Kasa ta danne almajirai 11 sun mutu a Kaduna
Published: 4th, June 2025 GMT
Wasu almajirai su 11 sun rasa rayukansu bayan kasa ta danne su a kauyen ’Yardoka da ke karamar hukumar Kubau ta jihar Kaduna.
Bayanai sun nuna almajiran sun rasu ne lokacin da suke tsaka da hakar kasa domin taya malaminsu buga bulon kasa da zai yi gini da shi.
Lamarin ya faru ne wajen misalign karfe 1:45 na ranar Litinin.
Almajiran dai da aka bayyana rasuwar tasu sun hada da Muntari Abdulkadir da Aliyu Abba da Ali Umar da Mubarak Haruna da Usain Isa da Yusuf Shafiu da Mujitafa Jibril da Yusha’u Saidu da Aliyu Abdu da Hamisu Mohammed da kuma Ali Abdulmumini, dukkansu ’yan shekaru 10 zuwa 15 ne.
Wasu daga cikinsu dai ’yan garin da lamarin ya faru ne, yayin da wasu daga ciki suka fito daga makwabtan garin a yankin Damau.
Kazalika, an samu nasarar ceto wasu mutum bakwai da raunuka a jikinsu, inda aka garzaya da su asibitin garin inda yanzu haka suke can suna samun kulawar ma’aikatan lafiya.
Rundunar ’Yan Sanda ta jihar Kaduna ta tabbatar da faruwar lamarin ta bakin kakakinta a jihar, DSP Mansir Hassan.
Kakakin ya ce jim kadan da samun rahoton faruwar lamarin ne suka aike da jami’ansu wajen bayan sun samu kiran gaggawa.
Ya kuma ce tuni suka kaddamar da bincike domin gano musabbabin faruwar lamarin.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Almajirai
এছাড়াও পড়ুন:
Xi: A Shirye Sin Take Ta Hada Hannu Da Canada Wajen Mayar Da Dangantakarsu Bisa Turbar Da Ta Dace
Yayin ganawarsa da firaministan Thailand, Shugaba Xi Jinping ya ce a shirye kasarsa take ta karfafa hadin gwiwa da Thailand kan dabarun samun ci gaba, tare kuma da gabatar da gogewarta na samun ci gaba a sabon zamani, kuma ya yi kira da a gaggauta gina layin dogo tsakanin Sin da Thailand da bunkasa hadin gwiwa a bangaren cinikin amfanin gona da tattalin arziki mai kiyaye muhalli da kuma kirkire kirkiren fasaha. (Mai fassara: FMM)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA