Rashin Abinci Na A Waka Ya Sa Na Daina Yi -T Y Shaba
Published: 8th, June 2025 GMT
A masana’antar Nollywood dake Kudancin Nijeriya, manyan masu kudinsu, sarakuna, hukumomi da gwamnatoci na iyakar kokarinsu wajen ganin masana’antar ta cigaba, ta hanyoyi daban daban da suka hada da kayan aiki, wajen daukar fim, fadada ilimi, tallace tallace da sauran tallafi da masana’antar ke bukata, a wasu lokutan ma akan daukesu har kasashen Turai wajen koyon aiki da kuma tallata hajarsu ga manyan dillalan fim a Duniya wanda ta wannan hanyar sai su samu manyan kudade.
T Y ya cigaba da cewa idan ana maganar masana’antar Kannywood ba haka abin yake ba, domin kuwa a nan yankin sai mai shirya fim ya nemi gida ko kamfanin da zai shirya fim din sa ya rasa, hakan zai sa ya je ya dauki Hotel ko wani gidan haya domin gudanar da aikinsa wanda yace ta haka ne zakaga fina finai suna kamanceceniya da juna saboda kusan komai da komai a waje daya akayi su sakamakon rashin wurare.
Mu a nan arewacin Nijeriya har yanzu ba a daukemu a matsayin wasu da zasu iya kawo cigaba kokuma su samar da aiyuka ga matasa ba, shi yasa ba duk taimako ake mana ba saboda a nasu tunanin babu wani abin cigaba da zamu iya kawowa, yanzu ga misali wanda yafi kowane mutum dukiya a nahiyar Afirika dan arewa ne kuma bahaushe, amma idan yanzu ana son ayi fim wanda za a taka rawar babban mutum kamar Dangote ba lallai bane hakan ta faru.
Saboda ba za a samu isassun manyan gidaje ko manyan motoci da za ayi amfani dasu a fim din ba duk da cewa akwai su da dama, don haka ina kira ga manyan masu kudinmu, mahukuntanmu, sarakuna da gwamnatocinmu su yi kokarin taimakawa wannan masana’antar ta Kannywood da ake shirya fina finai da harshen Hausa ta kowane fanni, hakan zai sa muyi gogayya da takwarorinmu na gida da ma na kasashen waje inji TY Shaba.
Daga karshe ya bukaci matasa da su kasance masu biyayya da hakuri, da kuma jajircewa wajen ganin burikansu sun cika, yace dole ne sai an sha wuya akan sha dadi, kuma duk wanda suka gani a cikin masana’antar Kannywood babu wanda ya shigo a matsayin mai kudi, kowa a talaka ya fara kafin ya zama abinda ya zama, don haka kuma idan kukayi hakuri komai zai zo ya wuce ba tareda wata tangarda ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: masana antar
এছাড়াও পড়ুন:
Xi: A Shirye Sin Take Ta Hada Hannu Da Canada Wajen Mayar Da Dangantakarsu Bisa Turbar Da Ta Dace
Yayin ganawarsa da firaministan Thailand, Shugaba Xi Jinping ya ce a shirye kasarsa take ta karfafa hadin gwiwa da Thailand kan dabarun samun ci gaba, tare kuma da gabatar da gogewarta na samun ci gaba a sabon zamani, kuma ya yi kira da a gaggauta gina layin dogo tsakanin Sin da Thailand da bunkasa hadin gwiwa a bangaren cinikin amfanin gona da tattalin arziki mai kiyaye muhalli da kuma kirkire kirkiren fasaha. (Mai fassara: FMM)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA