Kar Ki Bari Naman Sallah Ya Kashe Miki Aure Yar’uwa
Published: 6th, June 2025 GMT
Ya ke ‘yar uwa mai albarka,idan kina da ‘ya a gidan aure ko kanwa,don Allah mu tuntube su ranar Sallah mu ji halin da suke ciki su da jikokinki, wannan lokaci ne da za ki taimaka musu don ganin farin cikin su, abin akwai wahala a Sallah ka ji gida shiru ba labari, don Allah iyaye a taimaka ma yaran da suke gidan aure.
Sannan makota masu karfi ku duba girman Allah ku yi sadaka idan kun yi yanka, ana raba naman Sallah uku, na amfanin gida, sadaka ma mabukata da kuma na kyauta ma, ‘yan uwa da abokan arziki, hakan zai taimaka wajen kowa ya yi walwala ya san Sallah ake yi.
Shekarar da ta wuce wata ke ba da labari ta ce, “Shekarun da suka wuce makotanta shanu biyu suka yanka da raguna wanda suke kallon juna, dayan makwabtan kuma shanu da raguna, amma ba wanda ya aiko musu sadaka ga yara ta kulle su a gida ta hana kowa fita, Jama’a wannan wane irin makotaka ne Sallah guda. Allah ya sa mu gane.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Sin Ta Yi Allah Wadai Da Illata Fararen Hula Tare Da Fatan Gaggauta Kawo Karshen Yaki A Sudan
Wasu rahotanni na cewa dakarun RSF a kasar Sudan, sun hallaka fararen hula kusan 2000 a birnin El Fasher, fadar mulkin jihar arewacin Darfur. Kuma tuni MDD, da kungiyar tarayyar kasashen larabawa ta AL, da kungiyar tarayyar Afirka ta AU, da ma wasu karin hukumomin kasa da kasa suka fara mayar da hankali kan yanayin jin kai da ake ciki a birnin na El Fasher, suna masu Allah wadai da muggan ayyukan da ake aikatawa kan fararen hula.
Game da hakan, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta bayyana a Litinin din nan, yayin taron manema labarai cewa, Sin na Allah wadai da duk wasu ayyuka dake illata fararen hula, tana kuma fatan Sudan za ta cimma nasarar tsagaita bude wuta da gaggauta kawo karshen yaki. (Saminu Alhassan)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA