Ruwanda ta sanar da janyewa daga kungiyar CEEAC
Published: 8th, June 2025 GMT
Gwamnatin kasar Ruwanda ta sanar da janyewa daga kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen tsakiyar nahiyar Afirka wato CEEAC, bayan ta zargi jamhuriyyar demokuradiyyar Congo da hada kai da wasu kasashe membobin kungiyar, wajen amfani da kungiyar don neman cimma bukatunsu.
Cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin waje da hadin gwiwar kasa da kasa ta kasar Ruwanda ta fitar, an ce, a gun taron koli na kungiyar ta CEEAC da aka gudanar a birnin Malabo dake kasar Equatorial Guinea, jamhuriyyar demokuradiyyar Congo ta hada kai da sauran kasashe membobin kungiyar, don hana Ruwanda damar karbar ragamar shugabancin kungiyar a wannan karo.
Ma’aikatar ta bayyana cewa an ware Rwanda daga taron koli na 22 na ECCAS da aka gudanar a Kinshasa a shekarar 2023 karkashin jagorancin Kongo, yayin da rikici tsakanin kasashen biyu ke kara tsananta.
Gwamnatin Rwanda ta jaddada cewa wannan yanayin wata sabuwar shaida ce ta “wuce gona da iri” na kungiyar, kuma ba ta wani dalili na ci gaba da kasancewa mamba na wata kungiya da ke aiki ba bisa ka’idoji da amfanin da aka kafa ta ba.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Najeriya Ya Kaddamar Da Aikin Samar Da Ruwa Da Kamfanin Sin Ya Gudanar A Birnin Abuja
Shugaban tarayyar Najeriya Bola Tinubu, ya kaddamar da aikin samar da ruwan sha mai tsafta wanda kamfanin CGCOC na kasar Sin ya tallafa wajen gudanar da shi a birnin Abuja, fadar mulkin kasar. Ya kuma jaddada aniyar gwamnatinsa, ta yin aiki tukuru a fannin samar da ababen more rayuwa, da kai tsaye za su inganta rayuwar al’ummun kasar.
Shugaba Tinubu ya bayyana aikin a matsayin muhimmin mataki na tabbatar da al’ummun birnin sun samu ruwa mai tsafta, mai dorewa kuma isasshen a gidaje da hukumomi, da dukkanin sassan birnin. Ya kuma godewa gwamnatin kasar Sin da kamfanin CGCOC, bisa hadin gwiwarsu wajen tabbatar da nasarar aikin.
Yayin da yake nasa tsokaci kuwa a bikin kaddamar da aikin, mukaddashin jakadan Sin a Najeriya Zhang Yi, ya ce aikin na da matukar muhimmanci ga kyautata samar da ruwa a birnin Abuja, kasancewar zai kara yawan ruwan da al’ummar birnin za su iya amfani da shi da rubi uku, wato daga kyubik mita 240,000 zuwa kyubik mita 720,000. Zai kuma baiwa al’ummun birnin har kimanin miliyan uku damar samun isasshen ruwa mai tsafta domin amfanin yau da kullum.
Bugu da kari, karkashin aikin, an horar da ma’aikata ‘yan kasa dabarun samar da ruwa, da fasahohin shimfida bututai, wanda hakan ya samar da guraben ayyukan yi na kai tsaye da wadanda ba na kai tsaye ba har sama da 3,000, matakin da ya ingiza fannin bunkasa kwarewa, da ciyar da tattalin arziki gaba, da ma raya zamantakewar al’ummar birnin na Abuja, kamar dai yadda kamfanin CGC Nigeria, reshen kamfanin CGCOC ya bayyana. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp