Ministan ya bayyana gabatarwar da C-WINS ta yi a matsayin mai motsa zuciya kuma mai cike da ƙarin haske.

Ya ce: “A yau na koyi abubuwa da dama. Yawancin ’yan Nijeriya, kamar ni kai na, sun san cutar masassarar cizon sauro amma ba su san da ƙyandar jamus da mummunan tasirin ta ba.

“Gaskiya batun cewa za a iya haihuwar yara makafi, kurame ko kuma masu nakasar zuciya sakamakon kamuwa da ƙyanda daga uwa a lokacin ɗaukar ciki babbar masifa ce da ya kamata mu haɗa kai mu daƙile ta.

Ya ƙara da cewa ma’aikatar za ta haɗa hannu da sauran hukumomin da suka dace wajen tsara saƙonnin faɗakarwa da shirye-shiryen ilimantar da al’umma.

Ya kuma shawarci tawagar da su nemi haɗin kan Majalisar Tarayya domin samun cikakken goyon baya na doka.

Ya ce: “Ba ma so wannan zama ya tsaya nan kawai. Mu mayar da wannan haɗin gwiwa abin da zai ɗore, mai amfani, kuma mai faɗi da tasiri. Rigakafi ya fi magani — kuma wannan fannin ne inda bayani ke ceton rayuka ainun.”

A cikin nata jawabin, jagorar tawagar C-WINS, Dakta Nihinlola Mabogunje, ta jaddada gaggawar wayar da kan jama’a kafin lokacin fara kamfen ɗin.

Ta gabatar da cikakken bayani kan muhimmancin rigakafin daga cututtukan ƙyandar jamus fata, musamman a matsayin da Nijeriya ke da shi wajen yawaitar waɗannan cututtuka.

Dakta Mabogunje ta bayyana cewa Nijeriya tana da kusan kashi 20 cikin ɗari na dukkan cututtukan ƙyandar da ake samu a duniya, inda yankin Arewa-maso-gabas yake ɗauke da fiye da kashi 60 cikin ɗari na waɗanda abin ya shafa a ƙasar nan.

Dangane da ƙyandar jamus, ta bayyana cewa cutar tana barazana musamman ga mata masu juna biyu, domin kamuwa da cutar a watannin farko na ɗaukar ciki yana iya janyo haihuwar jarirai masu nakasa kamar makanta, kurmancewa ko lalacewar zuciya.

Ta tabbatar da cewa rigakafin da za a yi amfani da shi yana da inganci kuma ba shi da wani haɗari ga lafiyar mutum, tana mai cewa tun tuni ake amfani da shi, fiye da shekaru 50 a duniya, kuma ya ceci rayuka sama da miliyan 94.

Ta kuma yaba da aikin Hukumar NAFDAC wajen tantancewa da amincewa da rigakafin domin amfani da shi a Nijeriya.

Ta roƙi Gwamnatin Tarayya da ta jagoranci faɗakarwar a matakin ƙasa domin kawar da ji-ta-ji-ta da ƙarfafa gwiwar jama’a.

Likita Mabogunje ta ce: “Don cimma burin kashi 95 na yawan masu karɓar rigakafi, muna buƙatar saƙonnin da suka dace, masu sahihanci da kuma daidaito, waɗanda za a isar ta hanyoyin da ’yan Nijeriya suke yawan dogaro da su a kullum.”

A martanin sa, Minista Idris ya umurci jami’an sashen sadarwa na ma’aikatar sa da su yi aiki tare da C-WINS domin ƙirƙirar kayan faɗakarwa da suka dace da al’adun jama’a, waɗanda za a yaɗa ta kafafen watsa labarai na gwamnati da masu zaman kan su a dukkan faɗin ƙasar nan.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

DSS ta maka Sowore da Facebook a Kotu kan cin zarafin Tinubu

Hukumar Tsaron Farin Kaya a Nijeriya DSS, ta gurfanar da fitaccen ɗan gwagwarmayar nan, Omoyele Sowore a kotu.

A ƙunshin ƙarar da DSS ta gabatar a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta haɗa da shafukan sada zumunta na X da kuma Facebook, inda take zarginsu da ba da ƙofar aibata Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Bida Poly ta sa sojoji kula da jarrabawar ɗalibai Kukan al’umma kan lalacewar hanyar Dukku

Darekan shigar da ƙara na Ma’aikatar Shari’a ta Tarayya, M.B Abubakar da wasu lauyoyi huɗu —M.E. Ernest da U.B. Bulla da C.S. Eze da kuma E.G. Orubor, ne suka shigar da ƙarar a madadin Gwamnatin Tarayya da kuma hukumar ta DSS.

DSS wadda ta kafa hujja da sashe na 24 da ke cikin kundin dokokin yanar gizo, ta ce Sowore ya yi amfani da shafukansa na dandalan sada zumunta na X da Facebook wajen wallafa wani saƙo da ke cin mutuncin Shugaba Tinubu.

Tun dai a farkon watan nan ne DSS ta buƙaci goge wani saƙo da ɗan gwagwarmayar ya wallafa wanda ta riƙa a matsayin bayanan ƙarya, cin zarafi ta yanar gizo da kalaman haddasa ƙiyayya, waɗanda kuma ta ce na iya haddasa rikici su kuma ɓata sunan Najeriya a ƙasashen waje.

Sai dai har zuwa ranar Litinin, 15 ga watan Satumba, babu wani mataki da aka ɗauka na goge saƙon da DSS ɗin ta buƙata.

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnatin Tarayya Ta Dawo Da Karatun Tarihi A Makarantu
  • Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Sabon Tsarin Kula Da Lafiyar Mata Masu Juna Biyu Da Kananan Yara
  • Gwamna Namadi Ya Taya Malaman Makarantu Da Suka Yi Fice A Jihar Murna
  • Gwamnatin Kano Ta Inganta Cibiyoyin Horas Da Sana’o’i Domin Dakile Aikata Laifuka Tsakanin Matasa
  • Saudiyya Ta Saki ‘Yan Nijeriya 3 Da Aka Yi Wa Sharrin Safarar Ƙwayoyi
  • Saudiyya Ta Saki ‘Yan Nijeriya 3 Da Ta Kama Bisa Kuskuren Safarar Ƙwayoyi
  • Najeriya Na Asarar Dala Biliyan 10 Bayan Girbi Duk Shekara- Gwamnatin Tarayya
  • DSS ta maka Sowore da Facebook a Kotu kan cin zarafin Tinubu
  • Ɗan Majalisar Tarayya Ya Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-haren Ta’addanci A Sakkwato 
  • An kama tsohon minista kan zargin kisan kai domin tsafi a Nijar