Trump ya haramtawa ‘yan kasashen duniya 12 shiga Amurka
Published: 5th, June 2025 GMT
Shugaba Donald Trump na Amurka ya haramtawa kasashen duniya 12 shiga Amurka a wani mataki da ya ce na kare kasar ne daga “yan ta’adda na kasashen waje.
Wata takarda da fadar White House ta fitar a ranar Laraba ta ce haramcin, wanda zai fara aiki daga ranar 9 ga watan Yuni, ya shafi kasashen Afghanistan, Burma, Chadi, Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, Equatorial Guinea, Eritrea, Haiti, Iran, Libya, Somalia, Sudan, da kuma Yemen.
Baya ga hakan akwai wasu kasashe bakwai su ma da aka gindawa wasu sharudda da suka hada da Burundi, Cuba, Laos, Saliyo, Togo, Turkmenistan da kuma Venezuela.
A cewar Amurka matakin bai shafi mutanen da balaguron su zuwa kasar ke da amfani ga muradun kasar ba.”
Haka ma ‘Yan wasan kwallon kafa da za su fafata a gasar cin kofin duniya ta 2026, da za a gudanar a Amurka, Mexico da Canada, da kuma ‘yan wasa a gasar Olympics ta Los Angeles ta 2028, takunkumin ba zai shafe su ba.
Matakin dai na da nasaba ne da harin da aka kai a Colorado, in ji Donald Trump.
A ranar Lahadi, data gabata ce, wani mutum ya jefa abubuwa masu tayar da wuta a kan mahalarta tattakin mako-mako a jihar Colorado na nuna goyon baya ga ‘yan Isra’ila da ake garkuwa da su a zirin Gaza.
A cewar fadar White House, wanda ake zargi da kai harin ya shiga a Amurka ne “ba bisa ka’ida ba.”
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Har Kullum Burin Sin Shi Ne Wanzar Da Daidaito Da Cimma Moriya Tare Da Amurka
Har kullum, Sin za ta ci gaba da martaba ka’idojin kare hakkokin kamfanoninta. Duba da cewa manhajar TikTok ta shafe tsawon shekaru tana aiki a Amurka, ta kuma samar da dumbin ayyukan yi ga tarin Amurkawa, tare da bayar da gudummawa ga tattalin arzikin kasar, ya kamata gwamnatin kasar ta baiwa manhajar damar cin gajiya daidai da sauran makamantanta dake kasar. Kamar dai ko da yaushe, burin Sin shi ne wanzar da daidaito da cimma moriyar bai daya tare da Amurka.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp