HausaTv:
2025-09-17@23:21:16 GMT

Iran Ta Sami Muhimman Bayanai Na Sirri Akan Shirin Nukiliyar HKI

Published: 8th, June 2025 GMT

Tashar talabijin din ‘almayadin” ta ambato wata majiya ta Iran tana cewa; Jami’an leken asirin kasar sun sami muhimman byanai akan Shirin Nukiliyar HKI.

Majiyar ta kara da cewa; Jami’an leken asirin Iran sun iya isa ga wadannan muhimman bayanan masu yawan gaske tare da yin jigilarsu zuwa cikin kasar Iran.

Daga cikin bayanan da akwai wadanda su ka shafi shirye-shiryen da ‘yan sahayoniyar suke aiwatarwa na Nukiliya da kuma cibiyoyin Nukiliyar.

Majiyar ta kara da cewa;  jami’an leken asirin na Iran sun iya kai wa ga wadannan bayanan tun shekarun  da su ka gabata, kuma saboda yawan bayanan da kuma hanyoyin shigo da su cikin Iran ne ya sa ba a bayyana shi ba sai yanzu.

Haka nan kuma majiyar ta ce bayanan sun hada hotuna na cibiyoyin Nukiliyar HKI da kuma bidiyo da suka bukaci lokaci mai tsawo na yin nazarinsu.

Majiyar almayadin ta ce; Abu ne mai yiyuwa mutanen da HKI ta bayyana cewa ta kama su a cikin kwanakin bayan nan, suna da alaka da wadannan bayanan da su ka shiga hannun Iran.

Har ila yau, tashar talabijin din ta kuma ambaci cewa; Fitar da wannan sanarwar a wannan lokacin yana da nashi muhimmanci bisa la’akari da halin da ake ciki a wannan yankin na yammacin Asiya.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Tinubu Ya Janye Dokar Ta-baci A Jihar Rivers

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanar da janye dokar ta-baci a Jihar Rivers daga ƙarfe 12 na daren 17 ga watan Satumban 2025.

Shugaban Ƙasar, a wata sanarwa da ya sanya wa hannu, ya ce dokar ta-bacin da ta dakatar da Gwamna, Mataimakiyarsa, da ‘yan majalisar dokokin jihar na tsawon watanni shida ta cimma manufarta na dawo da zaman lafiya a jihar.

Tinubu ya bayyana cewa ya yi amfani da Sashe na 305 na Kundin Tsarin Mulkin 1999 ne a watan Maris na 2025 sakamakon durƙushewar mulki a Jihar Rivers.

A cewarsa, rashin jituwa tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da Majalisar Dokokin Jihar, da kuma lalata muhimman kadarorin gwamnati sun jefa jihar cikin rikici.

“Lamarin ya kai ga Babbar Kotun Ƙoli ta bayyana a ɗaya daga cikin hukuncinta cewa babu gwamnati a Jihar Rivers.” In ji Shugaban Ƙasa.

Ya gode wa Majalisar Ƙasa bisa amincewa da wannan sanarwa, tare da yabawa Sarakuna da jama’ar jihar bisa haɗin kan da suka bayar.

Tinubu ya kuma yaba wa  masu adawa da suka kalubalanci wannan mataki a kotu, yana cewa wannan shi ma wani ɓangare ne na dimokuraɗiyya.

Da yake magana kan sabuwar fahimta tsakanin manyan ‘yan siyasa a jihar, Shugaban Ƙasa ya ce babu dalilin ƙara tsawaita dokar ta-bacin.

Ya bayyana cewa Gwamna Siminalayi Fubara, da Mataimakiyarsa Ngozi Nma Odu, da Shugaban Majalisar Dokoki Martins Amaewhule da dukkan mambobin majalisar jihar za su koma bakin aiki daga 18 ga Satumban 2025.

Tinubu ya yi kira ga shugabannin siyasa a faɗin Najeriya da su ƙarfafa zaman lafiya da haɗin kai domin isar da fa’idodin dimokuraɗiyya ga al’umma.

 

Daga Bello Wakili

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnati ta ƙaddamar da jiragen ruwa na zamani 20 a Sakkwato
  • Microsoft ya ƙwace shafukan wasu kamfanoni 340 a Najeriya
  • Tinubu Ya Janye Dokar Ta-baci A Jihar Rivers
  • Za A Kada Kuri’ar Raba Gardama Akan Sabon Tsarin Mulki A Kasar Guinea
  • Gwamna Namadi Ya Taya Malaman Makarantu Da Suka Yi Fice A Jihar Murna
  • Tinubu bai shirya gudanar da sahihin zaɓe ba a 2027 – Buba Galadima
  • Gwamnati ta fara duba yara marasa galihu kyauta a asibitin Aminu Kano
  • Jihar Jigawa Ta Amince Da Karin Kasafin Kuɗi Na Naira Biliyan 75 Na Shekarar 2025
  • NSCDC Za Ta Fara Sanyan Ido Kan Muhimman Abubuwan More Rayuwa A Jihar Kano
  •  Dan Kasar Iran Mai Kirkira Ya Sami Kyautar Yabo A Kasar China