2027: Wasu Gwamnonin PDP Na Shan Matsin Lamba Don Sauya Sheka Zuwa APC
Published: 7th, June 2025 GMT
Wasu sahihin rahotannin daga cikin gwamnatin sun shaida cewa Gwamna Eno ba zai iya sauya sheka zuwa APC ba tare da amincewar Emmanuel ba, domin yin hakan na iya jawo masa asarar goyon bayan mambobin majalisun kasa da na jihar, ciki har da sauran muhimman masu ruwa da tsaki na jam’iyyar.
An kuma tattaro cewa wani bangare na shirin fadar shugaban kasa shi ne, dukkan jihohin Kudu Maso Gabas su kasance na APC.
A Jihar Jihar Zamfara kuwa, an gano cewa fadar shugaban kasa ta nuna sha’awarta na shigo da gwamnan cikin jam’iyyar APC. Duk da haka, daya daga cikin matsalolin shi ne, akwai wadanda ba sa son lamarin ya tabbata kamar karamin ministan tsaro, Bello Matawlale.
A cikin wata tattaunawa da aka yi da shi a ‘yan kwanakin nan kan shirin komawa APC, Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ce a halin yanzu yana nan a cikin PDP.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Mokwa: Zulum ya kai ziyarar jaje Neja, ya bayar da tallafin N300m
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya kai ziyara Jihar Neja domin jajanta wa mutanen Mokwa da iftila’in ambaliyar ruwa ya shafa.
Zulum ya kuma bayar da tallafin Naira miliyan 300 domin taimaka wa waɗanda iftila’in ya shafa.
Ana zargin uwa da kashe ’yarta kan Naira 100 a Zariya Majalisar Dokokin Kuros Riba ta dakatar da shugabar ƙaramar hukuma na wata 3Zulum, ya ce Gwamnatin Borno ta kawo wannan taimako ne don tallafabwa gwamnatin Neja wajen rage raɗaɗin ambaliyar da ta kashe mutane da lalata dukiyoyi.
Ya kuma buƙaci sauran gwamnatocin jihohi da ƙananan hukumomi su haɗa kai don kare al’umma daga iftila’i da sauyin yanayi ke haddasawa.
Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya nuna godiya bisa wannan ziyara da tallafi.
Ya ce ya yi matuƙar farin ciki da irin wannan kulawa da ƙauna da Gwamnatin Borno ta nuna wa al’ummarsa.
Bago, ya tabbatar da cewa za a yi amfani da tallafin cikin gaskiya da adalci, tare da ci gaba da faɗakar da jama’a su guji gina gidaje a kusa da bakin kogi.
Zulum, ya samu rakiyar Sanata Mohammed Tahir Monguno, wasu ‘yan Majalisar Wakilai, Injiniya Bukar Talba, Hon. Abduljadir Rahis da mataimakin kakakin Majalisar Dokokin Jihar Borno, Injiniya Abdullahi Askira.