‘Yansanda A Kano Sun Gargadi Sarki Sanusi Kan Yekuwar Fitowa Hawan Sallah
Published: 4th, June 2025 GMT
“Saboda haka, rundunar ‘yansandan ta nanata cewa, dokar hana duk wani nau’in hawan Sallah a jihar yana nan, zai ci gaba da wanzuwa har zuwa lokacin bukukuwan Sallar Layya ta bana ta 2025 da ake shirin yi domin har yanzu, akwai barazanar tsaro mai karfi a jihar.
“An yanke wannan shawarar ne bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki a harkar tsaro biyo bayan rahotannin sirri da ke nuni da shirin wasu bata gari da masu daukar nauyinsu na yin amfani da bukukuwan hawan Sallah wajen gurgunta tsaro da zaman lafiya a jihar, kamar yadda aka tabbatar a lokacin Sallar Azumi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Iran: Sojojin Ruwan Iran Sun Kori Jirigin Yakin Amurka Daga Tekun Oman
Sojojin ruwan Iran sun sanar da cewa, wani jirgin ruwan Amurka na yaki da ya yi kokarin shiga tekun Oman, ya fuskanci gargadi daga sojojin ruwan Iran tare da tilasta masa janyewa.
Da saiyar yau Laraba ne dai jirgin sama mai saukar angulu mallakin sojojin ruwa, ya yi gargadi ga jirgin ruwan na Amurka da a karshe ya tilasta masa janyewa.
Da fari, jirgin ruwan yakin na Amurka ya yi wa jirgin sama mai saukar angulu na Iran barazanar kai masa hari, said ai duk da haka sojojin ruwan na Iran sun ci gaba da yin gargadi ga Amurkawan da su kar su shiga cikin ruwan tekun Oman.
Bayan wannan barazana ne aka aikewa jirgin ruwan Amurkan sako daga dakarun tsaron sararyin samaniyar Iran akan cewa, wannan jirin mai saukar angulu yana da cikakkiyar kariya, don haka wajibi ne ga jirgin ruwan na Amurka mai suna “DDG Fitzgerald ya janye.