Kungiyar Bada Agaji Ta ‘Red Cross” Ta Ce Ta Fice Daga Jumhuriyar Nijer
Published: 7th, June 2025 GMT
vvddxfKungiyar bada agaji ta Red Cross ta nbada sanarwan cewa ta rufe ofishinta a Nijer kuma ta fidda dukkan ma’aikatanta na kasashen waje daga kasar.
Ta kuma kara da cewa, gwamnatin kasar ta bukacin kungiyar ta fice daga Nijer tun watanni 4 da suka gabata, amma bata yi hakan bas ai yanzu.
ICRC ta tabbatar da hakan a ranar Alhamis da ta gabata Sannan Patric Yousuf daraktan kungiyar a Nahiyar Afirka ya bayyana cewa sun janye ma’aikatansu a Nijer sannan suna tattaunawa da gwamnatin kasar don sake dawowa kasar da kuma ci gaba da ayyukansu na bada agaji.
A cikin watan Fabrayrun wannan shekara ne ministan harkokin wajen kasar ya bada wannan umrnin ba tare da bayyana dalilan yin haka ba.
Kungiyar ta bada sanarwan cewa tun watan Fabrairun wannan shekara ne suke bin jami’an gwamnatin sojojin kasar domm samun takamemmen dalilin da yaaa sa suka dauki wannan matakin amma daga karshe sun fice daga kasar bayan sojojin sun dage a kan rufe ofishin kungiyar
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Ta Yi Kira Ga “FIFA” Da Ta Kori “Isra’ila” Daga Cikinta
Kungiyar kwallon kafa ta Iran ta aike da sako zuwa ga hukumar kwallon kafa ta duniya da ta kori HKI daga cikinta
Shugaban kungiyar kwallon kafa ta Iran Mahdi Taj, ya bayyana cewa: Mun yi kira ga Sheikh Salman akan daukar kwakkwaran mataki akan ‘Yan Sahayoniya. Mun kuma rubuta wasika zuwa ga Fifa akan cewa ya zama wajibi a dagawa HKI jan kati.
Bugu da kari, ya kuma ce; “Yan sahayoniya sun kai wa hukumar kwallon kafa ta Iran hari, ta kuma kashe mana alkalai, ‘yan wasa, don haka ya zama wajibi a kore su daga Fifa.
Taj ya kuma ce; Mun sami ci gaba sosai a wannan fagen, muna fatan kungiyar Fifa ta yi la’akari da wadannan laifukan na Isra’ila.