Mutum 9 sun rasu a hatsarin mota a Jigawa
Published: 8th, June 2025 GMT
Aƙalla mutum tara ne suka rasu a wani mummunan hatsarin mota da ya auku a ƙauyen Kyaramma da ke Ƙaramar Hukumar Ringim ta Jihar Jigawa.
Rundunar ’yan sandan jihar, ta ce hatsarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2 na ranar Asabar, inda motoci biyu ƙirar Golf 3 suka yi taho-mu-gama, kuma mutane da dama sun jikkata.
Ɗaya daga cikin motocin, mai lambar Kaduna MKA 687 AY, ana ɗauke da ita ne daga Abuja zuwa garin Gujungu, kuma direban motar mai suna Adamu Sunusi, mai shekaru 35 daga Ƙaramar Hukumar Hadeja.
Rahoton ’yan sanda ya nuna cewa hatsarin ya faru ne bayan ɗaya daga cikin direbobin motarsa ta ƙwace masa, wanda hakan ya sa motocin biyu suka yi karo da juna.
’Yan sanda sun isa wajen, kuma sun garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa Asibitin Gwamnati na Ringim domin kula da su.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP A.T. Abdullahi, ya jajanta wa iyalan waɗanda suka rasu, sannan ya yi addu’ar samun sauƙi ga waɗanda suka jikkata.
Ya kuma shawarci direbobi da su riƙa bin dokokin hanya, su guji gudu fiye da ƙima, tare da tabbatar da cewa motocinsu na cikin ƙoshin lafiya kafin su hau hanya.
Ya bayyana cewa mutum 11 da suka jikkata suna asibiti inda ake kula da su, kuma suna samun sauƙi.
Yanzu haka ana ci gaba da gano sunayen waɗanda lamarin ya shafa da kuma sanar da iyalansu.
’Yan sanda sun ce za su ci gaba da fitar da bayanai yayin da bincike ke gudana.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Sanda hatsarin mota Jigawa
এছাড়াও পড়ুন:
Tsoffin Jami’an ‘Yan Sanda Sun Bukaci A fitar Da Su Daga Cikin Shirin Fansho
Jami’an ‘yan sanda da suka yi ritaya a jihar Kwara sun gudanar da zanga-zangar lumana don neman a cire su daga shirin bayar da gudunmawar fansho (CPS).
An ga jami’an ‘yan sandan da suka yi ritaya a jihar karkashin kungiyar ‘yan sandan Najeriya mai ritaya (ARPON), dauke da kwalaye masu rubuce-rubuce daban-daban kamar su “Shugaban kasa, NASS da IGP ya kamata a girmama ‘yan sanda su kebe ‘yan sanda daga CPS, su kafa hukumar ‘yan sanda ta fensho don gudanar da gratuity da fansho, idan CPS na da kyau haka, me ya sa AIGs da sauran su suka fice daga cikin shirin?
Da yake jawabi ga ‘ya’yan kungiyar a lokacin zanga-zangar lumana a Ilorin, shugaban kungiyar, Yakubu Jimoh, babban Sufeton ‘yan sanda mai ritaya, ya yi zargin cewa shirin yana cike da kalubale tun farkonsa.
A cewarsa jami’an da suka yi ritaya wadanda suka fada cikin tsarin fansho ya kamata a kebe su kamar wadanda suka kai matsayin Janar a rundunar.
Ya nemi kafa hukumar fansho ta ‘yan sanda mai alhakin kula da al’amuran ‘yan sanda na fansho kamar yadda ya shafi sauran hukumomin tsaro.
Jimoh ya bayyana cewa rahoton kwamitin majalisar dattijai mai kula da kafa da ayyukan gwamnati a kan kudirin dokar kafa hukumar fansho ta ‘yan sanda, wadda aka gudanar a watan Nuwambar bara ta fitar da shi, duk da cewa an gudanar da shi watanni takwas da suka gabata.
Ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da majalisar dokokin kasar da su gaggauta bin diddigin yadda majalisar za ta bi wajen fitar da naira biliyan 758, karancin kudaden fansho da ke bin hukumomin tsaro.
A nasa bangaren, mashawarcin shari’a na kungiyar ‘yan sandan Najeriya mai ritaya Adekunle Iwalaiye, ya ce jami’an da suka yi ritaya sun cancanci a biya su fansho na rayuwa ba wai dan abin da ake jefa musu ba duk wata ba.
Ya bukaci gwamnati da ta yi aiki da bukatar wadanda suka yi ritaya, duba da irin ayyukan alheri da suka yi wa kasar nan tsawon shekaru 35.
COV/ALI MUHAMMAD RABIU