Gwamnatin Tarayya Da Hadin Gwiwar IFAD Za Su Yi Wa Manoma Rijista Domin Tantance Su
Published: 7th, June 2025 GMT
A jawabinsa a wajen taron kaddamar da tsarin tattaunawa kan shirin yin amfani da fashar zamani na samar da yin rjitsar ta manoman kasar (NDFR), wadda aka gudanar a babban birnin tarayyar Abuja, Babban Sakatare a Ma’aikatar Aikin Noma da Samar da Wadataccen Abinci, Dakta Marcus Ogunbiyi, ya bayyana cewa; sabon tsarin zai taimaka matuka, wajen rage duk wani matsayi da manoman kasar suke ciki, musamman manoman da ba su mallaki wata gona ba.
“Za mu tabbatar mun yi rijistar sunayen manoman kasar da kuma gonakinsu, sannan kuma ba wai kawai yin rijistar ba, har da irin nau’in amfanin da suke nomawa da kuma nau’in irin kasar da ke gonakin nasu,” in ji Marcus.
Dakta Marcus ya kara da cewa, babu wata gona da ba ta da manomi, amma akwai manoma da dama da ba su mallaki gonaki ba.
“Idan mun yi wa manoman rijistar, za mu raba musu Kati kai tsaye da kuma wani Katin na manhajar zamani, domin a rika yin aiki da manoman kai tsaye ta yadda za a iya saurin gano kowane manomi a cikin sauki,” a cewar Marcus.
Ya ci gaba da cewa, hakan zai bayar da damar samun adana bayanansu kai tsaye da ya kunshi na sheda, musamman domin su rika samun taimakon daga wurin gwamnat da ya hada da samun rancen kudin yin noma.
Markus ya bayyana cewa, domin samun cin nasarar wannan aiki, Ma’aikatar Aikin Noma da Samar da Wadataccen Abincii, ta dauki wasu matakai domin samun bayanan manoman kasar tare da adana bayannan nasu.
Ya ci gaba da cewa, guda daga cikin dabarun aikin shi ne, na yin hadaka da hukumar da ke rajistar katin dan kasa (NIMC), musamman domin wanzar da wannan aiki na yi wa manoman rijista da kuma tattara bayanansu, domin tabbatar da ganin kowane manomi, an sanya shi a cikin tsarin.
Ita kuwa a nata jawabin, Daraktar IFAD a kasar nan, Madam Dede Ahoefa Ekoue ta bayyana cewa, sashen samar da abinci na Majalisar Dinkin Duniya, na alfaharin kasancewa cikin wannan sabon shirin.
“Gundunmawarmu ita ce, kokarin samun damar jawo sauran abokan hadaka na gwamnati da kuma masu kamfanoni masu zaman kansu, ta yadda za su zuba kudade tare, domin taimaka wa kokarin gwamnatin kasar, na yin rijistar manoman kasar,“ in ji Dede.
Madam Dede ta kara da cewa, koda-yake a baya, an yi irin wannan kokarin, amma ya kamata a ci gaba da wannan shirin, duba da muhimmancin da yake da shi.
“A yanzu, gwamnatin kasar ta samar mana da wata alkibla da kuma umartar daukacin masu ruwa da tsaki a fannin aikin noman kasar, domin a yi aiki tare,“ in ji ta.
Ta sanar da cewa, irin wannan aikin ne muke yi da sauran abokan hadaka kamar irin su; Bankin Raya Nahiyar Afrika, Hukumar Bunkasa Samar da Wadataccen Abinci, Bankin Duniya, Tarayyar Turai, Bankin Bunkasa Musulunci da kuma Gwamnatin Burtaniya.
Kazalika, ta sanar da cewa; babbin abin shi ne, ta hanyar yin aiki da kungiyoyin manoman kasar nan, domin su ne za su amfana da aikin.
Madam Dede ta ci gaba da cewa, hukumar ta IFAD, na matukar farin cikin jawo abokan hadaka da sauran sassan ma’aikatun gwamnati da sauran hukomomin gwamnatin kasar, domin tafiya tare cikin aikin.
Ta yi nuni da cewa, wannan aiki zai kasance tamkar samar da wani sauyi ne na ci gaba ga fanin aikin noman kasar.
Shi ma a nasa jawabin, Darakan kungiyar kasa da kasa ta Heifer da ke aiki a kasar nan, Dakta Lekan Tobe ya bayyana babban muhimancin da ke tattare da aikin, musamman ta hanyar yin hadaka.
Ya sanar da cewa, wannan aikin na daga cikin wasu shawarwarin da aka bayar a baya, wanda gwamnatin kasar nan ta yi hadaka da nufin yin amfani da fasahar zamani, domin a kara samar da wadataccen abinci a kasar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: gwamnatin kasar manoman kasar wannan aiki
এছাড়াও পড়ুন:
Mataimakin Gwamnan Sakkwato bai karɓi shanun tallafin layya ba — Hukumar Zakka
An samu cece-ku-ce a Jihar Sakkwato bayan da wata jita-jita ta yaɗu cewa Mataimakin Gwamnan jihar, ya karɓi shanu 400 da aka tanadar domin tallafa wa marasa galihu domin yin layya a lokacin Sallah Babba.
An ce shanun wata ƙungiya ce daga ƙasar Turkiyya ta bayar da su, ta hannun Hukumar Zakka da Waƙafi ta jihar, domin tallafa wa waɗanda ba su da halin yin layya.
Iran ta kai sabbin hare-hare birnin Tel Aviv da Haifa An tallafa wa mata 250 da abinci da kayan sana’a a KadunaSai dai an zargi Mataimakin Gwamnan da karɓe su don amfanin kansa.
Wannan batu ya jawo jama’a a jihar suk dinga bayyana ra’ayoyinsu, inda wasu ke zargin an fifita jami’an gwamnati fiye da talakawa da aka yi nufin bai qa shanun.
Wasu sun zargi cewa malamai, limamai, ‘yan siyasa da ƙungiyoyin addini ne suka fi cin moriyar shanun.
Sai dai a wata hira da wakilinmu ya yi, da mataimakin gwamnan ya musanta karɓar shanun.
Ya ce: “Hukumar Zakka ce ke raba wa ’yan gudun hijira da ke fama da matsalar tsaro kamar a Sabon Birni da Isa.
“A shekarar da ta gabata sun karɓi shanu 20 kowane. Haka nan Illela da Gwadabawa sun samu goma-goma.”
Ya ƙara da cewa ba shi da hannu kai-tsaye, domin an tuntuɓar shi ne kawai a matsayin wanda zai jagoranci rarraba shanun ga jama’ar yankin da ke ƙarƙashinsa.
Shugaban Hukumar Zakka da Waƙafi ta jihar, Malam Muhammad Lawal Maidoki, ya ƙara bayyana cewa:
“Mataimakin gwamna bai karɓi shanun ba. An kafa kwamiti ƙarƙashinsa domin kula da rabon a yankin Gabas da ke fama da matsalar tsaro. Shanun sun ƙare kafin a gama rabawa. An ware 150, amma 106 ne aka samu.”
Ya kuma bayyana cewa sun yi niyyar yanka shanu 4,500 amma saboda wasu matsaloli, ciki har da rashin samun dabbobi da suka cika sharuɗan layya, sun yanka 3,000 kacal.
Malam Maidoki ya nemi afuwa ga duk wanda bai samu shanun ba, da waɗanda aka saba bai wa amma aka kasa ba su, da waɗanda suke tsammanin samun amma ba su samu ba.
Ya ƙara da cewa sun rubuta sunayen waɗanda ba su samu ba domin tunawa da su a shekara mai zuwa.
“Muna fata Allah Ya kawo mu wata shekara cikin lafiya da dama don ci gaba da tallafa wa marasa ƙarfi a irin wannan lokaci,” in ji shi.
A cewar hukumar, shirin ya laƙume sama da Naira biliyan ɗaya, kuma an raba naman layya ga dubban mutane da ba su samu damar yin yanka ba.