2025-07-23@05:02:04 GMT
إجمالي نتائج البحث: 4087

«a Majalisar Dinkin Duniya»:

    A cewar Ringim, idan ana so a sami cigaban da ya shafi kowa da kowa a Arewacin Nijeriya da ma ƙasa baki ɗaya, to ana buƙatar siyasa irin ta Kwankwaso wadda ke mayar da hankali kan talakawa da gaskiya a mulki. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya sanya hannu kan kudurin dokar da ta kafa Hukumar Hisba a matsayin hukuma ta dindindin a ƙarƙashin gwamnatin jihar. Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da Sakataren Yada Labarai na gwamnan Hamisu Muhammad Gumel ya fitar ga manema labarai a Jigawa. Sanarwar ta bayyana cewa bikin sanya hannun ya gudana ne a zauren majalisar zartarwa na fadar gwamnati dake Dutse, inda manyan jami’an gwamnati suka halarta, ciki har da Mataimakin Gwamna, Injiniya Aminu Usman, da mambobin Majalisar Dokokin Jihar Jigawa karkashin jagorancin Mataimakin Kakakin Majalisar, Hon. Sani Isyaku. Ta ce Gwamna Namadi ya bayyana cewa wannan rana na ɗaya daga cikin manyan nasarorin da aka cimma, bayan kai-komo na sama...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun, ya ce taron koli na Sin da kungiyar Tarayyar Turai ta EU karo na 25 dake tafe, zai taimaka wajen bunkasa tattaunawa bisa matsayin koli, da zurfafa shawarwari, da hadin gwiwa tsakanin sassan biyu, lamarin da zai biya bukatu da moriyarsu, da ma na sauran sassan duniya baki daya. Guo Jiakun, ya jaddada muhimmancin taron, kasancewar ya zo a gabar da harkokin cudanyar kasa da kasa ke fuskantar yanayi na tangal-tangal, da ma karuwar daukar matakan kashin kai daga bangare guda, da kariyar cinikayya. Ya ce, hadin gwiwar sassan biyu, ya haifar da manyan nasarori a baya, wanda hakan ya bunkasa ci gaba da daukakarsu, tare da samar da tarin alfanu ga...
    Babbar Kotun Tarayya da ke Bauchi ta yanke hukunci a kan gwamnatin jihar Bauchi da ta biya tsohon Akanta-Janar na jihar, Dakta Sa’idu Abubakar, Naira miliyan 100 a matsayin diyyar take masa haƙƙi da kuma tsare shi ba bisa ƙa’ida ba. Kotun ta kuma umarci gwamnati ta wallafa ban haƙuri a manyan jaridu guda biyu cikin kwanaki 14. Mai Shari’a Aminu Garba ya yanke wannan hukunci ne a ƙarar da Dakta Abubakar ya shigar, yana zargin gwamnati da jami’anta da take masa haƙƙi, da kama shi ba tare da bin ƙa’ida ba, da musgunawa. Ya bayyana cewa hakan ya saɓawa tanade-tanaden kundin tsarin mulki da kuma yarjejeniyar kare haƙƙin bil’adama ta Afrika. Tsohon Sakataren Gwamnatin Bauchi, Ibrahim Kashim, Ya Fice...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kungiyar ta malaman musulumi ta fitar da fatawa da a ciki ta bukaci gwamnatoci da al’ummar musulmi da su yunkura cikin gaggawa domin kawo karshen killace yankin Gaza da aka yi, da kuma wajabcin kai musu abinci da magunguna. Kungiyar malaman musulmin ta kuma bayyana abinda HKI take yi na killace mutanen Gaza fiye da miliyan biyu da haka su abinci da magani,musamman mata, yara da manya,wani babban laifi ne da ba shi da tamka a cikin tarihi, tana mai yin kira ga al’ummu da gwamnatoci da su motsa saboda su taimaki raunana. Kwamitin fatawa da yake a karkashin wannan kungiyar ta malaman musulmi, ya dogara da ayoyin alkrur’ani da hadisan ma’aiki ( s.a.w) da manufofi na shari’a da ka’idoji...
    Shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan ya bayyana cewa; Batun kare hakkin bil’adama da ake yi a duniya ba komai ba ne sai karya. Shugaba Fizishkiyan ya yi ishara da yadda masu ikirarin kare hakkin bil’adama suke sa kafafunsu suna take hakkin mutanen Gaza da cikin kasashen yammacin Asiya da kuma tafka manyan laifuka. A yau Talata ne dai shugaban kasar ta Iran ya gabatar da jawabi a wurin bikin girmama shahidan kallafaffen yaki na kwanaki 12, ya bayyana cewa: “A cikin wannan duniyar wacce take riya ci gaba da wayewa, a gaba idon duniya, ake yanke wa mutanen Gaza ruwan sha da abinci, a hana mata da kananan yara. Haka nan kuma ake tafka laifukan da su ka kunshi kisan...
    Asusun kula da ƙananan yana na Majalisar Ɗinkin Duniya UNICEF, ya ce ya wani sabon bincike da ya gudanar ya banƙado yadda cin zarafin ƙananan yara da kuma kulle su ba bisa ƙa’ida ba ke ci gaba da bazuwa a Nijeriya. A cikin rahoton da ya fitar ranar Litinin, UNICEF ya ce har yanzu akwai dubban ƙananan yara da gwamnati ta rufe su ba kuma tare da cikakken bayani ga iyalansu ba, wasu ma a yanzu babu cikakken bayani kan inda suke ko kuma halin da suke ciki. Zazzaɓin Lassa ya kashe mutum 151 a Nijeriya bana — NCDC Jami’an tsaro sun dakile yunkurin Sanata Natasha na shiga harabar Majalisa Asusun ya ce a Nijeriya rufe ƙananan yara tare da...
    Alkaluma da aka fitar a hukumance sun nuna cewa, kasar Sin ta samar da sabbin guraben aikin yi miliyan 6.95 a rabin farko na bana, inda ta cimma kaso 58 bisa dari na burinta na shekara. Kakakin ma’aikatar kula da ma’aikata da walwalar al’umma ta kasar Sin Cui Pengcheng ne ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai a yau Talata, inda ya ce a watan Yuni, yawan wadanda ba su da aiki a birane ya tsaya kan kaso 5 bisa dari, watau bai sauya ba daga yadda ya kasance shekara 1 da ya wuce. Kasar Sin na da burin adadin marasa aikin yi ya tsaya kan kaso 5.5 a bana, tare da burin samar da guraben aikin yi sama...
    Su kuwa mahalarta taron, sun yaba da kyautatuwar dangantakar kasashen biyu da rawar da SCO ke takawa. Sun kuma bayyana fatan Masar da Sin za su yi amfani da damarmakin ci gaba da SCO ta samar domin su hada hannu tare, su inganta tsarin jagorantar harkokin duniya da farfadowar kasashe masu tasowa. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Hukumar Hisbah ta ce ta kama tare da lalata barasa da ta kai kimanin naira miliyan 5.8 a karamar hukumar Kazaure ta Jihar Jigawa. Kwamandan Hisbah a jihar Malam Ibrahim Dahiru ne ya bayyana haka a wata hira da manema labarai a Dutse, babban birnin jihar. Jami’an tsaro sun dakile yunkurin Sanata Natasha na shiga harabar Majalisa Kamfanonin lantarki za su katse wuta kan bashin N5.2trn da suke bin gwamnati  Ya ce an gudanar da aikin ne karkashin jagorancin shugaban hukumar da ke Kazaure, Mansur Dabuwa, inda aka lalata katan 400 na barasa da darajar kudinsu ya kai naira miliyan 5.8. Ya bayyana cewa an kama barasa da aka kona a lokacin samamen da aka kai a sassa daban-daban a...
    Hukumar yaƙi da cututtuka masu yaɗuwa a Nijeriya (NCDC) ta ce adadin mutanen da zazzaɓin lassa ya kashe bana sun kai 151 a fadin kasar. Cikin wata sanarwa da NCDC ta wallafa a shafinta na X ranar Litinin, ta ce yawan kisan da cutar zazzaɓin lassa ke yi ya ƙaru daga kashi 17.3 cikin 100 da aka samu a bara. Jami’an tsaro sun dakile yunkurin Sanata Natasha na shiga harabar Majalisa Kamfanonin lantarki za su katse wuta kan bashin N5.2trn da suke bin gwamnati  Sanarwar ta ce an yi bitar alkaluman mamatan a bana ne bisa  la’akari adadin waɗanda suka kamu kuma ta yi ajalinsu a shekarar 2024. Hukumumar ta ce alkaluman mamatan ya kai kashi 18.9 cikin 100 na...
    Kamfanonin wutar lantarki sun yi barazanar katse wutar a fadin Najeriya saboda tarin bashin da ya haura Naira tiriliyan 5.2 da suke bin gwamnati. Taurin bashin, wanda ke barazana ga ci gaba da ayyukan kamfanoni, ya hada da Naira tiriliyan 1.2 na wutar da aka samar a watanni shidan farkon shekarar 2025, da Naira tiriliyan 2 daga 2024, da kuma bashin da aka gada tun daga 2015 wanda ya kai Naira tiriliyan 1.9. Shugabar ƙungiyar kamfanonin samar da wutar lantarki, Dakta Joy Ogaji, ta bayyana cewa kamfanonin sun daɗe suna nuna kishin ƙasa ta hanyar ci gaba da samar da wuta duk da rashin biyan su kuɗaɗensu, amma yanzu sun gaji. Ta bayyana cewa kudin da ake kashewa wajen samar...
    Kamfanonin wutar lantarki sun yi barazanar katse wutar a fadin Najeriya saboda tarin bashin da ya haura Naira tiriliyan 5.2 da suke bin gwamnati. Taurin bashin, wanda ke barazana ga ci gaba da ayyukan kamfanoni, ya hada da Naira tiriliyan 1.2 na wutar da aka samar a watanni shidan farkon shekarar 2025, da Naira tiriliyan 2 daga 2024, da kuma bashin da aka gada tun daga 2015 wanda ya kai Naira tiriliyan 1.9. Shugabar ƙungiyar kamfanonin samar da wutar lantarki, Dakta Joy Ogaji, ta bayyana cewa kamfanonin sun daɗe suna nuna kishin ƙasa ta hanyar ci gaba da samar da wuta duk da rashin biyan su kuɗaɗensu, amma yanzu sun gaji. Ta bayyana cewa kudin da ake kashewa wajen samar...
    Gwamnatin ƙasar Guinea ta rufe wasu sassan kamfanoni guda 1,724 sakamakon kama su da laifin ƙin bin dokokin hukuma, yayin da aka janye kayayyakin da suke sarrafawa daga kasuwa. Sanarwar na zuwa ne ƙarƙashin ma’aikatar kasuwanci a ƙasar, tana mai cewa an ɗauki matakin ne don kare lafiyar masu sayen kayayyakin da kuma tabbatar da kare muhalli, da kuma tilasta musu biyayya ga dokokin tafiyar da kamfanoni. Ma’aikatar kasuwanci ta ƙasar ta ce ba shakka wannan mataki zai zama tamkar hannunka mai sanda ga sauran kamfanoni da ke tafiyar da ayyukansu ba dai-dai ba. Da yake magana shugaban ƙungiyar masu sayen kayayyaki na ƙasar, Ousmane Keita, ya ce tun shekaru sama da uku suke ta wannan kiraye-kiraye, amma ba a...
    Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Ɓarkewa (ATBUTH) da ke Bauchi zai fara gwajin rigakafin cutar zazzabin Lassa. Wannan shiri na da nufin tabbatar da ingancin rigakafin, kuma wani ɓangare ne na babban shiri mai kasashe da yawa mai suna “Background Rates of Adverse Events for Vaccine Evaluation in Africa (BRAVE).” ATBUTH na daga cikin cibiyoyin kiwon lafiya huɗu a Najeriya da aka zaɓa don wannan aikin na tsawon shekaru uku (tare da yiwuwar ƙarin shekaru biyu don sa ido). Sauran su ne Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya (Owo) da Babban Asibitin Irrua da Asibitin Koyarwa na Jami’ar Benin. Wannan shiri, wanda Gidauniyar Ƙasa da Ƙasa kan Cututtukan Masu Saurin Yaɗuwa a Najeriya (IFAIN) ke gudanarwa tare da haɗin gwiwar...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Tashin farashin takin zamani yana hana manoma da dama noman wasu nau’ukan abinci. Manoma da dama sun ƙaurace wa noman masara da shinkafa da aka fi amfani da su a Najeriya sakamakon tsadar takin zamani, abin da masana ke ganin in ba a ɗauki mataki ba, hakan zai kawo ƙarancin abinci a ƙasar. NAJERIYA A YAU: Abin da ya sa muke yi wa PDP zagon ƙasa —Sule Lamiɗo DAGA LARABA: Makomar Siyasar Najeriya Bayan Rasuwar Shugaba Buhari Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan dalilan da suka sa farashin takin zamani ya yi tashin gwauron zabo a ƙasar. Domin sauke shirin, latsa nan
    Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, ya yi kira da a tsananta hukunci kan masu cin zarafin ’ya’ya mata, yana mai cewa babu wani musulmi nagari da zai yi wa matarsa dukan da har zai yi mata lahani. A yayin da yake tunatar da malamai da limamai kan muhimmiyar gudunmawar da za su bayar a wannan fage domin yi wa tufkar hanci, Sarkin ya bayyana damuwa kan yadda matsalolin fyade da kuma samun magidantan da ke dukan matansu suka zama ruwan dare a Jihar Kano. Yunwa na ƙara tsanani a Arewa maso Gabashin Nijeriya — ICRC Mutum 16 sun mutu a haɗarin jirgin sama a Bangladesh Sarki Sanusi na wannan furuci yayin da ya karbi bakuncin tawagar cibiyar bunkasa bincike (dRPC)...
    Kungiyar Agaji ta Red Cross (ICRC) ta bayyana cewa yunwa na ƙara tsananta a Arewa maso Gabashin Nijeriya, musamman a jihohin Borno, Adamawa da Yobe. A cewar rahoton, rikicin da ya dauki shekaru 16 ya durƙusar da kasuwanci da hanyoyin samun aiki, wanda hakan ya tilastawa mutane dogaro da ƙananan gonaki don rayuwa. Mutum 16 sun mutu a haɗarin jirgin sama a Bangladesh Jihohin da za a samu ruwan sama da iska mai ƙarfi a sassan Nijeriya — NiMet ICRC ta bayyana cewa fiye da mutum miliyan 3.7, wadanda galibi manoma ne na fuskantar barazanar matsanancin rashin abinci a yankin da aka shafe shekaru ana rikici. Churi Ibrahim, wani tsohon manomi dan shekara 70 da ke ciyar da iyalinsa goma,...
    Hukumar kula da yanayi ta Nijeriya (NiMet) ta sanar da cewa a ’yan kwanakin nan za a samu ruwan sama da iska mai ƙarfi a wasu jihohi da ke sassa daban-daban na ƙasar. Hakan na kunshe cikin hasashen yanayi na kwana uku, daga Litinin 21 zuwa Laraba 23 ga Yulin 2025 da hukumar ta fitar. Ƙalubalen da ke tattare da sauya sunan jami’a An nada ’yar Najeriya a Kwamitin Nukiliya na Majalisar Dinkin Duniya NiMet ta shawarci al’umma da su yi taka-tsantsan kan yiwuwar samun ambaliya da kuma ɓarna da iska mai ƙarfi ke iya haddasawa. A cewar sanarwar da hukumar ta wallafa a shafin sada zumunta na X, jihohin Arewa da na Kudu da kuma yankin tsakiya, duk za...
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    “Ba kawai girma tsarin samar da kayayyaki na kasar Sin yake da shi ba, har ma ya hade dukkanin fannoni, tare da amsawa da sauri kwarai da gaske.” “Daga kulla kwangila zuwa samun wurin gudanarwar ayyuka bai wuce watanni 3 ba, lamarin da ya ba mu mamaki sosai!” A ranar 20 ga wata, an rufe bikin baje kolin samar da kayayyaki na kasa da kasa karo na uku a birnin Beijing. A yayin bikin na wannan karo, kamfanonin kasashen ketare da suka hada da Honeywell, da Louis Dreyfus, da Corning, da kuma Wacker Chemie AG da dai sauransu, sun jinjinawa tsarin samar da kayayyaki na kasar Sin mai inganci. Sun ce, za su ci gaba da raya ayyukansu a kasar...
    An shawarci mata da su daina amfani da tsumma ko soson katifa, da takarda a lokacin al’adar su don inganta tsafta da rigakafin matsalolin lafiya.   Jami’ar tallafawa masu kula da tsaftar jinin haila a jihar Kano (MH-NoW) Amina Sabiu Musa ta yi wannan kiran ne a lokacin wani taron karawa juna sani na tsaftar jinin haila ga kwararrun ‘yan jarida da masu fada a ji a shafukan sada zumunta da aka gudanar a Kano.   A cewarta, shirin na MH-NoW ya shafi ‘yan mata da mata masu shekaru 10 zuwa 24 su 200,000 da nufin magance matsalar talaucin kudin sayen audugar mata a fadin Najeriya.   Ta bayyana cewa shirin wanda Population Services International (PSI) Nigeria ta aiwatar, zai...
    Jami’an ‘yan sanda da suka yi ritaya a jihar Kwara sun gudanar da zanga-zangar lumana don neman a cire su daga shirin bayar da gudunmawar fansho (CPS).   An ga jami’an ‘yan sandan da suka yi ritaya a jihar karkashin kungiyar ‘yan sandan Najeriya mai ritaya (ARPON), dauke da kwalaye masu rubuce-rubuce daban-daban kamar su “Shugaban kasa, NASS da IGP ya kamata a girmama ‘yan sanda su kebe ‘yan sanda daga CPS, su kafa hukumar ‘yan sanda ta fensho don gudanar da gratuity da fansho, idan CPS na da kyau haka, me ya sa AIGs da sauran su suka fice daga cikin shirin?   Da yake jawabi ga ‘ya’yan kungiyar a lokacin zanga-zangar lumana a Ilorin, shugaban kungiyar, Yakubu Jimoh,...
    Gwamnatin Libya ta tasa keya daruruwan baƙin haure ‘yan ƙasar Sudan 700 zuwa ƙasarsu da yaƙi ya ɗaiɗaita, A cewar mahukuntan, waɗannan mutanen sun yi hijira zuwa Libya ne domin gujewa yaƙi da talauci, inda suke neman hanyar tsallakawa zuwa Turai. A cewar huƙumar kula da baƙin haure, an kori mutane 700 daga Libya da aka kama a tsakiya da kudu maso gabashin ƙasar, inda aka tura su zuwa Sudan a ranar Juma’ar da ta gabata ta ƙasa. Bayanin ya nuna cewa wasu daga cikin waɗanda aka korar na ɗauke da cututtuka masu yaɗuwa kamar su hepatitis da cuta mai karya garkuwar jiki, wasu kuma an tura su ne saboda laifuffuka ko kuma dalilan tsaro. Korar ta zo ne a...
    Mataimakiyar Shugaban Majalisar Dinkin Duniya, Hajiya Amina Mohammed, ta yaba wa Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa kokarinsa wajen inganta ci gaban zamantakewar al’umma da kuma tallafawa aiwatar da Muradun Cigaba mai Dorewa (SDGs). Hajiya Amina Mohammed ta kai ziyara Jihar Kano ne domin yin ta’aziyya ga gwamnati da al’ummar jihar bisa rasuwar fitattun dattawan nan  biyu, wato Alhaji Aminu Alhassan Dantata da tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari. A yayin ziyarar tata, Mataimakiyar Shugaban Majalisar Dinkin Duniyar ta nuna gamsuwa da wasu daga cikin shirye-shiryen Gwamna Yusuf na cigaban al’umma, musamman wadanda suka yi daidai da muradun ci gaban duniya. Daga cikin wadannan shirye-shirye akwai sanya fitilu masu amfani da hasken rana a titunan Kano, kafa cibiyar kula...
    Jami’in harkar shari’ar kasa da kasa ya bayyana cewa: Harin da aka kai wa Iran babban laifi ne kuma jarrabawa ce ta tarihi ga kwamitin sulhu Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran kan harkokin shari’a da kasa da kasa, Kazem Gharibabadi, ya ce: Harin da aka kai wa Iran babban laifi ne, kuma jarrabawa ce ta tarihi ga kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya. A yayin wani taron manema labarai da ya yi da wakilan kasashe mambobin Majalisar Dinkin Duniya fiye da 110 a birnin New York na kasar Amurka a jiya Litinin, Gharibabadi ya bayyana ma’auni na wuce gona da iri da gwamnatin yahudawan sahayoniyya da Amurka suka dauka kan yankin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kuma sakamakonsa ga zaman...
    Kwamandan rundunar hadin gwiwar hedikwatar tsaron saman Iran ya jaddada cewa: Duk wani sabon kuskure da ‘yan sahayoniyya suka aikata zai haifar da mummunan sakamako Kwamandan rundunar hadin gwiwar hedikwatar tsaron saman Iran kuma  kwamandan bataliyar Khatam al-Anbiya (s.a.w) Birgediya Janar Alireza Sabahi Fard, ya jaddada cewa: Duk wani sabon kuskure da yahudawan sahayoniyya za su sake yi, zai haifar da mummunan sakamako. Birgediya Janar Seyyed Majid Mousavi, kwamandan rundunar sararin samaniyar Iran na dakarun kare juyin juya halin Musulunci ta Iran ya ziyarci hedikwatar hadakar tsaron sojojin saman na Khatam al-Anbiya, inda ya tattauna da Birgediya Janar Sabahi Fard, kan sakamakon arangamar da sojoji suka yi a baya-bayan nan da kuma hanyoyin inganta hadin kan tsaro. A zaman taron,...
    Jami’in kungiyar Hamas ya bayyana cewa: Kamen da hukumar Falasdinawa ta yi wa ‘yan gwagwarmaya a yankin Gabar Yammacin Kogin Jordan yana nuna goyon baya ne ga ‘yan mamayar Isrta’ila Jami’in kungiyar Hamas Abdel Rahman Shadid ya bayyana cewa: Kamen da jami’an tsaron Hukumar Falasdinawa suka yi na wani gungun ‘yan gwagwarmaya a Nablus da Jenin, da kwace makamansu, da kuma ci gaba da fatattakar ‘yan gwagwarmaya a duk fadin yankin gabar yammacin kogin Jordan, yana nuni da ci gaba da goyon bayan gwamnatin mamayar Isra’ila ce da murkushe al’ummar Falastinu. A cewar cibiyar yada labaran Falasdinu, Shadid ya jaddada a cikin wata sanarwa da ya fitar cewa: Kamen da jami’an tsaron hukumar cin gashin kan Falasdinawa suka yi kan...
    Mataimakin shugaban kasar Iran na farko ya jaddada cewa; Ra’ayin gwamnati shi ne tattaunawa akan fagen yadda al’amura zasu karfafa Mataimakin shugaban kasar na farko na kasar Iran Mohammed Reza Aref ya bayyana cewa: Babu wani bambanci tsakanin diflomasiyya da fannin, inda ya ce har yanzu ra’ayin gwamnati shi ne tattaunawa kan hanyoyi kyautata gudanar da madafun iko. A yayin ganawarsa da malaman jami’ar Shariff ta fasahar kere-kere, Aref ya yaba da irin rawar da al’ummar Iran suka taka a yakin kwanaki 12 da yahudawan sahayoniyya da Amurka suka dorawa Iran, inda ya ce: Matsayin al’ummar Iran da kasancewarsu a fagen kare kasar ya kasance mai karfi wajen yakar makiya, saboda dabarun makiya shi ne cewa bayan harin da aka...
    Mamba a kwamitin tsaron kasar Iran ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran zata zama daya daga cikin manyan kasashen duniya Ala’uddin Boroujerdi mamba a kwamitin tsaron kasa da manufofin kasashen waje na majalisar shawarar Musulunci ya bayyana cewa: Kisan gillar da aka yi wa fitattun malamai irin su Shaheed Tehranji ba zai kawo cikas ga ci gaban ilimi na Iran ba, illa dai zai kare daliban da suka yi karatu karkashin tallafin wadannan malamai don ci gaba da tafarkinsu tare da rubanya hidimarsu. Boroujerdi ya yi ishara da ma’auni na Shaheed Tehranji, inda ya bayyana shi a matsayin fitaccen malami da ya yi karatu a makarantar Imam al-Khameini, kuma jagoran juyin juya halin Musulunci. Ya tabbatar da cewa al-Shahed...
    Ministan yakin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila yana alfahari da rusa Gaza da tarwatsa mazauna yankin! Isra’ila Katz, ministan yakin gwamnatin mamayar Isra’ila, ya wallafa wani hoto da ya nuna yadda aka lalata garin Beit Hanoun a arewacin zirin Gaza, yana mai alfahari da yadda aka rusa gine-ginen garin”. Kuma ta hanyar dandalin “X”, Kats yayi sharhi game da hoton, yana cewa: “Bayan Rafah da Beit Hanoun.. babu mafaka ga ‘yan ta’adda. Hoton da aka dauka ta sama yana nuni da dimbin baraguzan gine-gine da kango da kuma irin barnar da aka yi wa daukacin garin da ke daura da layin da aka shimfida da tarwatsewar kango da ragowar gine-ginen da suka ruguje a hoton inda ke nuni irin girman bala’in...
    Sanata Yemi Adaramodu, mai magana da yawun Majalisar Dattawa, ya ce matsalar tsaro a Najeriya na raguwa, kuma tattalin arziƙi ya fara farfaɗowa. Ya yaba da ƙoƙarin da sojoji ke yi wajen yaƙi da ’yan bindiga da ’yan ta’adda. Haɗakar ’yan hamayya alheri ce ga siyasar Nijeriya — Gbajabiamila WFP ya dakatar da tallafin abinci a Yammaci da Tsakiyar Afirka “Sojoji suna ƙoƙari saboda muna ba su isasshen kuɗi don siyan makamai da kula da jin daɗinsu. Yanzu matsalar ’yan bindiga ta ragu a wasu jihohi, kuma ana magance ta.” Ya ƙara da cewa satar mutane ta ragu: “A da, mutane ba sa iya bacci saboda tsoro. Amma yanzu abubuwa sun ɗan gyaru. Sai dai waɗanda za su sa siyasa...
    Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Nijeriya, Femi Gbajabiamila ya ce haɗakar ’yan siyasa a jam’iyyar ADC alheri ce ga siyasar Nijeriya. Ya bayyana cewar haɗaka ’yan adawar za ta taimaka wajen hana ƙasar faɗawa cikin siyasar jam’iyyar ƙwaya ɗaya tal. WFP ya dakatar da tallafin abinci a Yammaci da Tsakiyar Afirka Za a sa zare tsakanin Amurka da Turai kan harajin kasuwanci Gbajabiamila ya bayyana haka ne jim kaɗan bayan ya kaɗa ƙuri’arsa a zaɓen ƙananan hukumomin da aka yi a Jihar Legas a jiya Asabar a mazaɓarsa da ke Surulere. Sai dai tsohon shugaban Majalisar Wakilan ya bayyana shakkunsa kan haɗakar, inda ya ce ce ba ya tunanin za ta yi wani tasirin a-zo-a-gani. “Muna maraba da samar da haɗakar....
     Shugaban kasar Korea ta Arewa ya bayyana goyon bayan sag a kasar Rasha a yakin da take fafatawa da kasar Ukraine. Kafafen yada labarai na Korea ta Arewa sun bayyana cewa Kim Jong Un ya fadawa ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Layrov, a cikin xiyarar kwanaki 3 da ya kai ziyara kasar. Kasar korea ta Areawa dai ta sha taimakawa kasar Rasha da sojoji da kuma makamai ma yakin da take fafatawa da kasar Ukraine fiye da shekaru uku da suka gabata. Kim ya hadu Lavrov ne a kan iyakokin kasashen biyu na ruwa da ke Wonsan . Kasashen bi yu sun tattauna karin taimakawa juna a bangaren tsaro.  KCNA ya bayyanan cewa shuwagabannin biyu sun tattauna al-amura da...
    Benyamin Natanyahu firai ministan HKI ya amince da cewa gwamnatinsa ta kashe masana fasahar Nukliya na kasar Iran da dama, don haka kasar ci gaba a wannan bangaren. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Natanyahu yana fadar haka a lokacinda yake hira da tashar talabijin ta Amurka mai sun a FOX NEWS. Wannan ikrarin dai ya fidda shakka da ake da shi ne cewa gwamnatin HKI ce take kashe masana fasahar Nikliyar kasar kuma wannan furucin ya zama shaida a kansa a duk lokacinda al-amarin ya zaman a shari’a. Har’ila yau furucin ya tabbatar da cewa HKI tana zagon kasa wa JMI wacce shirin makamashin nukliyar ta, ta zaman lafiya ce karkashin kula na hukumar IAEA. Banda...
    A wani bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta, Usman Dako ya bayyana yadda aka kori iyalinsa, aka rusa gidansu, aka kuma tsorata matarsa da ‘ya’yansa. Ya ce gida ne da aka ware wa mahaifinsa tun zamanin marigayi Sarki Ado Bayero, amma yanzu an rusa shi ba tare da haƙƙi ba. Dako ya dage da cewa zai ci gaba da nuna biyayya ga Aminu Ado Bayero, duk kuwa da korar da aka yi masa. Har yanzu dai Sarki Sanusi bai ce uffan ba game da lamarin, kuma ba a samu wani bayani daga majalisar Sarakunan ba. Ana sa ran za a ci gaba da sauraron shari’ar nan ba da jimawa ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun...
    Kakakin ma’aikatar sharia a nan Iran ya bayyana cewa shi bai da wata masaniya dangeneda cewa HKI ta kai hare-hare kan gidan yarin Evin na Tehran ne don kashe ma’aikatanta da aka kama aka kuma tsare a gidan yarin. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto kakakin na ma’aikatar sharia yana fadar haka a nan Tehran ya kuma kara da cewa, a cikin yakin kwanaki 12 da ya gabata jami’an tsaron kasar Iran sun kama ma’aikatan leken asirin na HKI da dama a lokacin, suna aikawa Haramtacciyar kasar Rahotanni a cikin yakin. A lokacinda aka tambayeshi kan cewa kun gano cewa hare-haren ranar 22 ga watan Yunin da ya gabata a cikin yakin kwanaki 12, HKI ta kai...
    Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar ya bayyana hukumar kula da shige da fice ta Najeriya a matsayin matakin farko na tsaro wajen kare rayuka da dukiyoyi a kasar.   Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin daliban jami’ar Immigration da ma’aikatan kwalejin Sokoto a ziyarar ban girma a fadarsa.   Ya yi kira da a samar da jami’an shige-da-fice don duba bakin haure da ke barazana ga zamantakewa da ci gaban tattalin arzikin kasar.   Ya kara da cewa galibin ‘yan kungiyoyin ta’addanci irin su Lakurawas da Boko Haram ba ’yan Najeriya ba ne.   Jagoran ya bayyana cewa, hukumar shige da fice na taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da tsaron...
     Shugaban kasar Korea ta Arewa ya bayyana goyon bayan sag a kasar Rasha a yakin da take fafatawa da kasar Ukraine. Kafafen yada labarai na Korea ta Arewa sun bayyana cewa Kim Jong Un ya fadawa ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Layrov, a cikin xiyarar kwanaki 3 da ya kai ziyara kasar. Kasar korea ta Areawa dai ta sha taimakawa kasar Rasha da sojoji da kuma makamai ma yakin da take fafatawa da kasar Ukraine fiye da shekaru uku da suka gabata. Kim ya hadu Lavrov ne a kan iyakokin kasashen biyu na ruwa da ke Wonsan . Kasashen bi yu sun tattauna karin taimakawa juna a bangaren tsaro.  KCNA ya bayyanan cewa shuwagabannin biyu sun tattauna al-amura da...
    A cikin wannan mako dai an yi ta murna da farin ciki a fadin jihar Kano inda dubban ‘yan fansho suka fara karbar kudaden fansho da garatuti da aka dade ba su yi ba.     Kudaden da aka fitar na ‘yan fansho na jihar Kano, sun kasance wani babban ci gaba a kokarin da gwamnan ke ci gaba da yi na biyan bashin zunzurutun kudi har naira biliyan 48 na kudaden alawus-alawus da kuma na mutuwa da ya gada daga gwamnatocin baya.   ‘Yan fansho da suka karbi kudadensu sun nuna matukar godiya ga Gwamna Yusuf kan abin da mutane da yawa ke kira a matsayin hanyar rayuwa bayan shekaru da aka yi watsi da su.   Daga cikin...
    Shirin Samar da Abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya (WFP) ya sanar da dakatar da bayar da tallafin abinci a ƙasashen Yammaci da Tsakiyar Afirka da ke fama da rikici. Hakan dai na zuwa ne a sakamakon rage tallafin da Amurka ke bayarwa na kuɗi ƙarƙashin Hukumar USAID, wanda hakan ke kawo cikas ga ayyukan wannan ƙungiyar. Za a sa zare tsakanin Amurka da Turai kan harajin kasuwanci An sanya dokar hana fita a Adamawa Duk da cewa lokaci ya bambanta daga ƙasa zuwa ƙasa, ana hasashen kayan abinci za su isa zuwa kusan watan Satumba a mafi yawan ƙasashen da abin ya shafa, wanda hakan zai bar miliyoyin mutane masu rauni cikin halin rashin tallafin gaggawa, a cewar WFP. “Muna...
    ‘Rundunar ‘yan sandan jihar Kwara ta ce ta kama wasu da ake zargi da aikata laifuka, ta kwato bindigogi, da kuma kama sama da Naira miliyan 11 da ake zargin kudin fansa ne a cikin wannan lokaci.   Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Adekimi Ojo ne ya bayyana haka yayin da yake zantawa da manema labarai a Ilorin.   A cewarsa jami’an ‘yan sanda tare da hadin gwiwar kungiyoyin tsaro na cikin gida sun cafke wani kasurgumin mai garkuwa da mutane mai suna Idirisu Sariki a Okuta, karamar hukumar Baruten.   Ojo ya ce ana kyautata zaton Sariki na da alaka da sace-sacen mutane da dama a yankunan kan iyaka a jihar   Ya bayyana cewa, a yayin samamen jami’an tsaro...
    Dan majalisa mai wakiltar mazabar Katagun ta tarayya a jihar Bauchi Alh. Awwalu Abdu Gwalabe, ya bayar da hujjar cewa tattalin arzikin Najeriya na da karfin da zai iya dorewar karin jihohi 12.   Ya bayyana haka ne ga manema labarai a wajen taron jin ra’ayin jama’a kan sake duba kundin tsarin mulkin 1999 a Arewa maso Gabas a Gombe   Alh. Awwalu Gwalabe, ya ci gaba da cewa, idan har Gwamnatin Tarayya za ta iya kashe Naira tiriliyan 17 wajen gina titin lagos-calabar kadai, hakan na nuni da cewa tattalin arzikin zai iya dorewar samar da karin jihohi.   Ya ce sama da shekaru arba’in ne al’ummar shiyyar katagun a jihar Bauchi suke ta tada jijiyoyin wuya na ganin...
    Shugaba Trump da abokansa sun ce sun gano cewa ana tafka almundahana da zamba a hukumar. Rahoton na zuwa ne yayin da gomman shugabannin duniya ke taro a Birnin Sabeilla na kasar Sifaniya cikin makon nan domin tattauna batun katse tallafin, wanda ya fi kowane bayar da agaji a duniya. Bayan nazarin bayanan alkaluman tallafin hukumar a kasashe 133 a duniya, binciken ya kiyasta cewa tallafin USAID ya rage mutuwar mutum miliyan 91 a kasashe masu tasowa tsakanin 2001 zuwa 2021. Sun kuma yi amfani da wani kiyasi wajen hasashen yadda rage tallafin da kashi 83% adadin da gwamnatin Amurka ta sanar a farkon wannan shekara na iya shafar adadin masu mutuwa. Rahoton ya ce katse tallafin zai haifar da...
    An haifi Peter Rufa’i a ranar 24 ga watan Agusta, 1963, a Oshodi, Legas, a wani gidan sarautar gargajiya, Mahaifinsa shi ne sarkin kabilar Idimu a Jihar Legas, duk da hasashen da ake yi na cewa zai yi gadon sarautar gidansu, Rufa’i ya yi watsi da sarautar don ci gaba da fuskantar abin da yake sha’awa wato kwallon kafa. 2. Ya yi Wasa A Manyan Kungiyoyin Kwallon Kafa A Kasashen Turai Rufa’i ya fara sana’ar kwallon kafa a kungiyoyin gida Nijeriya kamar Storeery Stores da Femo Scorpions kafin ya tsallaka zuwa kasar waje, ya taka leda a kungiyoyi a kasar Benin (Dragons de l’Ouémé), Belgium (Lokeren, Beberen), Netherlands (Go Ahead Eagles), Portugal (Farense, Gil Bicente), da Spain (Hércules, Deportibo La...
    An nada Dabide Ancelotti, dan gidan tsohon kocin Real Madrid kuma kocin babbar tawagar kasar Brazil Carlo Ancelotti a matsayin sabon kocin Botafogo, in ji kulob din na birnin Rio de Janeiro, Ancelotti, mai shekaru 35, ya shirya fara aikin horarwa na farko bayan ya zama mataimakin mahaifinsa a kungiyoyin Real Madrid, Eberton, Napoli da Bayern Munich. Zai maye gurbin Renato Paiba wanda aka kora bayan Botafogo ta fice a zagayen 16 na gasar cin kofin duniya, Dabide Ancelotti ya rattaba hannu kan kwantiragi har zuwa karshen shekarar 2026, ya koma kasar Brazil domin kasancewa cikin masu horar da ‘yan wasan kasar Brazil tare da mahaifinsa, amma an sauke shi daga matsayinsa don ba shi damar karbar ragamar horar da...
    Watanni shida bayan da kasar Uganda ta rufe iyakokinta da DRC, saboda yadda kungiyar M23 take kama yankuna, ta sake bude ta a halin yanzu. Jami’in sojan kasar Uganda, Chris Magezi ya tabbatar da sake bude kan iyakar a wata sanarwa da ya yi ta kafar sadarwa ta al’umma, yana mai cewa an yi hakan ne bisa umarnin shugaban kasar Yoweri Museveni. Har ila yau jami’in sojan kasar ta Uganda ya ce za a gudanar da bincike akan wadanda su ka jawo rufe iyakar da ya kawo tsaiko a harkokin kasuwanci a tsakanin al’ummun kasashen biyu. Wannan matakin da gwamnatin kasar ta Uganda ya biyo bayan kulla yarjejeniyar zaman lafiya ce a Washington, inda Rwanda da DRC su ka amince...
    Dakarun rundunar “Shahid Izzuddin al-kassam’ da kuma ” Sarayal Kuds” sun sanar da kai jerin hare-hare akan sansanonin ‘yan sahayoniya a yankuna mabanbanta na Gaza. A bayanin da dakarun ” Kassam” su ka fitar sun bayyana hare-hare masu yawa da su ka kai wa ‘yan mamaya, da su ka hada da tarwatsa motocin buldoza biyu samfurin D9 a unguwar Zaituna a cikin birnin Gaza. Haka nan kuma sun kai wani harin a ranar 6 ga watan Yuli wanda su ka rusa tankar yaki ta “Mirkava” ta hanyar amfani da wata nakiya mai tsananin fashewa. Bugu da kari , Kassam ta ce a ranar 9 ga watan Yuli din ta kai wani harin akan sansanin da kwamandoji masu bayar da umarnin...
    Gwamnatin Adamawa ta ayyana dokar ta baci ta hana zirga-zirgar mutane na tsawon sa’o’i 24 a Karamar Hukumar Lamurde da ke Kudancin jihar. Bayanai sun ce wannan lamarin na zuwa ne bayan samun rahotannin mutuwar kimanin mutane hudu a wani sabon rikici na kabilanci da ya auku a yankin. Tinubu ya dawo Najeriya bayan ziyarar aiki a Saint Lucia da Brazil Sanatan Abuja ta sauya sheƙa zuwa ADC DW ta ruwaito kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Suleiman Nguroje yana ba da shaidar matakan da suke dauka domin dakile rikicin. Kazalika Kwamishin ’yan sandan jihar, Dankombo Morris ya kaddamar da kwamitin bincike kan musabbabin afkuwar lamarin. Kana Kwamishinan ya ba da umarnin jibge ’yan sandan kwantar da tarzoma a yankin...
    A nasa jawabin, shugaban hukumar NAFDAC na shiyyar Arewa maso yamma, Nantim Dadi Mullah, ya bayyana gamsuwarsa dagane da matakin da kungiyar masu maganain gargajiya ta kasa ta dauka na kawo tsabta a sana’arsu. Ya tabbatar da cewa NAFDAC ta amince za ta yi aiki kafada da kafada da kungiyar domin ganin duk wani mai sana’ar maganin gargajiya ya yi rajista da hukumarsu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban kasar Guinea Bissau Umaro Sissoco Embalo, ya jinjinawa gudunmuwar kasar Sin ga ci gaban kasarsa. Da yake jawabi jiya a fadar shugaban kasar yayin da yake bitar ziyara ta baya-bayan nan da ya kai Amurka, shugaba Embalo ya ce kasar Sin abokiyar hulda ce ta hakika, kuma sahihi yayin da take bayar da taimako. Ya ce babu wanda ke gindaya sharudi a hadin gwiwarsu da Sin, yana mai nanata cewa Guinea Bissau kasa ce mai cikakken ‘yanci kuma ‘yar ba ruwanmu. A cewarsa, kasar Sin ta kasance abokiyar kasar tun farko kuma ba ta taba watsi da su ba. Yana mai bayyana ta da hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu a matsayin mai matukar inganci. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)...
      Ko za ka iya fada wa masu karatu dan takaitaccen tarihinka? An haife ni a Unguwar Adakawa cikin birnin Kano, na yi makarantar firamare a Adakawa, daga nan kuma na tafi zuwa makarantar sakandire (Gwammaja One), bayan na sauke Alkur’ani, daga baya na tafi sai na wuce zuwa ‘School of Health Technology’ ta Kano. Bayan nan, sai kuma na tsunduma harkokin kasuwanci da siyasa, kazalika ina da mata biyu da kuma ‘ya’ya goma a halin yanzu.   Kamar wane irin kasuwanci kake yi? Ina harkar takalma ‘yan Kofar Wambai, wadda ita ce sana’ar dana fara koya, sannan kuma ita ce sana’ar da dangina suke yi.   Me ya ja hankalinka har ka tsunduma cikin masana’antar Kannywood? Tun ina yaro...
    Har ila yau a wannan rana, Wang Yi ya gana da ministan harkokin wajen Sri Lanka Vijitha Herath a birnin na Kuala Lumpur. Bugu da kari, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya mai da martani a yau Asabar game da furucin da Philippines ta yi kan sanarwa game da bikin cika shekaru 9 da fitar da hukuncin takkadamar “Philippines v. China”, inda ya bayyana cewa, “hukuncin” ya saba wa ka’idojin dokokin kasa da kasa da kuma yarjejeniyar MDD kan batun teku, kuma ya sabawa ainihin gaskiyar dake tattare da batun tekun kudancin kasar Sin, haka kuma ba shi da wata daraja ko amfani.(Safiyah Ma) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin...
    Eh, wasu mata suna daukar lambar motar duk wanda ya yi musu kyau ko ya zo da motar alfarma, su kai wa malami ko boka domin a janyo hankalinsa ya zo neman aurensu. Hakan kuskure ne babba, ba daidai ba ne a nemi aure ta hanyar sihiri ko dabara marar tsarki. Duk wata riba da ke tattare da hakan ba ta da karko, kuma tana iya dawo da akasin abin da aka nema, kamar rashin samun auren kwarai da tsayayye, zama da mutumin da ba da gaske yake ba, daukewar albarka daga rayuwa, fushin Allah da rushewar aure cikin lokaci. Shawara ga masu haka; ku dogara da addu’a, tarbiyya da hakuri, idan aure naku ne, zai zo da sauki cikin...
    Ya jaddada buƙatar samar da tsarin adalci da zai bai wa ƙasashe masu tasowa damar cin moriyar ci gaban fasaha da samun rance cikin sauƙi daga ƙasashen duniya. Ya kuma bayyana yadda Afirka ke fuskantar manyan matsalolin muhalli duk da cewa ba ta fitar da gurbataccen hayaƙi sosai. A gefe guda kuma, Tinubu ya bayyana shirye-shiryen gyaran da gwamnatinsa ke yi, ciki har da amfani da makamashi, yaƙi da sauyin yanayi, gina birane da kuma inganta harkar kiwon lafiya ga kowa. Ya ce Nijeriya za ta ci gaba da aiki tare da sauran ƙasashe masu tasowa. Jawabin Tinubu a taron BRICS na 2025 ya nuna matakin farko da Nijeriya ta taka a matsayin ƙasa mai ƙawance da BRICS. Nijeriya ta...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: An mika fayil ɗin haɗin gwiwa tare da Hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa ga kwamitin koli na tsaron ƙasa Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana a wata ganawa da jakadun kasashen waje da na kasa da kasa cewa: Iran bangare ce a yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya ta “NPT” kuma tana yin aiki da tanade-tanaden da aka yi mata, amma idan aka yi la’akari da sabbin yanayi da abubuwan da suka faru a baya-bayan nan, hadin gwiwarta da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA za ta dauki wani sabon salo. Yayin da yake ishara da cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana ci gaba...
    Dakarun juyin jaya halin Musulunci ta Iran sun kama wani wakilin hukumar leken asirin Isra’ila Mossad a arewacin kasar Iran Dakarun kare juyin juya halin Musulunci sun sanar da kame wani jami’in hukumar leken asirin haramtacciyar kasar Isra’ila “Mossad” a lardin Mazandaran (arewacin kasar Iran), wanda ke shirin kai harin ta’addanci a cikin kasar. Sanarwar da dakarun kare juyin juya halin suka fitar ta bayyana cewa: wani ma’aikacin fage na makiya da ke shirin aiwatar da ayyukan ta’addanci ta hanya kai tsaye wajen jagorantar masu adawa da Iran a kasashen waje, an kama shi ne a wani gagarumin samame da jami’an leken asirin na Karbala suka kai, kafin ya aiwatar da duk wani aikin ta’addanci. Sanarwar ta kara da cewa:...
    Gwamantin kasar Mauritaniya ta musanta cewa shugabanta ya gana da Netanyahu, ta yi kira ga tashar Al Arabiya da ta tabbatar da sahihancin rahoton kafin watsa shi Ministan al’adu da sadarwa na Mauritaniya kuma mai magana da yawun gwamnatin kasar Hussein Ould Maddou ya musanta sahihancin rahotannin ganawar da ake zargin shugaban kasar Mauritaniya da Fira ministan haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu. Kamfanin dillancin labaran Jamus ya nakalto ministan na cewa rahoton da tashar Al Arabiya ta watsa game da ganawar da ake zargin shugaba Mohamed Ould Ghazouani da Fira ministan Igwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ba shi da tushe balle makama. Ya yi nuni da cewa, labaran ba su da inganci, inda ya yi kira ga tashar Al-Arabiya da ta...
    Sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da kai hare-hare a yankuna daban-daban na Gaza, kuma Falasdinawa da dama sun yi shahada Jiragen yakin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila sun ci gaba da ruwan bama-bamai a yankuna daban-daban na zirin Gaza a rana ta 117 da yakin ya yi sanadiyar shahadan Falasdinawa da dama. A cewar majiyoyin kiwon lafiya, sama da Falasdinawa 45 suka yi shahada tun daga wayewar garin Juma’a a zuwa safiyar yau a yankuna daban-daban na zirin Gaza. Yousuf Al-Zaq, wanda aka bayyana shi a matsayin fursuna mafi ƙanƙanta bayan mamayar da aka kai wa gidansa da ke kan titin Al-Thawra a tsakiyar Gaza ya yi shahada. An haifi Yousuf a cikin gidan yarin Isra’ila a shekara ta 2008,...
    Sanata Ireti Kingibe, wacce ke wakiltar Babban Birnin Tarayya, ta fice daga jam’iyyar LP zuwa ADC. Da ta ke magana da ’yan jarida a Abuja, ta ce wannan matakin nata wani shiri ne na tunkarar babban zaɓen 2027. Abin da ya faru tsakani na da DSS bayan kama ni — Ɗan Bello DSS ta saki Ɗan Bello bayan ta kama shi a Kano “Ni cikakkiyar mamba ce ta ADC yanzu,” inji ta. Da aka tambaye ta ko tana da ƙwarin gwiwa game da shugabancin ADC da haɗin gwiwar da suke ƙoƙarin ginawa, ta ce jam’iyyar na ci gaba da samun tagomashi. Tace kowace tafiya a sannu ake binta wanda daga bisani ta ke girma. Wasu sun nuna damuwa cewa wannan...
    Sanata Ireti Kingibe, wacce ke wakiltar Babban Birnin Tarayya, ta fice daga jam’iyyar LP zuwa ADC. Da ta ke magana da ’yan jarida a Abuja, ta ce wannan matakin nata wani shiri ne na tunkarar babban zaɓen 2027. Abin da ya faru tsakani na da DSS bayan kama ni — Ɗan Bello DSS ta saki Ɗan Bello bayan ta kama shi a Kano “Ni cikakkiyar mamba ce ta ADC yanzu,” inji ta. Da aka tambaye ta ko tana da ƙwarin gwiwa game da shugabancin ADC da haɗin gwiwar da suke ƙoƙarin ginawa, ta ce jam’iyyar na ci gaba da samun tagomashi. Tace kowace tafiya a sannu ake binta wanda daga bisani ta ke girma. Wasu sun nuna damuwa cewa wannan...
    Ya tunatar da cewa a bara, Antoni-Janar na Ƙasa kuma Ministan Shari’a ya nemi fassarar doka daga Kotun Ƙoli, inda kotun ta tabbatar da cewa kundin tsarin mulki ya tanadi ’yancin cin gashin kai ga ƙananan hukumomi.   “An samu hukunci daga babbar kotun ƙasa da ke nuna cewa kundin tsarin mulkin mu ya tanadi buƙatar ƙananan hukumomi su samu ’yancin kai – su kasance masu cikakken iko da damar aiki a fannoni daban-daban, ko siyasa ko kuma kuɗi,” inji shi.   A cewar sa, bai wa ƙananan hukumomi dama za ta ƙarfafa dimokiraɗiyya a matakin ƙasa da kuma samar da cigaba a cikin al’umma.   Idris ya nuna damuwa kan yadda tsarin ƙananan hukumomi ya raunana a tsawon lokaci,...
    Wasu da ake zargin Jami’an Hukumar Farin Kaya (DSS), sun kama fitaccen mai barkwancin nan a kafafen sada zumunta, Bello Habib Galadanci, wanda aka fi sani da Ɗan Bello, a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano. Sun kama shi ne bayan isowarsa filin jirgin saman, wanda hakan ya jawo hankalin mutane da dama, ciki har da fasinjoji da ma’aikatan filin jirgin. DSS ta saki Ɗan Bello bayan ta kama shi a Kano Yadda aka kama ɗan bindiga ɗauke da N13m a hanyar Jos Sai dai Ɗan Bello cikin wata hira ta wayar tarho da ya yi da kafar DCL, ya bayyana abin da ya faru, inda ya ce: “Dana sauko wasu mutane wanda kana ganinsu ka san hukumomi ne...
    Ƙungiyar Malaman Jami’a ta Ƙasa (ASUU), reshen Jami’ar Jihar Yobe (YSU), ta fara yajin aikin sai baba-ta-gani saboda gwamnati ta kasa cika alƙawuran da ta ɗaukar musu. Waɗannan alƙawura sun haɗa da ƙarin albashi, biyan bashin da suke bi, da kuma barin jami’ar ta riƙa gudanar da harkokinta da ƙashin kanta. Lakurawa sun kashe ’yan sanda 3 a Kebbi Yadda aka kama ɗan bindiga ɗauke da N13m a hanyar Jos Shugaban ASUU na Jami’ar Yobe, Dokta Ahmed Karage, ya bayyana hakan bayan kammala wani taro da suka gudanar. Ya ce sun fara yajin aikin ne bayan dogon lokaci da suka ɗauka suna tattaunawa da gwamnati, amma ba su cimma matsaya ba. “Mun kwashe watanni muna magana da gwamnati, amma abin...
    Ƙungiyar Malaman Jami’a ta Ƙasa (ASUU), reshen Jami’ar Jihar Yobe (YSU), ta fara yajin aikin sai baba-ta-gani saboda gwamnati ta kasa cika alƙawuran da ta ɗaukar musu. Waɗannan alƙawura sun haɗa da ƙarin albashi, biyan bashin da suke bi, da kuma barin jami’ar ta riƙa gudanar da harkokinta da ƙashin kanta. Lakurawa sun kashe ’yan sanda 3 a Kebbi Yadda aka kama ɗan bindiga ɗauke da N13m a hanyar Jos Shugaban ASUU na Jami’ar Yobe, Dokta Ahmed Karage, ya bayyana hakan bayan kammala wani taro da suka gudanar. Ya ce sun fara yajin aikin ne bayan dogon lokaci da suka ɗauka suna tattaunawa da gwamnati, amma ba su cimma matsaya ba. “Mun kwashe watanni muna magana da gwamnati, amma abin...
    ’Yan ta’addan Lakurawa sun karbe ’yan sanda uku har lahira a yankin Gozirma da ke Ƙaramar Hukumar Bunza a Jihar Kebbi. ’Yan sandan sun kwanta dama ne a yayin musayar wuta a yayin da ’yan ta’addan da ke ƙoƙarin kai hari ga matafiya a kan Babbar hanyar Gozirma zuwa Till. Kakakin ’yan sanda a Jihar Kebbi, ya sanar da cewa a yayin ƙazamin faɗan, “an kashe ’yan ta’adda da dama, amma wasu sun tsere da raunukan harbi a jikinsu. Sai dai kuma an yi rashin sa’a ’yan sanda uku sun kwanta dama a yayin arangamar.” Ya ƙara da cewa Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kebbi, Bello M Sani, ya yaba da namijin ƙoƙarin jami’an rundunar da ke yankin Zurmi da suka...
    Mai bawa jagoran Juyin Juya halin musulunci Imam Sayyid Ali Khamina’i, shawara Dr Ali Larijani ya bayyana cewa gwamnatin kasar Iran tana nazarin sakon gwamnatin Amurka na bukatar a farfado da tattaunawar shirin makamashin Nukliyar kasar tsakaninsu. Kamfanin dillancin labaran Ip na kasar Iran ya nakalto Dr Larijana yana cewa gwamnatin kasar Iran tana shakkar Amurka a cikin duk abinda zai hada su musamman bayan yaki kwanaki 12 da ita Amurka da kuma HKI suka dora mata. Dr Larijana ya fadawa tashar talabijin ta Aljazeera na kasar Qatar kan cewa, HKI da Amurka sun farwa kasar Iran da yaki ba tare da wani dalili ba, tana ma cikin tattaunawa da Ita kan shirin ta na makamas suka yi hakan. Suka...
    Jaridar NYT ta kasar Amurka ta bayyana cewa firai ministan HKI Benyamin Natanyaho da gangan yake tsawita yaki a Gaza don tsawaita zamansa a kan kujerar shugabancin kasar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto wani binciken da Jaridar New York Times ta yi, inda take cewa Natanyahu ya san cewa matukar ya sauya matsayinsa na shugaban gwamnatin HKI to kuwa sammashin kamasi da kuma tuhume-tuhumen da ake masa zasu tashi wadanda zasu zama masa matsala, kuma a lokacin hatta gwamnatin Amurka ba zata iya yi masa wani taimako ba. An fara yaki a Gaza ne a ranar 07 ga watan octoban shekara ta 2023 . daga lokacin ya zuwa yanzu sojojin Natanyahu sun kashe falasdinawa kimani 57,000....
    Ali Mohammad Sabeghi, tsohon jami’in bangaren al-adu na ofishin jakadancin kasar Iran a kasar China ya karbi kyautar ‘Jakadan Abota’ na kasar China a wannan shekara ta 2025M. A bikin bada irin wannan kyauta karo na biyu. Labarin ya kara da cewa dangantaka tsakanin JMI ta kuma China yana daga cikin abota mafi kyau tsakanin kasashen yankin da kasar China. Labarin ya kara da cewa girmama kasar Iran ta wannan kyautar yana daga cikin al-amuran da zasu kara dankon zumunci tsakaninta da Tehran. Hukumar al-adu na kasar China ta bayyana cewa ta samar da irin wannan kyautar ne don karfafa danganta kasar China da da sauran kasashen duniya musamman kasashen Asia. A shekarar da ta gabata dai wannan kyauta ta...
    Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov ya ja kunnen shuwagabannin kasashen yammacin Turai kan shiga yaki da kasar Rasha. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Lavrov yana fadar haka, a jiya Jumma’a. Ya kuma kara da cewa, labaran da suke isa kunnensa daga biranen Landan, Paris da kuma Berlin sun tabbatar masa da cewa, kasashen suna shirin yaki da kasar Rasha. Ya ce, Rasha ta sha fadawa kasashen yammacin Turai, ci gaba da goyon bayan kasar Ukrai zai jawosu zuwa yaki da kasar Rasha. Yaki wanda rabuwamma da irinsa tun bayan yakin duniya na II. Ya shay a sha fada masu kan cewa makaman da suke turawa Kiev daga karshe ba zai taba samar da zaman...
    Ana zargin wani direban tirela ya gudu da buhunan masara 463 da aka aike shi da su, bayan da ya bai wa ɗan rakiyarsa guba a cikin shayi a yankin Maraban Jos da ke Jihar Kaduna. Wani ɗan kasuwa da ke safarar hatsi daga Jihar Kano zuwa kamfanoni a sassa daban-daban na Nijeriya, Injiniya Jamilu Haruna, ya shaida wa Aminiya cewa direban da ya ɗora wa masara buhu 463 domin kaiwa kamfanin Olam da ke Ilorin a Jihar Kwara, ya gudu da kayan. “Kuɗin kayan sun kama Naira miliyan miliyan ashirin da ɗaya da dubu ɗari shida da tamanin da shida da ɗari huɗu. “Wallahi jarin nawa ke nan ɗungurungum na dora a motar,” in ji ɗan kasuwar, wanda ya...
    Ya kara da cewa, Asusun ya kuma gano fannonin aikin noman kasar da ya kamata a kara bunkasa su, wanda hakan ya sanya Asusun ya dauki wannan mataki. Ya ci gaba da cewa, duba da irin amfanin gonar da manoma ke nomawa a kasar, musamman kananan manoma da kuma ribar da suke samu daga fannin, wani abu ne da Asusun ya dauka da ke da matukar muhimmanci, wanda kuma hakan ne ya kara bai wa Asusun kwarin guiwar shirin fara kaddamar da aikin. Shi kuwa a nasa jawabin, Lanre Wilton-Wadell, mai taimaka wa Babban Sakataren a Asusun, ya yi bayani kan yadda za a gudanar da aikin. Ya bayyana cewa, Asusun zai bayar da kashi 100 na Irin noma da...
    Ana zargin wani ɗalibi da ke shekarar ƙarshe a jami’a da ƙona budurwarsa mai ɗauke da tsohon ciki a Jami’ar Fatakwal da ke Jihar Ribas. Wanda ake zargin da budurwar tasa mai suna Cynthia Chukwundah, dukkansu ɗaliban ajin ƙarshe ne a jami’ar. Ana zargin matashin ya ƙona Cynthia mai shekara 32 ne ta hanyar wata mata ruwan batir, daga bisani ta ce ga garinku nan. Cynthia ta gamu da ajalinta ne bayan saurayinta Sunny Amadi ya yi mata wannan aika-aika a gidansu da ke layin Okoro unguwar China da ke Birnin Fatakwal. Sojoji sun kama mai garkuwa da mutane da bindigogi Muna tunanin sayar da matatun man Najeriya — NNPCL Wani ganau da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida...
    Rahotanin sun bayyana cewa Shettima ya ziyarci Kano ne don yin ta’aziyyar rasuwar hamshakin dan kasuwa, Alhaji Aminu Dantata, wanda ya rasu kwanan nan, da kuma jajanta wa mutanen Kano kan wannan rashi. Haka kuma rahotannin sun bayyana cewa a irin wadannan manyan taruka a Nijeriya, an saba ganin shugabannin jam’iyya da goyon baya su tarbi manyan jami’ai kamar mataimakin shugaban kasa, amma lamarin ya bambanta yayin ziyarar Shettima, wanda ya haifar da zazzafar muhawara. Da yake musanta cewa akwai rikice-rikice na cikin gida a jam’iyyar, sakataren APC a Kano, Ibrahim Zakari Sarina, ya shaida cewa rashin halartar shugabannin jam’iyyar a ziyarar ta’aziyya da mataimakin shugaban kasa ya kawo Kano ya faru ne sakamakon rashin sadarwa. “Mun san cewa ziyarar...
    Kwanan baya, jagoran yankin Taiwan na kasar Sin Lai Ching-te ya gabatar da jawabai masu taken wai “jawabai 10 game da hadin kan al’umma”, da nufin ba da ingantacciyar hujja ga ra’ayinsa na shirme game da ballewar Taiwan daga kasar Sin, tare da yaudarar jama’ar yankin da kuma sauran al’ummun duniya. Kowa ya san yankin Taiwan wani bangare ne da ba za a iya raba shi da kasar Sin ba, kuma wannan shi ne matsaya daya da al’ummun Sinawa da yawansu ya kai biliyan 1.4 ciki har da jama’ar yankin Taiwan da yawansu ya kai miliyan 23 suka dauka, wanda kuma ra’ayi ne daya tilo da kasashen duniya suka cimma matsaya a kai. Sanawar Alkahira da sanarwar Potsdam da dai sauran takardun shari’a sun aza ingantaccen tubali ga dokar kasa...
    A dokar hukumar zabe ta 2010 sashe na 124, biyan kudi ga wani a matsayin cin hanci a kowane irin zabe ko karbar kudi ko kyauta domin jefa kuri’a ko hana jefa kuri’a a kowane zabe babban laifi ne da ke da hukuncin tarar naira dubu 500, 000 ko daurin watanni 12 a gidan gyaran hali ko kuma duka biyu. A kowane zabe kama daga na shugaban kasa zuwa kansila, Hukumar Zabe da hukumomin yaki da cin hanci da rashawa na fuskantar kalubale daga masu sayen kuri’a da ke canzawa masu zabe zaben ra’ayin kan su zuwa zaben wanda aka ba su kudi ko ma kin yin zaben. Duk da kama masu sayen kuri’a da hukumomin yaki da cin hanci...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, ta bayyana dalilin da ya sa ta gayyaci malamin addini Sheikh Lawal Triumph. A wata sanarwa da ta fitar, ’yan sanda sun ce sun sani cewa wasu daga cikin wa’azozin da Sheikh Triumph ke yi suna haddasa rashin jituwa a tsakanin al’ummar jihar. Ya kamata mulkin Najeriya ya ci gaba da zama a hannun ’yan Kudu — Hannatu Musawa Ba lallai matatun man gwamnati su sake aiki ba har abada a Najeriya – Ɗangote Rundunar ta ce kowa na da ’yancin faɗin albarkacin bakinsa, amma dole ne komai ya kasance bisa doka. Saboda haka ne Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar, ya gayyaci Sheikh Lawal Triumph don tattaunawa da jami’an gwamnati, shugabannin addini da na al’umma. Manufar...
    Kamfanin dillancin labarun “Associated Press” wanda ya sami hotunan tauraron dan’adam na cibiyar sojojin Amurka dake “al-udid” a kasar Qatar, ya nuna yadda harin ya sami wata Qubba, da a cikinta akwai na’urorin sadarwa da Amurka ke amfani da su.” Hotunan tauraron dan’adam na ” Planet Labs” sun nuna yadda Qubbar ta sansanin Amurka a Qatar take sa’o’i kadan gabanin a kai harin a ranar 23 ga watan Yuni. Rundunar Amurka ta 379 mai aikin ttatara bayanai ta kafa wannan Qubbar ne tun a 2016 da kudin da sun kai dalar Amurka miliyan 15. Haka nan  kuma tauraron dan’adam din ya nuna yadda qubbar ta  bace, da kuma yadda ginin da yake  kusa  da ita ya illata. Kamfanin dillancin labarun...
    Tashar talabijin din “Cane” ta HKI ta bukaci Amurka da ta kafa kawance mai fadi na kasashe domin fuskantar kasar Yemen. A yayin ziyarar da Fira ministan HKI, Benjamin Netanyahu a Amurka ne dai ya bijiro da wannan bukatar, kamar yadda rahoton tashar talabijin din ta “Cane” ya ambata.  Rahoton ya kuma ce, Jami’an HKI sun sanar da Amurka cewa, ci gaba da hare-haren Yemen, ya tashi daga zama matsalarta ita kadai, don haka da akwai bukatar kai hare-hare na hadin gwiwa da Amurka da kuma shigar da kasashen wannan yankin da kuma wasu na duniya.” Tun daga 2023 ne sojojin Yemen suke kai wa jiragen ruwa na HKI hare-hare a cikin tekun “Red Sea” ko kuma wadanda su ka...
    Ministan harkokin wajen Najeriya Yusuf Maitama Tuggar  wanda ya yi hira a wata tashar talbijin din kasar ya yi amfani da salon maganar wani mawakin Amurka  mai suna Flavour Flav da ya shahara a shekarun baya, wajen mayarwa da shugaban Amurka Donald Trump martani da cewa: Babu abinda zai iya yi ma ka.” Jaridar Wall Street Jouran ta buga labarin dake cewa; A yayin taron da aka yi a tsakanin wasu shugabannin kasashen Afirka biyar da shugaban kasar Amurka a fadar White House, an bijiro musu da karbar bakuncin ‘yan ci-ranin kasashe waje da Amurka take son kora daga cikinta. Jaridar ta ambaci Nigeria a cikin kasashen da Amurka ta bijirowa da bukatar ta karbi bakuncin ‘yan ci-ranin kasar Venezuela...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shi ma Shugaban Kwamitin Asusun Jama’a na Majalisar Dattawa, Sanata Ahmed Wadada, ya bayyana cewa wannan kyauta alama ce ta gaskiya da amincewa da ayyukan hukumar. Ya ce NPA ta nuna ƙwazo wajen bin ƙa’idojin lissafi da kuma tallafa wa hanyoyin bayyana gaskiya a ayyukan gwamnati. Shugaban NPA, Dr. Abubakar Dantosho, wanda ya karɓi kyautar a madadin hukumar, ya sake tabbatar da ƙudirinsa na yin gyare-gyare da kuma tabbatar da gaskiya a dukkanin ayyukan hukumar. Dr. Dantosho ya ƙara da cewa yin adalci da riƙon amana wajen harkokin kuɗi na daga cikin abubuwan da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke da niyya a ƙarƙashin shirin “Renewed Hope”. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da...
    An kaddamar da shirin koyar da Sinanci mai taken “Hello China”, na gidan rediyon Nijeriya (FRCN), a Abuja babban birnin kasar. Kusan mutane 100, ciki har da jakadan Sin a Nijeriya Yu Dunhai da darakta janar na FRCN Mohammed Bulama ne suka halarci bikin kaddamarwar da ya gudana a jiya Alhamis. Cikin jawabin da ya gabatar, Yu Dunhai ya ce kaddamar da shirin na koyar da Sinanci da gidan rediyon ya yi, zai samar wa ‘yan Nijeriya wani sabon dandali na koyon harshen Sinanci da fahimtar kasar Sin, tare da samar da kuzari mai dorewa ga hadin gwiwar moriyar juna a fannonin cinikayya da tattalin arzikin tsakanin Sin da Nijeriya Daga ranar 16 ga wata ne za a fara watsa...
    Ministar Raya Al’adu, Hannatu Musawa, ta ce ya kamata shugabancin ƙasar nan ya ci gaba da kasancewa a hannun ’yan Kudu domin a samu adalci da daidaito. Ko da yake kundin tsarin mulkin Najeriya bai tilasta tsarin karɓa-karɓa ba, manyan jam’iyyun siyasa suna bin tsarin sauya mulki tsakanin Arewa da Kudu. An tsare mutum 20 da ake zargi da kisan ’yan ɗaurin aure a Filato Ba lallai matatun man gwamnati su sake aiki ba har abada a Najeriya – Ɗangote A wata hira da ta yi da gidan talabijin na Channels a ranar Juma’a, Hannatu Musawa ta ce tun da an samu Shugaba daga Arewa (Muhammadu Buhari) na tsawon shekaru takwas, to ya dace yanzu kuma a bar ’yan Kudu...
    Taron ministocin kasa da kasa na tattaunawa kan wayewar kan bil Adama, wanda aka gudanar a birnin Beijing na kasar Sin daga ranar 10 zuwa ranar 11 ga watan nan, mai taken “Kiyaye bambancin wayewar kan al’adun bil’adama don samun zaman lafiya da ci gaban duniya”, ya ja hankalin baki daga kasashe da yankuna 140 da suka hada da ‘yan siyasa da ministocin gwamnatoci da kuma wakilan bangarori daban daban, inda suka yi musayar ra’ayin tare da cimma matsaya a fannoni da yawa, da kuma fitar da sanarwar Beijing, bayan kammala taron. Sanarwar ta bayyana cewa, mu’amalar wayewar kai muhimmin karfi ne wajen inganta ci gaban wayewar kan bil’adama da bunkasuwar zaman lafiyar duniya. Kuma ya kamata kasashe da kabilu daban-daban su...
    Wata Kotu a Jos, Babban Birnin Jihar Filato, ta tura mutum 20 da ake zargi da kisan ’yan ɗaurin aure a Jihar Filato zuwa gidan yari. Ana zarginsu da kashe wasu ’yan ɗaurin aure a ƙauyen Mangun da ke Ƙaramar Hukumar Mangu a jihar. Ba lallai matatun man gwamnati su sake aiki ba har abada a Najeriya – Ɗangote NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Wasu Matasa Ba Sa Aiki Tukuru Wajen Neman Arziki Mutanen da aka kashe suna cikin wata motar haya da ta taso daga Basawa a Karamar Hukumar Sabon Gari ta Jihar Kaduna. Baƙin suna kan hanyarsu ta zuwa ƙauyen Kwa a Ƙaramar Hukumar Qua’an Pan da ke Jihar Filato domin halartar ɗaurin aure. Wasu ɓata-gari ne suka...
    Amurka ta bayyana dalilin sabunta manufofin, tare da lura da cewa “an tsara sharuddan bizar Amurka da ka’idoji domin kare tsarin shige da fice na Amurka.” Ofishin jakadancin ya kara da cewa “wadannan ka’idoji sun dogara ne kan ma’aunin fasaha da tsaro na duniya.” A cewar ofishin jakadancin Amurka yana aiki tare da hukumomin Nijeriya domin cimma wadannan matakan. Sanarwar ta ce “Tawagar Amurka tana aiki tare da gwamnatin Nijeriya domin tabbatar da cewa Nijeriya za ta iya cika sharuddan.” Misalin wannan sabon tsari ya hada da “Takardun tafiye-tafiye masu aminci: tabbatar da cewa kasashe suna ba da amintattun takaddun balaguro tare da ingantattun bayanan matafiyi, Kada aikin gudanar da Bisa ya wuce lokacin da aka dauka:.” Duk da sabbin...
    Kididdigar ta nuna cewa maimakon amfani da wannan kudaden shigar don rage basussuka, wasu jihohi suna kara amso bashin. Jihar Ribas ta zama ta farko a jerin jihohin da adadin bashin cikin gida na naira biliyan 364.39 a wata uku na farkon 2025, mafi girma tsakanin jihohi 10. Basukan Jihar Inugu sun tashi daga naira biliyan 82.48 a farkon wata uku na 2024 zuwa naira biliyan 188.42 a farkon wata uku na 2025, wanda ke nuna karuwa na naira biliyan 105.95 ko kashi 128.4 cikin dari. Jihar Neja ta biyo baya da karuwar naira biliyan 57.68 a kowanne shekara, daga naira biliyan 86.07 zuwa naira biliyan 143.75, wanda shi ne karuwa na kashi 67 cikin 100. Jihar Taraba ta nunka...
    Wata Kotu a Jos, Babban Birnin Jihar Filato, ta tura mutum 20 da ake zargi da kisan ’yan ɗaurin aure a Jihar Filato zuwa gidan yari. Ana zarginsu da kashe wasu ’yan ɗaurin aure a ƙauyen Mangun da ke Ƙaramar Hukumar Mangu a jihar. Ba lallai matatun man gwamnati su sake aiki ba har abada a Najeriya – Ɗangote NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Wasu Matasa Ba Sa Aiki Tukuru Wajen Neman Arziki Mutanen da aka kashe suna cikin wata motar haya da ta taso daga Basawa a Karamar Hukumar Sabon Gari ta Jihar Kaduna. Baƙin suna kan hanyarsu ta zuwa ƙauyen Kwa a Ƙaramar Hukumar Qua’an Pan da ke Jihar Filato domin halartar ɗaurin aure. Wasu ɓata-gari ne suka...
    Ɗangote Ya ƙara da cewa “A yau, bayan kashe sama da dalar Amurka biliyan 18 wajen gudanarwa tare da gyara matatun man har yanzu basa aiki. Kuma bana tunanin nan gaba za su iya ci gaba da aiki. Ƙoƙarin zamanantar da su kamar misalin zamanantar da tsohuwar motar da ta yi shekara 40 ne, ko an canja inji ba zai sa ta koma dai-dai da ta zamani ba”. Alhaji Aliko Ɗangote ya ce ya yanke shawarar gina matatar man fetur ne mai fitar da ganga dubu ɗari shida da hamsin a rana bayan da marigayi Umaru Musa Yar’adua ya yanke shawarar ƙin siyar masa da matatun man fetur ɗin ƙasar nan. Sabuwar matatar man fetur ta Ɗangote ana saran za...
    Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Ɗangote, ya ce yana da shakku a kan ko matatun mai mallakin gwamnatin Najeriya za su ƙara aiki a nan gaba. Najeriya dai na da matatun mai guda hudu mallakinta a biranen Fatakwal da Warri da Kaduna. Amma attajirin ya ce matatun man waɗanda ke ƙarƙashin kulawar Kamfanin Mai na Najeriya (NNPCL), sun laƙume sama da Dalar Amurka biliyan 18 wajen gyaransu, amma har yanzu sun ƙi aiki. Sojoji sun kashe ’yan fashin daji masu yawan gaske a Zamfara Muna so a kafa doka ta bincikar yadda ’yan Nijeriya ke tara dukiya — EFCC Ɗangote ya bayyana hakan ne ranar Alhamis lokacin da ya karɓi baƙuncin mambobin shugabannin kamfanoni wadanda ke Karatu a Lagos...
    “A wajen jahilai, tsagaggen lebe lahani ne a kan makogwaro da lebe, amma idan akwai shinge tsakanin hanci da baki, ana kiran sa da suna handa. Wani abu ne da ba a san abin da yake kawo shi ba, amma kuma ana danganta shi da abubuwa da dama kamar karancin rashin sinadarin bitamin B.” “Don haka, muna shawartar mata masu juna biyu da su mayar da hankali wajen yawan zuwa awon ciki, sannan kuma su rika shan magungunan da ake ba su na yau da kullum, ta yadda za a rage haihuwar masu dauke da wannan cuta. “Hakika wannan babban abin takaici ne a cikin al’umma, shi yasa kwararrun likitoci, ma’aikatan jinya, jami’an jin dadin al’umma da likitocin makogwaro, hanci...
    “An tsara kungiyar ne domin hada kan Arewa da magance matsalar rashin aikin yi Wanda hakan ya sanya aka tattaro manyan hafsoshin soja da suka yi ritaya, da tsaffin gwamnoni, da masu rike da sarautun gargajiya, da masu fafutukar kare hakkin jama’a, da kungiyoyin matasa, da kwararrun a fannin ci gaban kasa wadanda da yawa daga cikinsu sun nuna rashin gamsuwa da yadda ake gudanar da mulki da kuma mayar da muradun Arewa saniyar ware a ‘yan shekarun nan”   “Yankin arewa na iya shawo kan kalubalen da suke fuskanta ta hanyar hadin kai da kuma sabunta kudurin samar da ci gaba,”   Bafarawa ya kuma tabbatar da cewa ba an kafa kungiyar bace a matsayin dandalin siyasa ba, kuma...
    Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya bayyana cewa: Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ba da umarninsa ga sabbin kwamandojin da kansu a lokacin yakin baya-bayan nan Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran Muhammad Baqir Qalibaf, yayin da yake ishara da umarnin da Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayar a yakin kwanaki 12 da aka kakabawa Iran, ya ce Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya kasance a dakin kwamandoji sau biyu a lokacin yakin tare da bayar da umarninsa ga sabbin kwamandojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran. A wata hira da aka yi da shi ta gidan telebijin, Qalibaf ya kara da cewa kwamandojin da aka nada sa’o’i bayan fara kai hare-hare kan kasar Iran,...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran yayi tsokaci kan takunkumin Amurka ta kakaba kan jami’ar Majalisar Dinkin Duniya da cewa: Ba za a iya murkushe gaskiya ba Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ismail Baqa’i ya yi tsokaci kan takunkumin da Amurka ta kakaba wa wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya na musamman kan halin da ake ciki na kare hakkin bil’adama a yankunan Falasdinawa da aka mamaye, Francesca Albanese. A cikin wani rubutu a dandalin “X” a ranar Juma’a, Baqa’i ya bayyana cewa: “Ba za a iya murkushe gaskiya ba.” Wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya ta musamman kan halin da ake ciki na kare hakkin bil’adama a yankin Falasdinu,  Francesca Albanese, ta fuskanci takunkumi da girman kai saboda fallasa gaskiya da kuma tsayin...
    Mataimakin shugaban kasar na farko ya jaddada cewa: Kalmar “mika kai” ba ta da gurbi a al’adun siyasa da tsaron Iran Mataimakin shugaban kasar Iran na farko Mohammad Reza Aref ya jaddada cewa: kalmar mika wuya ba ta da gurbi a al’adun siyasa da tsaron kasar. Arif ya ce: Kamar yadda kuke gani kalmar “mika kai” ba ta da gurbi a al’adun siyasa da tsaron Jamhuriyar Musulunci ta Iran, yana mai jaddada cewa, su mutane ne masu wayewa, tare da ingantaccen tarihin al’adu wanda ya wuce dubban shekaru. Ba su neman yaki, kuma ba su fara shi ba. Sun yi imani da zaman lafiya da kwanciyar hankali, kuma a shirye suke don tattaunawa, amma ba za su mika wuya a...
      A daya bangaren kuma Fita zuwa wani yanki daban da ba naka a halin yanzu, yana da nasa fa’idar. Domin kuwa, na ziyarci wasu jihohi uku kwanan nan; wadanda labarai a kansu babu dadin ji. Jihohin su ne, Delta, Inugu da kuma Zamfara, wadanda galibi labaransu marasa dadi ne ta fuskar siyasa, ta’addanci da sauran munanan laifuka. Daga labarun da ake samu yau da kullum, za ka yi tsammanin cewa; wadannan jihohi tuni sun tashi daga aiki, amma daga ziyarar da na kai musu; na ga abubuwan ban mamaki, tsoratarwa da kuma hadari duk da ke dauke cikin wannan labari. Duk da cewa, kowace jiha akwai abubuwan da ta fi bai wa muhimmanci, su ma kamar sauran jihohin; suna...
    Albarkacin taron ministocin kasa da kasa na tattauna mu’ammalar wayewar kai ta duniya, CGTN ta hada hannu da jami’ar Renmin ta kasar Sin, domin jin ra’ayin al’ummun kasashe 41 da yawansu ya kai dubu 12. Masu bayyana ra’ayoyin na ganin cewa, mu’ammala, da cudanyar al’adu, da wayewar kai muhimmin karfi ne na ciyar da bunkasar wayewar kan daukacin bil’adama da zaman lafiyar duniya gaba, don haka ne ma darajanta al’adu da magabata suke dora muhimmanci a kanmu, da kirkire-kirkire, na da babbar ma’ana ga zamanantar da al’ummun bil’adama, wanda hakan ya sa shawarar bunkasa al’adun duniya da Xi Jinping ya gabatar, ta samu karbuwa tsakanin sassan kasashe daban-daban, yayin da suke kokarin tinkarar kalubaloli a duniya. Yayin da aka tabo...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Matasan Najeriya da dama suna son yin arziki amma ba tare da sun sha wahala ba.   Sau da yawa matasa sun fi neman hanya mafi sauki da za ta basu arziki ba tare da sun sha wahala ba. NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Sa ’Yan Najeriya Ba Sa Cin Kifi Yadda Ya Kamata DAGA LARABA: Shin Ko Zafin Nema Na Kawo Samu? Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan dalilan da suka sa wasu matasa bin yanke don tara abin duniya. Domin sauke shirin, latsa nan