Kasar Sin Ta Harba Sabon Rukunin Taurarin Dan Adam Mai Samar Da Sadarwar Intanet
Published: 6th, June 2025 GMT
Kasar Sin ta yi nasarar harba sabon rukunin taurarin dan adam mai da’ira a kusa da doron kasa, daga cibiyar harba tauraron dan Adam ta Taiyuan dake lardin Shanxi na arewacin kasar Sin.
An harba rukunin wanda shi ne irinsa na 4 da ya kunshi taurari masu samar da sadarwar intanet da misalin karfe 4:45 na sanyin safiyar yau Juma’a agogon Beijing, ta hanyar amfani da rokar Long March-6 da aka sakewa fasali.
Wannan shi ne karo na 580 da aka yi amfani da dangin rokar Long March wajen gudanar da irin wannan aiki. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Ya Ce Ba’a Rufe Kofar Diblomasiyya Ba, Matukar HKI Ta Dakatar Da Kaiwa Kasar HKI
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya bayyaana cewa kasarsa bata rufe kofar diblomasiyya dangane da shirinta na makamashin Nukliya ba, matukar HKI zata dakatar da hare-haren da take kaiwa kasar.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka a yau Lahadi a taron yan jaridun da ya kira a birnin Tehran. Ya kuma kara da cewa Iran tana son ta ci gaba da shirinta na makamashin Nukliya ta zaman lafiya ta hanyar diblomasiyya idan an bata damar yin haka.
Ministan ya ce ikidar JMI ne warware dukkan matsaloli da farko ta hanyar Diblomasiyya, da kuma tattaunawa amma ba zamu taba amincewa wani ya hanamu hakkimu na mallakar makamashi nukliya ta zaman lafiya ba. Kuma mun bayyana cewa a shirye muke a gudanar da bincike a ayyukammu. Sojojin Iran sun cilla wasu sabbin hare-hare a kan HKI a yau Lahadi da rana.
Yakin da HKI ta fara a safiyar jumma’an da ta gabata, mai kuma samun goyon bayan Amurka, don tilsatawa Iran amincewa da sharuddanta na shirin Iran na makamashin nukliya ne.