Iran ta bukaci hadin kan al’ummar Lebanon wajen warware matsalolin kasar
Published: 4th, June 2025 GMT
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya bukaci hadin kan al’ummar kasar Lebanon wajen warware matsalolin kasar, yana mai kira da a yi shawarwarin kasa tsakanin dukkanin kungiyoyin siyasa domin cimma matsaya daya.
Araghchi ya bayyana haka ne a wata ganawa da ya yi a ranar Talata, da shugaban kasar Labanon, Joseph Aoun a birnin Beirut.
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya jaddada aniyar kasarsa na bunkasa alakarta da kasar Lebanon, bisa mutunta juna.
Ya kuma sanar da cewa, kamfanonin Iran a shirye suke su marawa gwamnatin Lebanon baya a kokarinta na sake gina kasar.
A nasa bangaren shugaba Aoun ya jaddada tsarin gwamnatinsa na bunkasa alaka da dukkan kasashen duniya tare da tabbatar da aniyar kasar Lebanon na kara dankon zumuncin da ke tsakaninta da Iran a fannoni daban daban.
Ya jaddada cewa kawo karshen mamayar wasu sassan kasar Lebanon da kuma gyara barnar da gwamnatin Isra’ila ta yi, su ne manyan abubuwan da sabuwar gwamnatin ta Labanon ta sa a gaba.
Araghchi ya kuma gana da firaministan kasar Lebanon Nawaf Salam, A yayin wannan ganawar, sun yi musayar ra’ayi kan bunkasuwar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, da kuma ci gaban yankin.
Araghchi ya bayyana ziyarar tasa a matsayin wani bangare na manufofin gwamnatin Iran na karfafa alaka da kasashe makwabta da na shiyya, ciki har da Lebanon.
Kafin hakan dama ya ziyarci kasar Masar, a ci gaba da wannan manufa.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kasar Lebanon Araghchi ya
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu Ba Zai Taɓa Tauye ’Yancin Kafafen Yaɗa Labarai Ba, In ji Ministan Yaɗa Labarai
Ya ƙara da cewa, “Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ba zai taɓa, a kowace hanya ko salo, tauye ko hana ci gaban aikace-aikacen kafafen yaɗa labarai a wannan ƙasa ba. Amma dole ne mu duka ‘yan jarida da masu aikin yaɗa labarai mu haɗa kai, mu bi wannan hanya mai sarƙaƙiya, mu tabbatar da cewa al’umma tana ci gaba da zama cikin haɗin kai, yayin da muke riƙe shugabanni da gwamnati da alhakin aikin su.”
Idris ya jaddada muhimmancin kafafen yaɗa labarai wajen kula da tsarin dimokiraɗiyya, inda ya shawarci ’yan jarida da su kula da rawar da suke takawa domin kada su zama abin da zai jawo ruɗani ko rikici a cikin al’umma.
“A yayin da kuke yin wannan aiki, kuna da babban nauyi na riƙe gwamnati da shugabanni da alhakin aikin su. Amma ko da kuna yin hakan, dole ne ku sani cewa saboda matsayin ku na musamman da rawar da kuke takawa, za ku iya taimaka wa ƙasa matuƙa, amma idan ba a yi taka-tsantsan ba, ayyukan ku na iya cutar da al’umma,” inji shi.
Ya bayyana buƙatar sanin ya kamata da hankali wajen tantance sahihin bayani daga wanda zai iya ɓata zaman lafiya ko raba kan al’umma.
Ministan ya ce duk da ƙalubalen da ke fuskantar fannin yaɗa labarai, akwai haske a gaba domin kafafen sun ci gaba da nuna jajircewa da ɗorewa.
Ya kuma bayyana cewa ba shi ba ne Shugaban kamfanin jaridar Blueprint ba tun bayan da aka naɗa shi Minista.
“Ba ni ne shugaban jaridar Blueprint ba yanzu. Ni ma baƙo ne aka gayyata zuwa wannan taro. Na san cewa a baya ni ne ke gaba wajen shirya wannan taron na Blueprint, musamman tun lokacin da aka kafa ta shekaru 14 da suka wuce. Dole ne in gode wa waɗanda aka gayyata su haɗu da ni a watan Mayun 2005 domin tunanin fara jaridar Blueprint: Malam Ibrahim Sheme; Manajan Darakta, Malam Salisu Umar; Shugabar Kwamitin Tace Labarai, Hajiya Zainab Okino, da dukkan ma’aikatan jaridar Blueprint.
“Na gode da cigaba da tafiyar da abin da muka faro cikin nasara. Na shekara guda ban ziyarci ofishin ba, amma ina ganin lokaci ya yi da zan yi hakan. Ina so in ga ko har yanzu kuna ci gaba da tafiyar da abin da muka faro. Ina alfahari kuma ina farin ciki da cewa abin da muka fara ya ci gaba da bunƙasa,” inji shi.
Idris ya taya waɗanda suka samu kyaututtuka murna, inda ya bayyana cewa ba a yi masu kyautar bisa wani son zuciya ko tasiri daga wani waje ba, sai hukuncin jaridar ne kaɗai.
Cikin manyan baƙin da suka halarci taron akwai Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume; Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin; Ministan Ma’adanai, Dakta Dele Alake; Ministan Raya Noman Dabbobi, Idi Mukhtar Maiha; Etsu Nupe, Mai Martaba Alhaji Yahaya Abubakar, da babban baƙon jawabi na taron, Farfesa Attahiru Jega.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp