Daya daga cikin manyan-manyan  jami’an gwamnatin tsohon shugaban kasar Amurka Joe Biden, ya bayyana cewa: “Babu tantama gwamnatin HK Isra’ila ta tafka laifukan yaki a kan Falasdinawa a zirin Gaza da ta killace.

Matthew Miller wanda ya yi aiki a matsayin kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka tun daga 2023 har zuwa karshen gwamnatin Joe Biden, ya fada wa tashar talabijin ta Sky News kan cewa; Isra’ilan ta tafka laifukan yaki.

Da aka yi masa tambaya a kan yakin Gaza a fadar White House, Miller ya ce; An yi ta samun tsabani dangane da yakin, sabani manya-manya wani lokacin kuma kananan sabani, kan yadda za a kare dangantakar  Amurka da HK Isra’ila duk tare da abinda take aikatawa.”. Amma Miller ya tabbatar da cewa HK Isra’ilan ta tafka laifukan yaki wanda babu shakka a cikin hakan..

Da aka tambaye shi a kan, ko me ya sa a lokacin suke Mulki bai bayyana cewa HK Isra’ila tana aikata laufkan yaki ba? Sai ya amsa da cewa:

“Idan mutum yana cikin gwamnati, ba ya bayyana ra’ayinsa na kashin kansa, yana bayyana ra’ayin gwamnatin Amurka ne.”

Haka nan kuma ya ce; Aikin mai magana  da yawun gwamnati, ko dai ka zama mai Magana da yawun shugaban kasa, ko gwmanatin kasar, amma idan baka cikin gwamnati, to za ka iya fadar ra’ayinka.”

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: HK Isra ila

এছাড়াও পড়ুন:

 Netanyahu: Ba Za Mu Daina Yakin Gaza Ba

Fira ministan HKI wanda kotun duniya ta manyan laifuka take nem ruwa a jallo ya bayyana cewa; Babu yadda za su tsayar da yakin Gaza, matukar kungiyar Hamas ba ta mika wuya baki day aba.

Benjemine Netanyahu ya kuma ce; A lokacin da Hamas za ta mika makamanta ne, shi ne za mu yi tunanin ko za mu bude mata hanyar ficewa daga Gaza, da kuma dakatar da yaki.

A gefe daya tashar talabijin din CNN ta ambato wata majiya ta gwamnatin Amurka tana cewa; Amurka ta gargadi kungiyar Hamas akan cewa, hakurinta ya kusa karewa akan batun tsagaita wuta, tare da neman kungiyar ta gwagwarmaya ta bayar da jawabi a cikin gaggawa kafin makwanni biyu masu zuwa.

Tashar talabijin din CNN din ta kuma bayyana cewa;  Amurkan ta bai wa Hamas lamunin cewa Isra’ila ba za ta shiga cikin tattaunawar kawo karshen yaki ba a tsawon lokacin dakatar da yaki da zai dauki kwanaki 60.

Sai dai kuma majiyar ta fada wa tashar talabijin din CNN cewa, Amurkan za ya janye wannan lamunin idan har kungiyar ta Hamas ba bayar da jawabi a cikin sauri ba.

 Sai dai kuma masu bin diddigin abubuwan da suke faruwa sun bayyana cewa; HKI ce ummul-haba’isin tsaikon da ake samu a tsagaita wutar yakin ba kungiyar gwgawarmaya ta Hamas ba.

A nata gefen kungiyar Hamas ta ce, a mataki na baidaya kungiyar tana son ganin an tsagaita wuta, duk da cewa jagorancin kungiyar na Gaza ne zai yanke hukunci na karshe.Khalilul Hayya wanda ya bayyana hakan ya kara da cewa; Jagororin Hamas na cikin gida ne ke da alhakin aiwatar da duk wani mataki na tsagaita wuta, don haka su ne za su bayyana mataki na karshe.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Shugaban Amurka Trump Ya Bukaci Gurfanar Da Tsohon Shugaban Amurka Barack Obama A gaban Kuliya
  • Kotu Ta Umarci Gwamnatin Bauchi Ta Biya Tsohon Akanta-Janar Naira Miliyan 100
  •  Netanyahu: Ba Za Mu Daina Yakin Gaza Ba
  • Jami’an tsaro sun dakile yunkurin Sanata Natasha na shiga harabar Majalisa
  • Rayuwata Na Cikin Hatsari, A Dawo Min Da Jami’an Tsarona – Natasha 
  • Ban Tsani Buhari Ba, Ina Sukar Sa Ne Kawai Kan Matsalar Tsaro – Ortom
  • Tsohon Sakataren Gwamnatin Bauchi, Ibrahim Kashim, Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP
  • Gwamnatin Zamfara Ta Kira Babban Taron Tsaro Tare Da Bayyana Sabbin Dabaru Na Yakar ‘Yan Bindiga.
  • Jami’in Shari’ar Kasa Da Kasa Ya Bayyana Cewa: Harin Da Aka kai Kan Iran Babban Laifi Ne
  • Jaridar Washington Post Ta Ce; Yeman Ta Gurguta Ayyukan Tashoshin Jiragen Ruwan Isra’ila