A shekara 25, na kashe tiriliyan 161 wajen inganta lafiya a Afirka – Bill Gates
Published: 5th, June 2025 GMT
Attajirin nan na duniya dan asalin kasar Amurka, Bill Gates, ya ce a shekara 25 da gidauniyarsa ta yi da kafuwa, ya kashe Dalar Amurka biliyan 100, kwatankwacin Naira tiriliyan 161 wajen inganta kiwon lafiya a nahiyar Afirka.
Attajirin ya bayyana hakan ne a Legas yayin wani taro da gidauniyarsa ta Gates Foundation ta shirya mai taken Goalkeepers, ranar Laraba.
Ya ce gidauniyar ta fara aiki ne a shekara ta 2000, kuma babban makasudinta shi ne ganin an rage samun mace-macen kananan yara a fadin duniya, musamman a Afirka.
Kotu ta aike da ɗan Tiktok gidan yari kan yin shigar mata a Kano NAJERIYA A YAU: Yadda Mayar Da Unguwa Mayanka Ke Shafar Lafiyar Al’ummaBill Gates ya ce, “Ganin haka ne ya sa na yi nazari na ce shin mutane suna mayar da hankalinsu wajen ganin an samar wa da wasu ba’arin mutane magungunan da yankunansu ke bukata, alal misali a bangaren zazzabin cizon sauro (maleriya), sai na gano babu.
“Wannan ne ya kasance alkiblar gidauniyar Gates Foundation. Sama da kaso 70 cikin 100 na abin da nake kashewa, Dala biliyan 100, a bangaren lafiya na duniya suka tafi, kuma a tsawon wadannan shekaru 25, mun inganta alakarmu da kasashen Afirka da dama.
“A nan Najeriya muna da abokan hulda masu dadin mu’amala da suka fahimci hanyoyin da za mu bi wajen taimaka wa gwamnati,” in ji shi.
Ya kuma ce inganta harkar lafiya kan taimaka wa kasa wajen samun ci gaban tattalin arziki ta yadda za ta iya dogaro da kanta.
Mamallakin kamfanin Microsoft din ya kuma bayyana kyakkyawan fatan cewa za a samu raguwar yawan mace-macen kananan yara da kaso 50 cikin 100 daga adadin yara miliyan biyar din da yanzu haka ake samu a fadin duniya.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Amurka na iya kashe jagoran addini na Iran don mun san inda yake — Trump
Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa ya san inda jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei yake “boye”, kuma ya yi gargadi cewa Washington na iya halaka shi, amma za su dakata a halin yanzu.
Wannan na zuwa ne yayin da Trump din ya gargadi Iran kan da kada ta kai harin makamai masu linzami kan fararen hula ko kuma sojojin Amurka, yana mai cewa hakurinsu na karewa.
Iran ta kai hari hedikwatar hukumar leƙen asirin Isra’ila Rikicin ƙabilanci ya yi ajalin mutum 20 a ChadiA wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Truth mintuna kadan bayan wannan sako, Trump ya rubuta cewar Iran din ta mika wuya ba tare da wani sharadi ba kawai.
Rahotanni a bayan nan sun ce Trump ya ƙi amincewa da shirin Isra’ila na kashe jagoran Iran, Ayatollah Ali Khamenei, kamar yadda majiyoyi uku suka shaida wa kafar yaɗa labarai ta CBS News.
Bayanan sun ce Shugaba Trump ya shaida wa Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu cewa kashe Khamenie “ba shawara ce mai kyau ba.”
Tattaunawar ta faru ne bayan harin da Isra’ila ta ƙaddamar kan Iran a ranar Juma’a.
A lokacin wata tattaunawa da kafar yaɗa labarai ta Fox News, Netanyahu bai fayyace kai-tsaye ko Trump ya ƙi amincewa da shawarar kashe Ayatollah ba, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.
“Akwai rahotannin da dama kan tattaunawar da ake cewa an yi amma kuma ba gaskiya ba ne, ba zan shiga cikin irin wannan maganar ba,” in ji Firaiminstan Isra’ila.
Tun tsawon kwanaki biyar, Isra’ila ke kai hare-hare a cikin Iran, da suka shafi wuraren nukiliya da manyan kwamandojin soji da masana kimiyya da cibiyoyin tsaro da birane da ma cibiyoyin mai da iskar gas.
Iran dai ta mayar da martani da makamai masu linzami gami da jirage masu sarrafa kansu a kan Isra’ila, lamarin da ke kara fargabar cewa Amurka za ta iya shiga cikin rikicin kai tsaye, wanda kuma zai iya haifar da sabon babi mai hadari a rikicin.
A gefe guda kuma, babban hafsan tsaron Iran ya yi gargadi ga mazauna Isra’ila “musamman ma na biranen Tel Aviv da Haifa da su gaggauta barin wurarensu don tsira da rayukansu.
Janar Abdolrahim Mousavi, ya ce ayyukan da aka gudanar zuwa yanzu sun kasance gargadi ne kan abin da ke tafe, kuma za a gudanar da wani aiki na ladabtarwa nan ba da jimawa ba daga Iran.
Koda yake hare-haren Iran sun kashe akalla Isra’ilawa 24 tun a ranar Juma’a, galibin makaman Iran din dai Isra’ila ta dakatar da su ta hanyar tsarin kariyarta ta sama.