miliyan 850 a duk shekara. An kuma kaddamar da wani wurin ajiyar alluran rigakafi mai amfani da hasken rana mai karfin awo miliyan 40 a Sheda da ke Abuja da dai sauran nasarori.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Ban Tsani Buhari Ba, Ina Sukar Sa Ne Kawai Kan Matsalar Tsaro – Ortom
Ya ce ya dinga ƙorafi ne domin gwamnatin Buhari ba ta ɗauki matakin da ya dace ba game da kashe-kashen da ake yi a Benuwe.
“Ba zan iya zama na yi shiru ina ci gaba da binne mutane ba. Dole ne na faɗi gaskiya,” in ji shi.
“Amma ban tsaya a magana kawai ba, gwamnatina ta kawo hanyoyin magance matsalar da muka ga za su taimaka.”
Ortom ya ƙara da cewa da gwamnatin Buhari ta karɓi shawararsa kuma ta yi aiki da ita, da matsalar tsaro a Benuwe ta ƙare.
Ya ce ya sha kokawa a lokacin, kuma shirye-shiryen da gwamnati ta kawo kamar Ruga ba su da amfani.
Ya ce ba wai rikici ne tsakanin makiyaya da manoma kawai ba, wasu daga cikin makiyaya suna kai wa ƙauyuka hari, suna kashe mutane, lalata gonaki, yi wa mata fyaɗe da aikata wasu laifuka.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp