Hukumar Alhazai Ta Jihar Jigawa Ta Yi Tanadi Na Musamman Ga Alhazanta A Mina
Published: 4th, June 2025 GMT
Alhazan Jihar Jigawa sun fara ayyukan hajji cike da kwarin gwiwa yayin da aka kaisu Mina daga birnin Makkah, inda za su wuce zuwa Dutsen Arafat domin gudanar da aikin hajjin shekarar 2025.
Aikin hajji na farawa ne daga ranar 8 zuwa 13 ga watan Dhul Hajj a duk shekara, inda ake daukar alhazai zuwa sansanin Mina sannan su wuce zuwa Arafat, zuwa Muzdalifa, sannan Jamarat (Jamratul Akbah), kafin su dawo Makkah inda za su kammala da Dawafi.
Yawancin Alhazan da suka zanta da Rediyon Najeriya sun bayyana cewa, duk da wahalhalun da ke tattare da aikin hajji, sun kuduri aniyar gudanar da hajjin lafiya kuma cikin nasara.
Wasu daga cikin Alhazan daga kananan hukumomin Jahun da Kiyawa, Hajiya Maijidda Abdulhamid da Alhaji Mohammed Abdullahi Idris sun bayyana cewa tsoron Allah da kaunarsa ke basu kwarin gwiwar jure wahalhalun aikin hajji, kasancewar Allah Ya bada tabbacin karbar dukkan addu’o’i, don haka wajibi ne su jure domin babu wani alheri da ke zuwa cikin sauki.
Wani Alhaji daga Dutse, Murtala Sani Lama, ya bayyana cewa aikin hajji yana daga cikin ginshikan Musulunci, kuma kowanne musulmi mai hali yana da hakkin gudanar da shi. Ya kara da cewa a cikin Alkur’ani an bayyana cewa duk wata bukata da Alhaji ya roka za a amsa masa.
Ya kara da cewa wannan tabbacin kadai yana isar masa da kwanciyar hankali wajen shan wahalhalun aikin hajji komai yadda suka kasance.
Alhazan sun bayyana ra’ayin cewa kasancewar aikin hajji kira ne daga Allah kuma su baƙinsa ne na musamman, ba wani dogon tafiya ko zafi ko yawan mutane da zai hana su gudanar da ibada.
A cewar koyarwar Musulunci, duk wanda ya gudanar da aikin hajji yadda ya kamata, Allah yana gafarta masa dukkan zunubansa kuma yana bashi sabuwar dama kamar yadda aka haifi sabon jariri.
Haka kuma, a wata hira da Rediyon Najeriya, Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa, Alhaji Ahmed Umar Labbo, ya ce dukkan abubuwan da suka wajaba domin jin dadin alhazan jihar an tanade su.
“An sanya ma tantin Alhazai na’urar sanyaya daki (air condition), tare da katifa da filo da kuma bargo ga kowane Alhaji. Kuma saboda zafin rana, mun saka firijin na ruwa tsakanin tantuna domin rage hatsarin kamuwa da matsanancin kishi.”
Labbo ya kara da cewa Alhazai za su rika samun abinci sau uku a rana tare da ruwan sha, da ‘ya’yan itatuwa da kuma lemun kwalba.
Ya shawarci Alhazai da su sanya tsoron Allah a zukatansu, yana mai cewa wannan ne mataki na farko na samun hajji mai kyau da tsari.
Usman Mohammed Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa bayyana cewa
এছাড়াও পড়ুন:
NSCDC Za Ta Fara Sanyan Ido Kan Muhimman Abubuwan More Rayuwa A Jihar Kano
“Bayan karbar mukaminsa na sabon kwamandan hukumar NSCDC na jihar Kano, kwamared Bala Bodinga ya umurci jami’ansa da su sadaukar da kansu ga muhimmin aiki na tabbatar da amincin muhimman kadarori da ababen more rayuwa na kasa.
“Kwamandan jihar ya ba da umarnin cewa, ba dare ba rana, cikin sa’o’i 24, dole jami’an hukumar su rika yin sintiri da sanya ido domin dakile ayyukan barayi da masu aikata laifuka a lunguna da sako na jihar,” inji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp