Shugaban Kasar Rasha Vladimir Putin Zia Kawo Ziyara Tehran Nan Kusa
Published: 5th, June 2025 GMT
Jakadan kasar Iran a Mosco ya bayyana cewa shugaban kasar Rasha Vladimir Putin zai kawo ziyarar aiki Tehran nan ba da dadewa ba.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran.
Labarin ya kara da cewa kasashen biyu sun kulla yarjeniyoyi masu yawa a tsakanin daga ciki har da masu dogon zango.
Kazem Jalali ya bayyana a yau Alhamis kan cewa kasar Rashe ce kasa tilo wacce ta zuwa jarin dalar Amurka biliyon $8 a bangaren gas da man fetur.
Banda haka zata kashe kudade don kammala layin dogo wacce ake kira hanyar Arewa zuwa Kudu. Banda haka Rasha zata fara tura danyen man fetur daga Rasha zuwa Iran don sayar da shi. Sannan a halin yanzu bankunan kasashen biyu a hadi da na’urori wanda zai bawa mutanen rasha kashe kudadensu a Iran tare da katin Mir a yayinda Iraniyawa zasu kashe kudadensu a Rasha da Katin banki na Shetab.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Namadi Sambo Ya Karyata Sauya Sheƙa Zuwa APC
Wasu na ganin jita-jitar ta samo asali ne bayan wani abokin aikinsa na baya, Sani Sidi, ya koma jam’iyyar APC tare da magoya bayansa a Kaduna.
Amma Sambo ya ce hakan bai shafe shi ba.
Hakazalika, an shirya Sambo zai halarci bikin ƙaddamar da asibiti mai gadaje 300 da ke Kaduna a ranar Alhamis, 19 ga watan Yuni, 2025.
Ya halarci bikin kuma hakan ba yana nufin ya goyi bayan wata jam’iyya ba ne.
Ƙungiyarsa ta nanata cewa Sambo yana nan daram a cikin jam’iyyar PDP, kuma labarin sauya sheƙar nasa ƙarya ce da aka ƙirƙira domin tayar da hankali da ƙoƙarin cimma wasu muradu na siyasa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp