Sojoji sun dakile hare-haren ‘Yan Boko Haram biyu a Borno
Published: 5th, June 2025 GMT
A wani hari ta kasa da na sama, rundunar sojojin Operation Hadin Kai sun dakile wasu manyan hare-haren ta’addanci guda biyu a ranar Alhamis a Jihar Borno.
Dakarun sun kashe da dama daga cikin maharan tare da kwato tarin makamai da alburusai.
Wani mutum ya mutu a cikin rijiya a Kano Mahajjata kusan miliyan biyu na hawan Arfa a SaudiyyaRahoton da hukumar tsaron sojan Najeriya suka fitar na nuna cewar, dakarun sojan rundunar ta OPHK an kaddamar da hare-haren ne a wasu wurare daban-daban na sojoji a Buratai da ke karamar hukumar Biu da kuma Mallam Fatori da ke karamar hukumar Abadam.
An bayyana cikakkun bayanan hare-haren a cikin wata sanarwa da Mukaddashin mataimakin daraktan hulda da jama’a na rundunar soji na hedikwatar Operation Hadin Kai, Kyaftin Reuben Kovangiya ya fitar ranar Alhamis, 5 ga Yuni, 2025.
Sanarwar ta ce, lamarin na farko ya faru ne da sanyin safiyar Alhamis a garin Buratai, inda ‘yan ta’addan suka yi yunkurin kutsawa inda dakarun suke daga wurare da dama.
“Sojojin, duk da haka, cikin hanzari sun yi artabu da ‘yan ta’addan da manyan bindigogi, yayin da dakarun sama da manya-manyan Jiragen yakin Tucano suka ba da tallafi ta sama ga sojojin.”
Kyaftin Kovangiya ya bayyana daga bayan an gano gawarwakin ‘yan Boko Haram dama, tare da tarin makamai da alburusai iri-iri.
Hakazalika, sojojin a Mallam Fatori sun dakile wani harin da ‘yan tada kayar bayan suka tunkaro inda suke daga bangarori daban-dabam.
Sanarwar ta kara da cewa, “Sojojin sun yi wa ‘yan Boko Haram mummunan barna lamarin da ya sa su tserewa cikin rudani.”
Bayan da ‘yan tada kayar bayan da suka ja da baya ya kai ga kashe mutane da dama, yayin da wasu suka tsere da raunukan harbin bindiga.
Abubuwan da aka kwato daga hannunsu a Mallam Fatori sun hada da: bindigogi kirar AK-47 da yawa, manyan bindigogi masu linzami (GPMGs), bindigogin roka (RPGs), da sauran kayan aikinsu na ta’addanci.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Boko Haram hare hare Operation Hadin Kai
এছাড়াও পড়ুন:
Jihar Kwara Ta Jaddada Kudirin Tallafa wa Wadanda Suka Tsira Daga Cin Zarafin Jinsi
Gwamnatin Jihar Kwara ta jaddada kudirinta na ba da ingantaccen kulawa da kuma ƙarfafa matakan rigakafi ga waɗanda suka tsira daga cin zarafin jima’i da na jinsi (SGBV) a fadin jihar.
Kwamishiniyar Harkokin Mata, Hajiya Opeyemi Afolashade, ce ta bayyana haka yayin ziyarar sa ido da tantance ayyuka a Cibiyoyin Tallafawa Wadanda Aka Yi wa Cin Zarafi (SARCs) da ke Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Kwara (KWASU) a Ilorin da kuma Asibitin Kwarari ta Sobi da ke Alagbado.
Kwamishiniyar ta bayyana cewa cibiyar an kafa ne tare da hadin gwiwar ofishin Uwargidar Gwamna, domin jinya kyauta da kuma kwantar da hankali, da tallafi ga wadanda suka tsira daga cin zarafi a jihar.
Afolashade ta ƙara da cewa bincike da tantancewar da ake yi yanzu zai taimaka wajen tantance ingancin kulawar da ake bayarwa, da gano wuraren da ake bukatar gyara domin samar da tsarin taimako mai inganci da niyya kai tsaye ga masu bukata.
Ta kuma jaddada bukatar ƙara haɗin gwiwa da masu ruwa da tsaki tare da horar da ma’aikatan cibiyoyin SARC a fannin tattara bayanai da bayar da rahoto domin inganta tsarin tallafi ga wadanda suka tsira daga cin zarafin jinsi.
Ali Muhammad Rabiu/Ilorin