2025-06-05@14:35:59 GMT
إجمالي نتائج البحث: 865
«tana goyon bayan»:
A wani cigaba makamancin haka, dakarun Mallam Fatori suma sun daƙile wani yunƙurin hari daga ‘yan ta’adda da suka zo ta wurare daban-daban. Ya ce bayan sa’o’i na musayar wuta, dakarun sun bi ‘yan ta’addan da suka tsere, inda suka hallaka da dama, wasu kuma suka gudu da raunukan harbin bindiga. An kuma kwato muggan makamai da dama kamar bindigogi AK-47, da bindigar kakkaɓo jirgi (RPG), da sauran kayayyakin yaƙi. Yanzu haka Sojojin na ci gaba da sintiri a yankin, tare da goyon bayan jiragen sama da na leƙen asiri. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin...
Mazauna unguwar da asibitin kula da ido ta kasa yake wato Mahuta da ke jihar Kaduna sun amince da Gwamna Uba Sani ya zarce karo na biyu, biyo bayan warware takaddamar filaye da aka dade ana yi wanda ya yi sanadiyar rushe gidaje da dama a gwamnatin da ta gabata. Wannan na zuwa ne bayan gwamnatin jihar Kaduna ta hannun hukumar kula da bayanan kasa ta jihar Kaduna (KADGIS) ta bayar da shedar mallakar filayen sama da 300 ga al’ummar da rusau da aka yi a zamanin tsohon Gwamna Nasir El-Rufai ya shafa. Da yake jawabi a madadin mazauna yankin, Kanar Haruna Idris Zaria mai ritaya, ya yabawa Gwamna Sani bisa abin da ya bayyana a matsayin tsarin sa...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Wata al’ada da ta zama gama gari a tsakanin matasa, ita ce yankewa da fige kaji a unguwanni, musamman a lokutan bukukuwan Sallah. A da, ana da wurare na musamman da ake yin irin wannan abu. NAJERIYA A YAU: Hanyoyin kauce wa ɓarnar ambaliyar ruwa NAJERIYA A YAU: Mokwa: Tsakanin Taraddadin Rashin Matsuguni Da Jimamin Rashin ’Yan-Uwa Sai dai masana sun ce wannan abu na iya haifar da matsaloli ga lafiya da kuma gurɓata muhalli. Wannan shi ne abin da shirin Najeriya A Yau zai tattauna a kai, yayin da ake Bikin Ranar Muhalli ta Duniya kwana ɗaya kafin Babbar Sallah. Domin sauke shirin, latsa nan
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya gana da gwamnan Jihar Ribas da aka dakatar, Siminalayi Fubara, a gidansa da ke Legas. Wannan ganawar na cikin ƙoƙarin warware rikicin siyasa da ya addabi jihar. Jami’an DSS sun kashe ’yan bindiga 45 a Neja ’Yan sanda sun sake hana hawan Sallah a Kano Fubara, ya samu saɓani da ubangidansa na siyasa, Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, bayan hauwansa mulki. Saɓani kan ikon mallakar kuɗin jihar da naɗin muƙamai ya janyo rarrabuwar kawuna a cikin gwamnatin jihar da kuma majalisar dokokin jihar. A watan Maris 2025, Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a jihar Ribas tare da dakatar da Gwamna Fubara, mataimakiyarsa, da kuma ‘yan majalisar dokokin jihar baki ɗaya. Ya naɗa...
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya karrama daya daga cikin masu kamfanin Microsoft, Bill Gates, da lambar girmamawa ta kasa — Commander of the Order of the Federal Republic (CFR), inda ya jaddada cewa Gates ya kasance abin koyi ga shugabanni a fadin duniya saboda yadda yake taimaka wa talakawa da masu bukata ta musamman. Shugaban ya kuma bayyana cewa Mista Gates, wanda shi ne Shugaban Gidauniyar Melinda da Gates, ya bada gudummawa a fannonin kiwon lafiyar mata, noma da bincike kan cututtuka masu yaduwa. Ya gode wa Bill Gates bisa gudummawar da yake bayarwa a duniya, musamman wajen saukaka rayuwa da kare lafiyar masu rauni da wadanda ke cikin bukata. Ministan Lafiya da Ci gaban Jama’a, Farfesa Ali Pate,...
ROOSC Ta Kaddamar Da Rabon Kayan Koyon Karatu a Karamar Hukumar Kaduna Sout Shirin Dawo da Yara Makaranta na Gwamnatin Jihar Kaduna Mai suna ROOSC ya kaddamar da rabon kayan koyon karatu ga dalibai a Karamar Hukumar Kaduna ta Kudu, Jihar Kaduna. An gudanar da bikin kaddamarwar ne a Makarantar Firamare ta LEA da ke Unguwar Mu’azu, inda manyan masu ruwa da tsaki kan harkar ilimi, musamman shugabannin addini da na al’umma, suka halarta. Da yake jawabi a wajen taron, Ko’odinetan ROOSC a Jihar Kaduna, Mr. Ezra Angai, ya bayyana cewa wannan shiri hadin gwiwa ne tsakanin Gwamnatin Jihar Kaduna da abokan ci gaba da kuma kungiyoyin aiwatar da shirin, domin inganta samun ilimi mai nagarta ga yaran da ba...
Rasha ta ce hare-haren Ukraine a kan yankunanta, musamman na baya-bayan nan zasu fuskanci martani mai zafi. Da yake sanar da hakan Mataimakin shugaban kwamitin sulhu na Tarayyar Rasha Dmitry Medvedev ya ce, sojojin kasar za su ci gaba da kai farmakin har sai an kawar da makiya gaba daya. Ya kuma kara da cewa babu makawa Rasha za ta mayar da martani kan ayyukan zagon kasa da sojojin Ukraine suka yi. A cewarsa, za a ci gaba da kai hare-hare ba tare da kakkautawa ba, kuma wadanda ke da alhakin wadannan ayyuka. Hukumar tsaro ta Ukraine dai ta ce an kai wa wata gada mai muhimmanci hari da ta hada Rasha da yankin Crimea da bamabamai. Ta ce an...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Yayin da sallah ya gabato, mutane da dama kan yi fadi tashi don biyan wasu bukatun su na bukukuwan sallah, kuma kamar yadda aka saba, a irin wannan lokaci ne iyalai da dama kan maida hankulan su don ganin sun biya wasu daga cikin bukatun su musamman wadanda suka jibanci bikin sallah. Siyayyan kayan kayan abinci na daya daga cikin wadannan hidindimu, sai dai kayan miya da suka zama dole ayi amfani dasu yayin bikin sallah sun yi tashin gwauron zabo inda alumma da dama ke ta bayyana damuwar su kan wannan batu. NAJERIYA A YAU: Hanyoyin kauce wa ɓarnar ambaliyar ruwa DAGA LARABA: “Sai Na Tara Kudin Cin Abinci Na Nake...
Sanarwar tafiyar tasa ta biyo bayan ganawar da Inzaghi ya yi da jami’an Inter a ranar Talata, sanarwar da Inter Milan ta fitar ta ce Kulob din da Simone Inzaghi sun yanke shawarar rabuwa, “Wannan shi ne shawarar da aka dauka bisa yarjejeniyar juna”, shugaban Inter Giuseppe Marotta ya kara da cewa “Ina so in gode wa Simone Inzaghi saboda aikin da ya yi, ya matukar taka rawar gani a shekaru 4 da muka shafe muna aiki tare, don haka Inter Milan na yi mashi fatan alheri a duk inda zai samu kanshi a nan gaba”. Inzaghi ya lashe gasar Seria A daya, Coppa Italia biyu da kuma Supercoppa Italia sau uku a lokacin da ya ke San Siro,...

Karuwar Darajar Sana’ar Samar Da Kayan Laturoni Da Dangoginsu a Sin Cikin Watanni 4 Na Farkon Bana Ya Karu Da 11.3%
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi wanda yake ziyar aiki a kasar Lebanon bayyana cewa kasarsa tana goyon bayan hadin kan mutanen kasar Lebanon. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka bayan ganawarsa da shugaban majalisar dokokin kasar ta Lebanon a yau Talata a birnin Beirut babban birnin kasar. Aragchi ya ce kasar Iran tana goyon bayan kasar Lebanon ta hanyar kungiyar Hizbullah. Kuma tana goyon bayanta kan HKI wacce take mamaye da wasu yankuna a kasar. Muna goyon bayan gwamnati da mutane a duk wani kokarin da zasu yi na kwato yankunan kasar wadanda HKI take mamaye da su. Ministan kafin haka ya bayyana cewa JMI tana daga cikin kasashen da zasu...
Iftila’in ambaliyar ruwa a garin Mokwa a Ƙaramar Hukumar Mokwa ta Jihar Neja ta yi ajalin mutane sama da 200, yayin da wasu sama da 500 suka bata. Ambaliyar, wadda ita ce mafi muni a yankin cikin shekaru 60, ta shafi yankunan Tiffin Maza da Anguwan Hausawa, bayan ruwan sama kamar da bakin ƙwarya a ranar Laraba da ta gabata da daddare. Ɗaruruwan gidaje sun lalace, inda mutane da yawa suka rasa matsugunansu. Kafar yaɗa Labarai ta BBC ta ruwaito a ranar Litinin cewa yawan mutanen da suka mutu ya ƙaru zuwa sama da 200, kuma an dakatar da ayyukan ceto saboda hukumomi sun yanke ƙauna daga samun wasu da rai. Babbar Sallah: Farashin kayan miya ya yi tashin...
Sojojin mamayar Isra’ilan sun sake aiwatar da wani sabon kisan kiyashi a birnin Rafah, inda suka kashe mutane da dama a kusa da cibiyar rarraba kayan agaji Fararen hula 23 ne suka yi shahada yayin da wasu kusan 200 suka jikkata a yau Talata lokacin da sojojin mamayar Isra’ila suka bude wuta kan mai uwa da wabi wa fararen hula a kusa da wata cibiyar rarraba kayan agaji a birnin Rafah da ke kudancin Zirin Gaza. Majiyoyin kiwon lafiya sun bayyana cewa: Shahidan sun fadi ne a lokacin da suke jiran agajin jin kai a titunan Rafah, lokacin da jirage masu saukar ungulu suka bude musu wuta. An tantance biyar daga cikin shahidan, yayin da wasu fiye da 20 kuma...
Ya ce yanzu lokaci ne da Arewa za ta nuna adalci ta hanyar barin shugaba daga Kudu ya kammala wa’adin mulkinsa. Ya ƙara da cewa, “Idan za a fitar da wani ɗan takarar shugaban ƙasa daga ‘yan adawa a nan gaba, to ya dace ya fito daga Kudu maso Yamma. Wannan ne dai-daito da adalci.” Sanatan ya kuma soki gwamnatin baya da cewa ko da yake kusan dukkan shugabannin tsaro sun fito ne daga Arewa, amma hakan bai dakatar da ta’addanci a yankin ba, kuma bai hana hare-hare da kashe-kashe a jihohin Filato, Binuwai da sauran jihohin Arewa ta Tsakiya ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na...
Farashin kayan miya, musamman kayan gwari ya yi tashin gwauron zabo a yayin da Babbar Sallah ta bana ta kawo jiki. Kuɗin kayan lambu ya ninka sau uku a cikin mako biyu, a yayin da Babbar Sallar ta zo wa iyalai da dama a Najeriya a hagunce, a sakamakon fama da matsananciyar matsalar tsadar rayuwa. Wannan hauhawan farashin, wana ta zarce abin da aka saba gani a lokutan rani, ya kasaara ƙarfin iyalai yin sayayya domin girki abincin Sallah, wanda hakan ya haifar da damuwa, musamman a jihohin Kano, Taraba, Kwara, da Jigawa. Tsadar da ba a taɓa gani ba a Kano Al’umma a Jihar Kano sun koka bisa mummunan tasirin wannan tsadar rayuwa. Wani ma’aikacin gwamnati mai ’ya’ya biyar,...
Masu sayar da rago a jihar Zamfara sun nuna damuwarsu kan rashin samun ciniki gabanin bikin Eid-el-Kabir, duk da cewa ana samun dabbobi a kasuwanni. Shugaban kungiyar masu sayar da dabbobi ta jihar Zamfara, Malam Saidu Ibrahim Gusau ya bayyana haka a wata tattaunawa da gidan rediyon Najeriya a Gusau. Malam Gusau ya bayyana cewa, duk da cewa ana samun raguna da yawa, amma an samu karancin masu saye. Sai dai ya bayyana fatan cewa lamarin zai iya gyaruwa yayin da bukukuwan Sallah ke kara gabatowa. “Amma idan abubuwa sun ci gaba da haka, to gaskiya, akwai matsala ta gaske,” “Har yanzu, na yi imani cewa da sauran kwanaki abubuwa za su iya canzawa, in...
’Yan bindiga sun sako wani magidanci da suka yi garkuwa da shi da amaryarsa na tsawon wata bakwai, bayan sun bindige matar tasa tare da karɓar kuɗin fansa Naira miliyan 30 daga iyalansa. A watan Oktobar 2024 ne ’yan bindiga suka yi garkuwa da mutumin suna Yakubu Dada tare da amaryarsa, a yayin da ma’auratan ke tafiya a kan babban titin zuwa Kontagora a Jihar Neja. A lokacin ’yan bindigar sun buƙaci kuɗin fansa Naira miliyan 10 daga iyalan mutumin, wanda tsohon ma’aikacin gwamnati ne. Ba su sako shi ba sai a ranar Litinin, bayan da suka karɓi ƙarin Naira miliyan 20 daga iyalansa, jimilla Naira miliyan 30 ke nan. A lokacin da suka yi garkuwa da ma’auratan sun buƙaci...
’Yan bindiga sun sako wani magidanci da suka yi garkuwa da shi da amaryarsa na tsawon wata bakwai, bayan sun bindige matar tasa tare da karɓar kuɗin fansa Naira miliyan 30 daga iyalansa. A watan Oktobar 2024 ne ’yan bindiga suka yi garkuwa da mutumin suna Yakubu Dada tare da amaryarsa, a yayin da ma’auratan ke tafiya a kan babban titin zuwa Kontagora a Jihar Neja. A lokacin ’yan bindigar sun buƙaci kuɗin fansa Naira miliyan 10 daga iyalan mutumin, wanda tsohon ma’aikacin gwamnati ne. Ba su sako shi ba sai a ranar Litinin, bayan da suka karɓi ƙarin Naira miliyan 20 daga iyalansa, jimilla Naira miliyan 30 ke nan. A lokacin da suka yi garkuwa da ma’auratan sun buƙaci...
Jami’an Tsaron Saudiyya sun kori mutane sama da 205,000 da ke neman yin aikin Hajji ta barauniyar hanya daga birnin Makka a yayin da aikin Hajjin bana ya kawo jiki. Daraktan Tsaron Jama’a kuma Shugaban Kwamitin Tsaron Hajji, Laftanar-Janar Mohammed Al-Bassami, ya bayyana cewa hukumomin kasar sun hana mutane sama da 269,000 marasa takardun izini shiga Makka, da kuma motoci 110,000 dauke da mahajjata ba bisa ka’ida ba da aka hana shiga. An kuma kama 1,239 da suka yi yunkurin jigilar mahajjata ba bisa ka’ida ba, tare da ci tarar masu karya dokokin Hajji sama da 75,000, kuma tare da bankado ofisoshin aikin Hajji na bogi sama da 415. Laftanar Janar Mohammed Al-Bassami ya sanar da hakan ne a...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta bayyana cewa: Rahoton IAEA na nuna son kai kuma an shirya shi ne a karkashin tasirin wasu kasashe Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Rahoton da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya ta fitar ya kunshi maimaici da wuce gona da iri, yana mai jaddada cewa, an shirya wannan rahoton ne karkashin tasirin wasu kasashen Turai. Ya bayyana takaicinsa kan yadda kasashen yammacin duniya ke cutar da martabar wata kungiya ta duniya ta hanyar siyasantar da ayyukanta. A farkon taron manema labarai na mako-mako, Baghaei ya yi la’akari da zagayowar ranar wafatin Imam Khumaini (Allah ya kara masa yarda) da shahidan juyin juya halin Musulunci. Ya kara da cewa: Ma’aikatar harkokin...
Wasu ’yan daba sun yi wa Mataimakin Firinsifal na wata makarantar sakandare dukan tsiya a wani mummunan harin da suka kai masa saboda ya hana wani ɗalibi satar jarabawa. A yayin da ake ci gaba da jarabawar kammala sakandare ta WASSCE da ake yi a halin yanzu ne, Mista Rotifa, mataimakin shugaban wata makaranta mai zaman kanta mai suna Child Development College da ke Akure, hedikwatar Jihar Ondo, ya hana ɗalibin satar amsa. Bayan haka ne ’yan daban sun tsare Mista Rotifa suka yi masa dukan kawo wuƙa bayan sun jawo shi daga motar ’yan sanda, kafin a ceto shi a kai shi asibiti. Lamarin ya faru ne bayan Mista Rotifa ya ƙwace wayar salula da wani ɗalibi ke amfani...
Ya buƙaci shugabannin haɗakar su fara tsarin kafa sabuwar jam’iyyar da za ta kasance mai suna ɗaya, falsafa ɗaya, da tsarin shugabancin da zai haɗa kan kowa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Jami’ai a Falasdinu sun ce akalla mutum 31 ne sukayi shahada sannan wasu sama da 150 sun jikkata, bayan wani hari da Isra’ila ta kai kusa da wurin rabon abinci a birnin Rafah. Dama shugaban hukumar MDD da ke kula da yan gudun hijirar Falasdinawa, Philippe Lazzarini, ya ce rabon kayan agajin ya zama tarkon mutuwa. Lamarin dai ya faru ne a kusa da wata cibiyar rarraba kayan abinci da gidauniyar agaji ta Gaza (GHF) ke gudanarwa, wani kamfani mai zaman kansa da ke samun goyon bayan Isra’ila da Amurka da kungiyoyin agaji na kasa da kasa suka yi suka. Kakakin kungiyar Hamas Sami Abu Zohri yayi Allah wadai da gwamnatin Isra’ila kan harin da ta aikata a rabon kayan...
Ma’aikatar lafiyar kasar Sudan ta bayyana cewa: Ana ci gaba da daukan matakan ganin an shawo kan ci gaba da yaduwar masifar kwalara a kasar Gidan talabijin na Al-Alam ya watsa rahoton cewa: A halin da ake ciki a fannin kiwon lafiya a birnin Khartoum fadar mulkin kasar bayan bullar cutar kwalara yana ta kokarin ya shawo kan matsalar tare da killace mutanen da suka kamu da cutar a wurare na musamman a babban birnin kasar Khartoum, rahotonni sun bayyana cewa: Cutar ta bazu cikin sauri a birnin. Sannan ma’aikatar lafiya ta Sudan da kungiyoyi da dama suna ci gaba da kokarin shawo kan cutar don kada ta zama annoba wadda za ta yadu zuwa jihohi da dama. Wakilin gidan...
Hon. Nasiru ya kara da cewa Gwamna Radda ya yi kokari wajen yaki da matsalolin tsaro wanda suka addabi Jihar Katsina, inda ya bayyana cewa ana samun sauki sosai a wannan bangare. Ya ce gwamnati ta gyara makarantu da asibitoci a fadin Jihar Katsina, inda aka maida su na zamani tare da daukar ma’aikatan lafiya da kuma malaman makaranta da yawansu ya kai 7,000, wanda ya ce ko haka aka tsaye suna da hujja da dalilin mara masa baya. Idan za a iya tunawa a makon da ya gabata ne, ‘yan majalisun tarayya guda 15 dukkansu na jam’iyyar APC suka ayyana Gwamna Radda a matsayin wanda za su goya baya a zaben 2027. Sai dai kuma ana dora ayar tambaya...
A nasa jawabin, shugaban kwamitin shirya musabakar karatun alkurani na karamar hukumar Igabi, Malam Abubakar Sadik Muhammad (Abu Asim), ya ce duk irin nasarar da kwamitin ya samu, ya samu ne bisa goyon bayan da Honarabul Yusuf Ibrahim Zailani yake ba su. Ya ce shi ne kashin bayan samun nasarar da suka yi a fadin duniya. Ya bukaci daukacin iyaye da su kara zage damtse wajen ganin ‘ya’yansu sun samu ilimi nagartacce da kuma sanya ido wajen kula da tarbiyyarsu. Haka zalika, kwamitin shirya musabakar karatun alkurani ya karrama Zailani da lambar yabo bisa irin gudummawar da yake bai wa addinin Musulunci a ciki da wajen Jihar Kaduna. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu...
Bayan mintuna 90 na wasan ba tareda wani ya doke wani ba sai alkalin wasa ya bayar da damar bugun daga kai sai mai tsaron raga, Jamaica ta ci kwallaye 4 inda Nijeriya ta ci dukkan kwallaye 5 da yan wasan suka buga, hakan ya sa yaran na Eric Chelle suka lashe gasar Unity Cup ta bana da ta kunshi kasashen Ghana, Trinidad And Tobago, Jamaica da Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
“Gane amfanin lamarin da ya shafi ilimi shi yasa, Gwamna Lawal ya kaddamar da dokar ta baci a bangaren ilimi a watan Nuwamba 2023,matakin da aka dauka an yi sa’a ya haifar da da mai ido a bangaren ilimi a Jihar Zamfara. “Fiye da makarantu 500 aka y masu kwaskwarima da samar masu abubuwan da suka kamata tun lokacin da aka kaddamar da dokar ta bacin.An horar da Malaman makarantun gwamnati,ana kuma ci gaba dayin hakan. “Saurin biyan kudaden bashi da Hukumomin WAEC da NECO ya kawo kwanciyar hankali ga daliban da suka kammala makaranta da rubiuta jarabawa, sai dai basu samu ci gaba da karatu ba saboda Hukumomin jarabawar sun rike masu sakamakon jarabawar da suka yi. Daga...
A karon farko, rundunar tsaron Indiya ta tabbatar da cewa ta rasa wasu jiragen yaƙi a yayin arangama mai tsanani da suka fafata da Pakistan a farkon watan Mayu. Wannan sanarwa ta fito ne daga bakin Babban Hafsan Tsaro na Indiya, Anil Chauhan, a taron Shangri-La Dialogue, babban taron tsaro na Asiya, a Singapore. Tun da farko, jami’an Indiya sun yi ta musanta duk wata asarar jiragen sama a cikin wannan arangama, wanda aka fara ne bayan wani hari da aka kai wa masu yawon bude ido a yankin Kashmir da Indiya ke mulka a watan Afrilu, wanda Indiya ta dora alhakinsa kan Pakistan. Ita kuwa Pakistan, ta yi ikirarin cewa ta harbo jiragen Indiya da dama, ciki har da...

Cutar Kwalara Ta Yadu A Sudan Baya Ga Matsalar Tashe-Tashen Hankulan Da Suke Ci Gaba Da Yuduwa A Kasar
Cutar kwalara ta yadu a Sudan, kuma ‘yan tawayen dakarun kai daukin gaggawa sun kai hare-hare kan asibitoci biyu a Jihar El Obeid na kasar Sudan na ci gaba da fama da tabarbarewar yanayin tsaro da lafiya bisa la’akari da abubuwan da ke faruwa a baya-bayan nan. A bangaren tsaro kuma, Dakarun Kai Daukin Gaggawa na Rapid Support Forces sun kai hare-haren bama-bamai a wasu asibitoci biyu da wasu unguwanni a birnin El Obeid da ke Arewacin Kordofan a tsakiyar kasar Sudan. Wata majiyar soji ta bayyana cewa: Dakarun kai daukin gaggawa sun afkawa Asibitin Al-Daman da kuma Jami’an lafiya da ke tsakiyar birnin da manyan bindigogi. Sojojin Sudan sun tabbatar da cewa: Sun yi luguden wuta kan sansanonin dakarun...
A jawabinsa a wajen rabbata hannun yarjejeniyar, jami’in shirin na jihar ta Gwambe, Farfesa Usman Bello Abubakar, ya danganta wannan aiki a matsayin wani babban ci gaba a jihar. Ya kara da cewa, aikin ba kawai wurin yanka dabbobi ba ne, akwai kuma batun zuba hannun jari ga ci gaban kiwon su kansu dabbobin. A cewarsa, za su tabbatar da aiki da ka’idojin duniya wajen tsafta, yanka da kuma sarrafa nama. Jami’in ya kuma yaba wa gwamnan na Jihar Gombe, Inuwa Yahaya bisa hangen nesansa na kokarin kyautata samar da kayan more rayuwa da kuma bunkasa tattalin arzikin jihar baki-daya. Shi kuwa a nasa jawabin, shugaban gudanarwa na kamfanin Arch. Yunusa Yakubu, ya yi alkawarin kammala aikin cikin inganci, sannan...
Jami’in kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya ya ce matakin da Isra’ila ta dauka na hana agajin abinci ga Falasdinawa da ke fama da yunwa a yankin Zirin Gaza da aka yi wa kawanya ya zama laifin yaki. “Muna ganin abinci dake jibge a kan iyakoki kuma ba a ba da izinin shigar da shi ba a lokacin da jama’a a gefen iyakar ke fama da yunwa, a yayin da muke jin ministocin Isra’ila suna cewa sun ayin hakan ne don matsa lamba kan al’ummar Gaza,” in ji Mataimakin Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Tom Fletcher a wata hira a ranar Jumma’a. Irin wannan na a matsayin laifin yaki ne,” in ji shi. Baya ga hakan...
Ya ce a nemi bayani daga wurare daban-daban kamar Kungiyar Ma’aikatan Kananan Hukumomin Nijeriya (NULGE) da Ma’aikatar Kudi, ya kara da cewa sakataren gwamnatin tarayya shi ne shugaban kwamitin aiwatar da hukuncin. Abubuwan da mutane yawa suke gnin ya janyo jinkirta aiwatar da hukuncin shi ne, shigar da sabon sharadi daga Babban Bankin Nijeriya (CBN), wanda ke bukatar dukkanin hukumomin gwamnati 774 su bayar da akalla shekaru biyu na rahotannin kudinsu kafin su iya karbar kasafin kudadensu kai tsaye daga asusun gwamnatin tarayya. Babban bankin ya bayyana cewa dole ne gwamnatocin kananan hukumomi su cika bukatun kafin su bude asusu don kura musu kudadensu kai tsaye. Ka’idojin da aka gindaya wa kananan hukumomin ya kara janyo tsaiko wajen jinkirta aiwatar...
Wani mutum mai suna Adamu Muhammed Tenimu ya suma bayan da samu labarin cewa matarsa ta haifi jarirai ’yan uku a asibitin koyarwa na Jami’ar Tarayya da ke Lokoja babban birnin Jihar Kogi ranar Juma’a. Shaidu sun ce, mutumin da ya ji cewa matarsa ta haifi ‘ya’ya mata uku, sai ya faɗi ya suma a harabar asibitin nan take. Zazzaɓin Lassa da sanƙarau ya kashe mutum 366 a jihohi 24 – NCDC Shekaru 6: Don amfanin matasa mun inganta ilimi da noma — Gwamna Buni Jami’an asibitin da masu jajantawa sun yi wa mutumin agaji inda cikin gaggawa aka samu ya farfaɗo. Jim kaɗan da farfaɗowarsa, Muhammed, wanda aka ce ya kasance mai neman aikin yi na tsawon shekaru, ya ce...
MDD ta yi gargadi akan yunuwar da mutanen Gaza suke fama da ita, sannan ta kara da cewa: Isra’ila ta hana shigar da kayan agaji, kuma rabin cibiyoyin kiwon lafiya na yankin sun daina aiki saboda rashin isar da kayan agaji daga waje.” Ofishin MDD wanda yake kula da ayyukan agaji ne ya yi wannan gargadin, sannan ya kara da cewa: Yankin Gaza shi ne wurin da aka fi fama da yunwa a duniya baki daya.” Mai Magana da yawun ofishin na MDD ya ce: da akwai manyan motoci 600 da suke dauke da kayan agaji da su ka isa kan iyakar Gaza, amma asalinsu 900 ne da bisa wasu dalilai an hana su isa bakin iyaka.” Haka nan kuma...
Wasu jami’an diplomasiyyar turai sun yi wa gwamnatin Benjamin Netanyahu da cewa za ta fuskanci Karin matsin lamba idan har ba ta sauya halayyarta akan Gaza ba. Jaridar “Washington Post” ta Amurka ta ambato jami’an diplomasiyyar turai suna cewa; sabon tsarin da ake yin aiki da shi na raba kayan agaji a Gaza, ya juya ya zama harigitsi kuma ana bude wuta akan mutane da hakan ya yi sanadiyyar jikkatar Falasdinawa da dama.” Har ila yau jami’an diplomasiyyar na turai sun ce, ko kadan ba su da aniyar bayar da kayan agajinsu ga masu tafiyar da tsarin da su ne Isra’ila da Amurka.” Bugu da kari, majiyar diplomasiyyar ta tarayyar turai ta ci gaba da cewa; Hotunan masu ban tsoro...

Han Zheng Ya Halarci Bikin Bude Tattaunawa Ta Hudu Kan Musaya Da Koyi Da Juna A Tsakanin Al’ummomi Ta Fannin Wayewar Kansu
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Kasar Faransa ta ce daga ranar daya ga watan Yuli mai zuwa ta haramta shan sigari a wuraren taruwar jama’a. Kasar ta ce wuraren da haramcin ya shafa sun hada da makarantu da tashoshin mota ko na jirgi, wuraren shakatawa, wuraren wasanni ko kasuwanni saboda kada yara kanana su gani. Yadda ambaliyar Neja ta ci mutum 12 ’yan gida daya NAHCON ta kammala jigilar maniyyata aikin hajjin 2025 Ministar Lafiya da Iyali na kasar, Catherine Vautrin ce ta bayyana hakan a ranar Alhamis, inda ta ce, “Dole a daina shan sigari a wuraren da yara suke. “’Yancin shan sigari ya kare ne a inda ’yancin yara na shakar tsaftatacciyar iska ya fara,” kamar yadda ministar ta shaida wa jaridar Ouest-France...
A tsawon kwanaki 602 a jere, sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da aiwatar da kisan kiyashi kan Falasdinawa a yankin Zirin Gaza Sojojin mamayar Isra’ila na ci gaba da yakin da suke yi na kisan kiyashi a zirin Gaza, inda suka sake kaddamar da wani sabon yaki kan Gaza bayan tsagaita bude wuta. Hakan ya biyo bayan sauya ra’ayi da Fira ministan gwamnatin haramtaciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi kan yarjejeniyar tsagaita bude wuta, bisa la’akari da goyon bayan siyasa da na soji da Amurka ke ba shi, a cikin shiru da kasashen duniya suka yi da kuma gazawar da ba a taba gani ba daga kungiyoyin kasa da kasa. Kafofin yada labaran Falasdinu sun ruwaito cewa: Sojojin...
PUNCH Metro ta tuna cewa a kwanakin baya jami’an hukumar EFCC shiyyar Ilorin sun kama wasu mutane 17 da ake zargi da damfarar yanar gizo a cikin hadaka a Kananan Hukumomin Ilorin da Ifelodun na jihar. Oyewale ya ce an tare wadanda ake zargin ne a madatsar ruwa ta Asa da yankin Jami’ar Al-Hikmah da yankin Gaa-Odota da ke Ilorin da kuma yankin Ganmo da Amoyo na jihar. “Kamen da aka yi a ranar Talata, 13 ga Mayu, 2025, ya biyo bayan bayanan sirri da aka samu wanda ya alakanta wadanda ake zargin da ayyukan damfara ta Intanet a jihar. Sanarwar ta kara da cewa, “Kayan da aka kwato daga hannunsu da aka kama sun hada da manyan motocin alfarma...
Wasu mutum 12 ’yan gida daya da almajirai sama da 50 na cikin mutanen da suka rasu a ambaliyar ruwan da ta afka wa yankin Tiffin Maza da Anguwan Hausawa na karamar hukumar Mokwa a jihar Neja a ranar Laraba. Ambaliyar, wacce ta biyo bayan wani mamakon ruwan sama da aka tafka a daren na Laraba, ta kuma lalata dukiyoyi da dama, yayin da har yanzu ake ci gaba da neman wasu mutanen da suka bace. Garin Mokwa dai ya shahara da zama wani zango na direbobin manyan motoci, wanda hakan ya sa garin ya zama daya daga cikin mafiya hada-hadar mutane a jihar ta Neja. NAHCON ta kammala jigilar maniyyata aikin hajjin 2025 Ambaliyar ruwa ta kashe sama da...
Kasar Brazil ta jaddada goyon bayanta ga ‘yancin Jamhuriyar Musulunci ta Iran na amfani da makamashin nukiliya na zaman lafiya A yayin ganawarsa da sakataren kwamitin kolin tsaron kasar Iran, mataimaki na musamman ga shugaban kasar Brazil ya sanar da cewa kasarsa tana goyon bayan ‘yancin Jamhuriyar Musulunci ta Iran na yin amfani da makamashin nukiliya na zaman lafiya da kuma aiwatar da shirin inganta sinadarin Uranium don bunkasa harkokin ilimi cikin gida ta hanyar fasahar makamashin nukiliya. A yayin ganawar tasu, Ali Akbar Ahmadian, sakataren majalisar kolin tsaron kasar Iran, da mataimaki na musamman ga shugaban kasar Brazil Celso Amorim, sun jaddada muhimmancin ci gaba da gudanar da hadin gwiwa da tuntubar juna tsakanin kasashen biyu masu cin gashin...
Sanarwar bayan taron koli na hadin gwiwar Sin da kungiyar tarayyar kasashen kudu maso gabashin Asiya wato ASEAN, da kwamitin hadin gwiwar kasashen Larabawa na yankin Gulf wato GCC, ta jaddada burin sassan uku na bunkasa hadin gwiwar raya tattalin arziki, musamman ta hanyar gudanar da cinikayya marar shinge, da kammala yarjejeniyar gudanar da cinikayya cikin ’yanci tsakanin Sin da da GCC. Idan mun waiwayi wannan sanarwa ta hadin gwiwa, za ku gano manufofin da sassan uku ke fatan cimmawa, wadanda suka hada da fatan dunkule shiyyoyinsu waje guda, da kara yin tafiya tare, da neman samun ci gaba mai dorewa. Karkashin wadannan burika, sassan uku za su yi amfani da fifikonsu wajen cimma moriyar juna da karfafa kawance a...
Shugaban kwamitin kungiyar Tarayyar Afrika (AU) Mahmoud Ali Youssouf, ya nanata godiyar kungiyar bisa irin goyon bayan da kasar Sin ke ba ta da ma kasashen Afrika a muhimman bangarori kamar na cinikayya da raya ababen more rayuwa da aikin gona da kiwon lafiya da bunkasa kwarewar jami’ai. Wata sanarwa da aka fitar jiya Laraba, ta ruwaito Mahmoud Ali Youssouf na bayyana haka ne yayin da yake bankwana da Hu Changchun, shugaban tawagar kasar Sin a AU. Shugaban na kwamitin AU ya kuma yaba wa jajircewar Hu tare da gode wa kasar Sin dangane da gudunmuwar da ta bayar na gina Cibiyar Kandagarki da Dakile Yaduwar Cututtuka ta Afrika, da taimakonta ga aikin wanzar da zaman lafiya da sauran taimakon...
Ɗaruruwan ɗalibai ne suka suka tsallake rijiya da baya a lokacin da ajujuwan da suke rubuta jarabawar kammala sakandare (SSCE) a ranar Laraba. Lamarin ya faru ne a makarantar sakandiren gwamnati da ke Namne a Ƙaramar hukumar Gassol a Jihar Taraba. Ko kwabo ban ciyo bashi ba tun da na zama Gwamnan Kaduna – Uba Sani Ambaliyar ruwa ta kashe sama da mutum 50 a Neja Ajujuwan sun rufta musu a lokacin da aka yi ruwan sama kamar da baƙin ƙwarya da iska. Ɗaliban da masu kula da jarrabawar sun maƙale a cikin ajujuwan da suka rufta na tsawon sa’o’i kafin wasu mazauna garin su kuɓutar da su. Wani mazaunin garin Alhaji DanAzumi Lauris ya shaida wa Daily Trust cewa,...
Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya ce tun da ya hau kujerar mulki shekaru biyu da suka wuce ko kwabo bai ciyo ba a matsayin bashi. Ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da wasu ’yan jaridu a Kaduna ranar Alhamis, albarkacin cikarsa shekaru biyu a mulki. A cewar Gwamnan, bankuna da dama sun tunkare shi suna neman ya ci bashi amma ya ki saboda ba ya so ya ci gaba da dilmiyar da jihar a kangin bashi. Ambaliyar ruwa ta kashe sama da mutum 50 a Neja ’Yar Najeriya ta tsinci miliyan 8.2 a Saudiyya ta mayar wa da mai su Gwamnan ya ce a maimakon haka, ya ma rage kudaden alawus-alawus na Sakataren Gwamnatin jihar da...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A yau shekara biyu ke nan cif tun bayan da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya karɓi mulkin Najeriya a matsayin shugaban ƙasa na 16 tun bayan samun ‘yancin kai. Daya daga cikin abubuwan da shugaban kasar ya fara yi yayin jawabin karbar mulkin shi ne sanar da kawar da tallafin man fetur. Yayin da yake cika shekaru biyu, ana ci gaba da muhawara mai zafi game da irin nasarorin da aka samu da kalubalen da ake fuskanta da kuma yadda al’ummar ƙasa ke amfana da tsare-tsaren gwamnati. NAJERIYA A YAU: Matsalolin Da Suke Tarnaki Ga Kananan Yara A Najeriya Da Hanyoyin Magance Su DAGA LARABA: “Sai Na Tara Kudin Cin Abinci Na...
A ci gaba da tafka laifukan yakin da HKI take yi a Gaza,Fiye da Falasdinawa 60 ne su ka yi shahada a jiya Laraba. A wani harin da sojojin mamayar su ka kai a yankin Jabaliya, Falasdinawa 5 sun yi shahada, yayin da wani adadi mai yawa su ka jikkata. Wani jirgin sama maras matuki ya kai wani harin a unguwar “Shuja’iyya” wnada ya yi sanadin shahadar mutum daya, sai kuma wasu shahidan 4 a unguwar “Shari’u 5”, da kuma wasu shahidan 4 a garin “Bani-Suhaila”. Wasu rahotannin sun ce, ‘yan sahayoniyar sun kai wasu hare-haren a garin ‘Abasan al-kabira’ da ya yi sanadin shahadar mutum daya da kuma jikkatar wasu masu yawa. A yankin Qizan kuwa, ‘yan sahayoniyar sun...
Daya daga cikin maniyyata Aikin Hajjin bana daga jihar Filato mai suna Hajiya Zainab ta mayar wa da wani dan kasar Rasha kudinsa da ta tsinta a birnin Makka na kasar Saudiyya, har kimanin Naira miliyan takwas da dubu 200. Rahotanni sun nuna matar ta tsinci guzirin maniyyacin ne a Masallacin Harami na Makka a ranar Talata . Ta tsinci kudin ne da yawansu ya kai Dala dubu biyar, kimanin miliyan takwas da dubu 200 a Naira, idan aka canza a kan farashin N1,648 a kan kowacce Dala daya. Babu wanda ya tayar da bam a Abuja —Wike Kotu ta yanke wa Murja Kunya hukuncin dauri a gidan yari Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) da kuma Shugaban...
Shugaban rundunar mayakan sama ta kasa,Air Marshal, Hassan Abubakar, ya bukaci tsoffin daliban makarantar ‘ya’yan sojoji dake Zaria watau NMS da su kasance masu kwazo da da’a a duk inda suke kamar yadda suka koya a makarantar. Ya bayyana haka ne lokacin da ya ke jawabi a matsayin Babban bako na musamman a wurin bukin cika shekara 71 da aka gudanar a filin faretin RSM Zakari Kumasi dake harabar makarantar a zaria. Shugaban rundunar mayakan saman ya bayyana cewa makarantar ta NMS ta yi fice wajen baiwa yara horo a fannonin karatu da kuma ilimin aikin soja wanda hakan ya sa ta samar da manyan sojoji da dama har ma da shi a ciki. Air Marshal Abubakar ya ce bukin...
Kunngiyar Tarayyar Turai, ta ce ba ta gamsu da sabon tsaron raba kayan agajin jin kai da Amurka da Isra’ila ke shirin aiwatarwa a Gaza. Babbar jami’ar diflomasiyyar kungiyar, Kaja Kallas, ta bayyana cewa Tarayyar Turai ba ta goyon bayan sabon tsarin raba agajin jin kai da Amurka da Isra’ila ke kokarin aiwatarwa wanda ke kaucewa hadin gwiwa da Majalisar Dinkin Duniya da sauran kungiyoyin agaji. Kallas, ta kuma bayyana cewa hare-haren da Isra’ila ke kai wa a Gaza sun wuce abun da suke bukata wajen yakar Hamas, a yayin da adadin wadanda suka rasa rayukansu ke ci gaba da karuwa. Tun bayan da Isra’ila ta dawo da yaki a watan Maris bayan ruguza yarjejeniyar tsagaita wuta da ta cimma...
Dakarun sojojin Najeriya sun dakile wani harin hadin gwiwa da ‘yan ta’addar Boko Haram da ISWAP suka kai a yankin Marte da ke jihar Borno, inda suka kashe wasu da dama daga cikin maharan. Majiyar leken asirin hedikwatar sojan Najeriya ta tabbatar da cewa harin ya faru ne da misalin karfe 1:35 na wayewar safiyar talata 27 ga watan Mayu. Majiyar ta ce wasu ’yan ta’adda da ba a tabbatar da adadin su ba sun kai hari a bataliya ta 50 da ke Marte. Kotu ta ci su El-Rufa’i tarar miliyan 900 Tinubu ya ɗaga darajar Kwalejin Kimiyya ta Kabo Zuwa Jami’ar Fasaha ta Tarayya Dakarun da ke samun goyon bayan wata tawaga ta runduna ta 24 da bataliya ta...
Falasdinawa da dama ne suka ji rauni a jiya Talata a lokacinda yahudawan Sahyoniyya suka bude rumbunajiyar kayakin abinda ga Falasdinawa a garin Rafah na kudancin gaza. Shafin yanar gizo na Afirka News ya bayyana cewa dubban Falasdinawa wadanda suka yi kwanaki 90 basu sami abinci ba saboda rufe kofar shiar da abinci zuwa gaza. Wannan dai yana daga cikin walakanci mafi girma wanda sojojin HKI suka yiwa Falasdinawa a Gaza, tun bayan fara yakin. An kiyasta cewa falasdinawa kimani dubu 180 ne suka fito don karban agajin HKI da Amurka. Sannan jiragen yakin HKI sun yi barin wuta a sama don tsorata falasdinawa masu neman agaji. A yayinda sojojin yahudawa suna harbi a sama don tsoratar da su. Duk...
Gwamnatin kasar Ireland ta yi doka a jiya Talata wacce ta hana a shigar da duk wasu kaya da aka kera a matsugunan ‘yan share wuri zauna da a karkashin dokokin kasa da kasa ake daukarsu a matsayin haramtattu. Mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Ireland ya fada wa kamfanin dillancin labaurn Faransa cewa; Gwamnati ta amince da a ci gaba da yin wasu dokokin da hana mu’amalar kasuwanci da matsugunan ‘yan share wuri zauna da ba su bisa doka, domin an yi su ne akan kasar Falasdinawa.” Daga cikin kayayyakin da Majalisar dokokin ta Ireland ta haramta, da akwai ‘ya’yan marmari da itatuwa. Ministan harkokin wajen Ireland Simon Harris ya fada wa ‘yan jarida cewa, yana fatan ganin...
Sun kara da cewa, kasashen Afirka za su kafe kai da fata wajen mutunta ka’idar Sin daya tak a duniya, da goyon bayan duk kokarin da kasar Sin ta yi na kare ikon ’yancinta da cimma burin sake hadewar kasar, da yin adawa da tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin, kana suka ce, kasashen Afirka za su kiyaye manufofi da ka’idojin yarjejeniyar kafa MDD, tare da kare muradu na bai daya na kasashe masu tasowa da kasar Sin. (Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe...
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da wasikar taya murna ga taron kasa karo na tara na kungiyar yara jagorori na kasar Sin (CYP), wanda aka bude a yau Talata a birnin Beijing. Xi ya jaddada muhimmancin ganin kungiyar ta bi sawun jam’iyyr kwaminis ta kasar Sin a da kuma yaye hazikai masu gina kasa da za su raya hanyar gurguzu mai sigogin kasar Sin. A game da bikin ranar yara ta duniya da za a yi a ranar 1 ga watan Yuni mai zuwa, ya taya musu shiryawa murna a madadin kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana ya mika sakon gaisuwa ga dimbin yara jagororin, da masu dora su a kan hanya, da bangarensu na...
Tabbas a halin yanzu, wasu kasashe ba su ba da’a muhimmanci ba, kana suna ta daukar matakan kashin kai yadda suka ga dama, lamarin da ya sa al’amuran kasa da kasa suka shiga rudani. Dangane da wannan batu, dole ne Sin da kasashen Afirka masu da’a su karfafa hadin kai, su yi adawa da siyasar nuna fin karfi, da daukaka ra’ayin cudanyar mabambantan bangarori masu fada-a-ji a duniya, da kare tsarin kasa da kasa dake karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya. Ta la’akari da yadda adadin yawan al’ummar Sin da Afirka ya kai kashi daya bisa uku na yawan al’ummar duniya, kokarin hadin gwiwarmu tabbas zai karkata duniya zuwa ga turba mai dacewa. (Bello Wang) Daga kanmu, magana ta...
Gwamnatin Jihar Kano ta amince da kashe Naira miliyan dari da hamsin da ɗaya da dubu dari takwas da sittin da uku (N151,863,895.97) domin sake gina wani masallaci da wani matashi ya cinna wa wuta a yayin da jama’a ke tsaka da sallar Asuba a cikin jam’i a Tiga Gadan da ke Karamar Hukumar Gezawa, a watan Mayun bara. Aikin sabunta masallacin ya kunshi gina makarantar Islamiyya tare da ofis da bandaki da kuma rijiyar burtsatse mai amfani da hasken rana tare da tankin ruwa na sama. Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Ibrahim Abdullahi Wayya, ya sanar amincewar sake gina masallacin ya biyo bayan alkawarin da Gwamna Abba Kabir ya yi a lokacin da ya...
Babbar Kotun Musulunci a Jihar Kano ta yanke wa Shafiu Abubakar hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda cinna wuta a wani masallaci a kauyen Gadan, Karamar Hukumar Gezawa, yayin da jama’a ke tsaka da jam’in sallar asuba a ranar 15 ga Mayu, 2024. Harin ya yi sanadiyar mutuwar mutane 23 tare da raunana wasu. An samu Shafi’u da laifuka hudu, ciki har da kisan kai da kuma barna ta hanyar gobara. Baya ga hukuncin kisa, alkali ya ba da umarnin a yi masa bulala 150, tare da biya tarar N1,500, sannan kuma a kwace babur dinsa mai kafa uku, inda za a sayar, a yi amfani da kudin da aka samu wajen gyaran masallacin da ya lalace. Yayin shari’ar, masu...
Wani bafalasdine ya rasa ransa, bayan da harsasai da sojojin yahudawa suka cilla masa a garin Ariha na yankin yamma da kogin Jordan sun fada a kansa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kamfanin dillancin labaran Falasdinawa WAFA ya na fadar haka a yau Talata, ya kuma kara da cewa Mohammed Yahya Asi Jalaytah ya yi shahada ne bayan da albarusan da sojojin suka cilla masa sun fada a kansa sun kuma ji masa munanan raunuka. Labarin ya kara da cewa bayan tsakiyar dare ne sojojin yahudawan suka soma barin wuta da bindigogi da kuma jefa hayaki mai sa hawaye a kan Falasdinawa a garin Ariha, Inda albarusai suka sami Asi Jalaita suka kuma kasashe shi. WAFA...
’Yan sanda sun tsare wata matar aure kan zargin ta da kashe kishiyarta a Ƙaramar Hukumar Daura da ke Jihar Katsina. Mai magana da yawun ’yan sanda a Jihar Katsina, DSP Abubakar Aliyu, ya bayyana cewa matar ta yi wa uwargidarta kisan gilla ne bayan wata hatsaniya da aka samu a tsakaninsu, wanda ya ƙazance har ya kai ga kisa. Amaryar, mai shekara 23 a duniya, ta yi wa uwargida wannan aika-aika ne ranar Lahadi a unguwar Sabon Gari, daura da Makaranta Firamare ta Daɗi. DSP Abubakar Aliyu, ya ce a ranar ce bayan mijinsu ya dawo daga kasuwa ya kai ƙara Babban Ofishin ’Yan Sanda da ke Daura cewa ya iske uwar gidansa kwance a cikin jini. An yanke...
Rundunar ‘yansanda ta fara gudanar da bincike kan fashewar wani abu a mashigar babban birnin tarayya Abuja a kan hanyar Mararaba zuwa Nyanya a ranar Litinin. Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yansandan babban birnin tarayya Abuja, SP Josephine Adeh, ya ce rundunar ‘yansandan ta samu rahoton kiran gaggawa a ranar 26 ga watan Mayun 2025 da misalin karfe 2:50 na rana, dangane da fashewar wani abu a kan hanyar. Sin Za Ta Harba Na’urar Binciken Samaniya Ta Tianwen-2 FCTA Ta Rufe Hedikwatar PDP Ta Ƙasa Saboda Ƙin Biyan Harajin Ƙasa “Bayan samun rahoton, nan take aka tura jami’an sashin warware bama-bamai (EOD) inda lamarin ya afku, cikin gaggawa aka killace yankin da lamarin ya shafa domin tantancewa...

Shugaban Kasar Kenya: FOCAC Ya Samar Da Damammaki Ga Sin Da Afirka Wajen Inganta Hadin Kansu Da Samun Moriya Tare
Shugaban kasar Kenya William Samoei Ruto ya ziyarci kasar Sin daga ran 22 zuwa 26 ga watan Afrilun da ya gabata, bisa gayyatar da takwaransa na Sin Xi Jinping ya yi masa. Yayin ziyararsa, shugabannin biyu sun kai ga matsaya daya kan daga matsayin dangantakar kasashen biyu zuwa hulda mai makoma ta bai daya a sabon zamani. William Samoei Ruto ya shedawa manema labaran CMG cewa, dandalin tattauna hadin kan Sin da Afirka na FOCAC ba samar da wani dandalin mu’ammalar ra’ayoyi kadai ya yi ba, ya kuma shimfida sharadi mai kyau ga bangarorin biyu wajen fidda sabbin damammakin hadin gwiwa da samun moriya tare. Ruto ya ce, FOCAC ya samar da wani ingantaccen dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ya ce: “Ya kamata ku nazarci Shugaban Ƙasa sosai. Za ku iya faɗin ra’ayoyin ku; zai saurare ku, amma a ƙarshe shawarar da zai yanke tasa ce. Ina ganin ya dace mu gane hakan.” Yayin da yake bayani kan taken taron, ministan ya ce Shugaba Tinubu na da cikakkiyar niyya wajen aiwatar da Shirin Sabunta Fata — wanda tsari ne da ya mayar da hankali kan jin daɗin talaka da fitar da cikakken ƙarfin Nijeriya. “Shirin Sabunta Fata na da nufin kawo sauyi mai ma’ana ga rayuwar al’ummar Nijeriya ta hanyar muhimman matakai da za su fitar da cikakken ƙarfin Nijeriya, ta hanyar da ba a taɓa gani ba,” inji ministan. Idris ya bayyana cewa Shugaba Tinubu...
Kasar Uganda ta dakatar da aikin hadin giuwa na soje dake tsakanin kasashen biyu, saboda sukan da jakadan kasar Jamus yayiwa dan shugaban kasar yake kuma goyon bayan wata jam’iyyar adawar kasar. Shafin yanar gizo na labarai Afirka News ya nakalto jami’iyyar shugaban kasar Uganda People’s Defence Forces (UPDF) tana bada rahoton cewa Jakada Schauer na kasar Jamus a Kamfani ya halarci wata taro tare da wata jam’iyyar adawa inda yake sukar dan shugaba Uwere Musevene jan yadda jam’iyyarsu take gudanar da harkokin shugabancin kasar. Kasashen Uganda da Jamus sun dade basu sami irin wannan rashin jituwa ba. Kuma harkokon kasuwanci tsakanin kasashen biyu yakai dalar Amurka miliyon $335 a shekara 2023 kadai. Sai dai muna iya cewa wannan ba...
Kwamishinan ‘yansanda na jihar, CP Bello Shehu, ya ja hankalin al’umma da su guji tashin hankali a cikin gida, yana mai jaddada muhimmancin neman hanyoyin zaman lafiya da bin doka wajen warware matsaloli. Ya gargaɗi jama’a da kada su ɗauki doka a hannunsu domin hakan yana ƙara taɓarɓarewa da tauye adalci. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Babban magatakardar kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikn Na’im Kassim ya bayyana cewa; Idan har gwamnatin kasar ta gajiya wajen yin abinda ya rataya a wuyanta na aiki da tsagaita wutar yaki, to gwgawarmaya tana da wata hanyar da za ta yi aiki da ita akan ‘yan mamaya. Sheikh Na’im Kassim wanda ya gabatar da jawabi a jiya danage da zagayowar cikar shekaru 25 daga korar ‘yan sahayoniya daga kasar Lebanon da gwgawarmaya ta yi, ya jaddada cewa; “Gwagwarmaya ba za ta yi shiru ba, ba kuma za ta mika wuya ba, tana yin hakuri ne saboda ta bayar da Karin lokacin,don haka ya zama wajibi a yunkura.” Sheikh Na’im Kassim ya kuma ce; Gwamnati ce mai hakkin ganin an...
Jaridar ” Up Isra’el” ta buga labarin cewa; shugaban cibiyar Ayyukan Agaji A Gaza” wacce ke karkashin Amurka da Isra’ila” ya yi murabus saboda abinda ya kira rashin gaskiya da ‘yanci a cikin Shirin. Jaridar ta ambato Jake Wood yana cewa; Ba abu ne mai yiyuwa ba a aiwatar da Shirin agaji a Gaza, sannan kuma a ce za a yi aiki da ka’idojin ‘yan’adamtaka, tsaftar aiki, da cin gashin kai, da abubuwa ne wadanda ba zan taba ja da baya a kansu ba.” Wood ya yi kira da a yi ayyukan gabatar da kayan agajin a cikin yankuna masu yawa na Gaza,a kuma a yi aiki da dukkanin hanyoyin gabatar da taimako.” Wood ya bayyana cewa; Tun watanni biyu...
Adadin “nau’i uku na manyan kamfanoni 500” da suka halarci bikin baje kolin a bana ya kai 114, wanda ya kai kashi 55.6 bisa dari. Daga cikin su, akwai kamfanoni 61 dake cikin manyan kamfanoni 500 na duniya, adadin da ya karu da kashi 74.3 bisa dari kan na baje kolin da ya gabata. (Bello Wang, Safiyah Ma) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga Bello Wakili Mataimaki na Musamman ga Shugaban Kasa kan Harkokin Yada Labarai da Ayyuka na Musamman, Mista Tunde Rahman, ya bayyana jerin goyon bayan da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke samu daga cikin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a matsayin shaida mai karfi kan tsare-tsaren da gwamnati ta aiwatar cikin shekaru biyu da suka gabata. A yayin wata tattaunawa da ya yi da Radio Nigeria a Abuja, Mista Rahman ya ce goyon bayan da ke fitowa daga gwamnoni na APC, ‘yan majalisar dokoki da shugabannin jam’iyya, na nuna karuwar amincewa da sauye-sauyen tattalin arzikin da Shugaba Tinubu ya aiwatar. Ya ce wannan ya hada da cire tallafin fetur da daidaita farashin canjin kudade. “Wadannan goyon bayan suna da matukar...
Fastan nan mai suna Rev. Azzaman David, shugaban majami’ar The King Worship Chapel da ke Kaduna, ya rasu a wani hatsarin mota a ranar Asabar yayin dawowarsa daga Makurdi, jihar Benue zuwa Kaduna. Shugaban ƙungiyar Kiristoci ta Nijeriya (CAN) na Jihohin Arewa 19 da FCT, Rev. John Joseph Hayab, ya tabbatar da mutuwar fastan, inda ya bayyana cewa al’ummar Kirista ta yi hasarar babban jarumi. “Evangelist Azzaman ya kasance mai himmar wa’azi, mai kare addinin Kirista, kuma mai fafutukar kare hakkin masu ƙaramin ƙarfi. Rayuwarsa ta kasance cikin jarumtaka da ƙwarin gwuiwa ga gaskiya da adalci,” in ji Hayab. CAN ta yi wa iyalansa, da ‘yan cocinsa, da duk wanda rayuwarsa ta shafa ta’aziyya, tare da addu’ar Allah ya ba...
Kakakin rundunar, Wasiu Abiodun, ya ce an yi garkuwa da Ilya ne daga kauyen Gatawa tare da mahaifinsa. Iliya da mahaifinsa dukkansu daga karamar hukumar Sabon-Birni ta jihar Sokoto. An yi garkuwa da su ne a cikin watan Afrilu, yayin da ‘yan bindigar suka mamaye kauyensu, suna ta harbe-harbe, inda daga nan ne ‘yan bindigar suka yi garkuwa da su. Ilya ya bayyanawa ‘yansanda cewa, ya tsere daga sansanin ‘yan bindigar ne bayan ya yi ta gudu a dajin har na tsawon kwanaki takwas sannan ya hadu da jami’an ‘yansanda a jihar Neja. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga...
Sanata Ali Ndume, mai wakiltar Borno ta Kudu a Majalisar Dattawa, ya yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, bisa bai wa ’yan Arewa mutum 12 manyan muƙamai a hukumomin gwamnati. Ya ce wannan matakin ya gyara rashin daidaito da ake gani a naɗin muƙaman da shugaban ya yi a baya, wanda ya janyo damuwa a yankin Arewa. Halin da fasinjoji ke ciki bayan hatsarin jirgin sama a Ilori Hakar man Kolmani: Jihohin Bauchi da Gombe sun gana da NNPC kan bukatun al’umma A ranar Juma’a ne Shugaba Tinubu, ya sanar da sunayen wasu ’yan Arewa da aka naɗa shugabanni a hukumomi kamar su Hukumar Inshorar Noma ta Ƙasa (NAIC), Shirin Tallafa wa Masu Ƙaramin Ƙarfi na GEEP, da Hukumar Inshorar...

Kafafen Watsa Labarun Isra’ila: Kungiyoyin Kasa Da Kasu Sun Ki Shiga Cikin Shirin Isra’ila Da Amurka Na Raba Kayan Agaji
Kafafen watsa labarun HKI sun ce, Amurka ta bayyana cewa, MDD ta ki aiki tare da kamfanonin Amurka da na Isra’ila domin raba kayan agaji a Gaza. Majiyar ta HKI ta kuma kara da cewa; An jinkirta aiwatar da Shirin na raba kayan agajin saboda wasu dalilai na kayan aiki. Wuraren hudu ne dai aka ware domin raba kayan agajin a kudancin Gaza, an kuma kai shi zuwa mako na gaba. Wasu kafofin watsa labaru sun ambato babban magatakardar MDD yana cewa; MDD ba za ta shiga cikin duk wani shiri a Gaza wanda ba zai girmama dokokin kasa da kasa ba. A cikin wani bayani da wata kungiya mai kula da iyalai a yankin Gaza ta fitar, ta nuna...
Birgadiya Janar Rasul Sanaei-Rad wanda shi ne babban kwamandan sojan kasa na Iran ya bayyana hakan ne a wurin tunawa da zagayowar ranar ‘yanto da garin Khurramshahr daga mamaya sojojin Ba’asiyya na Sadam, a lokacin kallafaffen yaki. Birgediya janar Sanaei -Rad ya kuma yi ishara da ‘yanto da garin na Khurramshar yana mai kara da cewa; yadda al’ummar Iran su ka yi gwagwarmayar ‘yanto da garin Khurramshahr, bayan tsawon shekaru 8 na yaki, ya sa Amurka ta fahimci cewa yaki da Iran yana da tsada da kuma hatsari; kuma da ace sun san za su yi nasara ta hanyar karfin soja da ba su zauna akan teburin tattaunawa ba. Janar Sanaei ya kuma yi kira ga al’ummar Iran da su...
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “A ƙoƙarinsa na yin garambawul a fannin ilimi a jihar Zamfara, Gwamna Dauda Lawal ya biya duk wani bashi a bangaren ilimi da gwamnatocin baya a jihar suka ƙi biya “Rashin biyan kuɗin jarabawar WAEC da NECO ya haifar da koma-baya ga makarantun gwamnati a faɗin jihar Zamfara, wanda hakan ya sa Zamfara ta kasance a baya a fannin ilimi a faɗin Nijeriya. “Da sanin matsalolin da ke tattare da harkar ilimi, Gwamna Lawal ya kafa dokar ta-baci a fannin ilimi a watan Nuwamba 2023, matakin da ya samar da sakamako mai kyau ga bangaren ilimi a jihar Zamfara. “Sama da makarantu 500 ne aka gyara tare da samar da kayan aiki tun bayan...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Hukumar Binciken Tsaro ta Najeriya (NSIB) ta sanar cewa mutanen da suka tsallake rijiya da baya a hatsarin jirgin sama da ya auku a Jihar Kwara suna samun kulawa a asibiti Da yake tabbatar da cewe duka mutanen cikin jirgin horon sun tsira da ransu, Babban Daraktan NSIB, Kyaftin Alex Badeh Junior, ya ce hukumar ta gano katin nadar bayanai daga jirgin, bayan aukuwar hatsarin a filin jirgin sama na Janar Tunde Idiagbon da ke Ilorin, Jirgin, nau’in Diamond, mai lamba BNI, mallakin Kwalejin Koyon Tukin Jiragen Sama ta Ilorin (IAC) ne, kuma ya yi hatsarin ne a yayin atisayen sauka na gwaji, inda ya kauce daga titi, ya yi cikin daji ya lalace fiye da yadda za a iya...
Gwamnatin Jihar Gombe ta sanya hannu kan yarjejeniyar Naira biliyan uku domin gina mayankar dabbobi ta zamani a garin Gombe. Hakan wani bangare ne na shirin inganta kiwon dabbobi da tsaftar abinci da kuma rage matsalolin kiwon dabbobi (L-PRES) wanda Bankin Duniya ke tallafa wa. Shirin L-PRES na da nufin kyautata harkar kiwon dabbobi da sarrafa nama cikin tsafta a jihar. An kulla yarjejeniyar ce tare da kamfanin Lubel Nigeria Limited da wa’adin kammalawa na watanni 9, zuwa watan Fabrairun shekarar 2025. An gudanar da bikin sanya hannu kan yarjejeniyar a ofishin L-PRES da ke G.R.A, a Gombe, inda shugaban shirin na jihar, Farfesa Usman Bello Abubakar, ya bayyana wannan aiki a matsayin babban ci-gaba a jihar. Sojoji sun kashe mayaƙan...
Dakarun sojin Najeriya sun kashe mayakan kungiyar ISWAP guda biyar sa’annan suka fatattaki ragowar da suka kawo hari a sansanin soji da ke kauyen Gajibo da ke Karamar Hukumar Dikwa a Jihar Borno. Wata majiyar daga Zagàzola makama na cewar, ’yan ta’addan sun kai hari kauyen Gajibo ne da misalin karfe 10:20 na daren ranar alhamis, inda sojojin rundunar Operation Hadin Kai suka yi musayar wata da su suka fatattaki maharan da hadin gwiwar dakarun rundunar ta 134 da suka isa garin. A yayin arangamar ’yan ta’addan sun tsere sun bar nau’uka daban-daban na makamai da suka hada da kuma na’urar sadarwa. Rundunar sojin Najeriya na ci gaba da jajircewa wajen ganin ta kawar da ta’addanci, musamman bisa la’akari da...
Mai magana da yawun ‘yansandan jihar, James Lashen, ya tabbatar da cewa an kashe mutane huɗu a harin, yayin da babu wani ɗansanda da ya jikkata a faɗan da suka yi da maharan. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Nijeriya Na Da Karfin Tattalin Arzikin Sarrafa Kayan Dandanon Da Muke Bukata A Cikin Gida – Yahaya Yakubu
Na yi imanin za mu iya hakan Kuma muna fasahar da za mu iya aiwatar da hakan? Idan aka yi la’akari da albarkatun noma da Nijeriya ke da shi, musamman a cikin amfanin gona irin su rogo da rake, da kuma ta hanyar saka hannun jari kan ababen more rayuwa da fasahar kere-kere, akwai gagarumin yuwuwar bunkasa damar samar da MSG na cikin gida ta hanyar amfani da wadannan albarkatun kasa da ake samu. Muna da injiniyoyi da yawa wadanda za su iya gyara injinan. Muna da dukkan abubuwan da ake bukata a Nijeriya don samar da kayan dandano. Yawanci muna samun abubuwan da duk da muke bukata. Idan kana bukatar ruwa mai yawa, muna da madatsun ruwa a Shiroro,...
Babban magatakardar MDD Antonio Guterres ya bayyana cewa; MDD ba za ta shiga cikin duk wani tsari da ba zai girmama dokokin kasa da kasa ba a Gaza. Bayanin nasa dai ya zo ne a matsayin mayar da martani akan maganar da ta fito daga HKI na cewa tana aiki tare da Amurka domin raba kayan agaji a Gaza. Babban magatakardar MDD ya kuma kara da cewa; kaso 80% na yankin Gaza, ko dai yana karashin mamayar Isra’ila da kuma wanda aka bai wa mazaunansa umarnin su fice daga cikinsa.” Antonio Guterres ya yi gargadin cewa matukar ba a bude iyakoki ba, aka kuma shigar da kayan agaji, to mutanen Gaza za su rasa rayukansu.” Babban magatakardar MDD ya tunawa...
A jiya Juma’a miliyoyin mutane Yemen sun cika dandalin ” Saba’in” dake birnin Sanaa, domin nuna cikakken goyon bayansu ga al’ummar Falasdinu. An bai wa gangamin taken: ” Muna tare da Gaza” domin jaddada ci gaba da nuna goyon bayan al’ummar Falasdinu da suke fuskantan kisan kiyashi daga sojojin HKI, da kuma nuna kin amincewa da jefa mutanen yankin cikin yunwa. Masu gangamin sun yi tir da yadda kasashen larabawa da na musulmi su ka nuna gajiyawa da kuma yin abin kunya saboda yadda su ka yi shiru akan abinda yake faruwa da mutanen Gaza. Bugu da kari a yayin wannan gangamin an yi jinjina ga sojojin kasar da suke kai wa HKI hare-hare da kakaba takunkumi akan tasoshin jiragen...
Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Abbas Arakci wanda ya gana da takwransa na fadar Vatican ya yi kira da a kawo karshen laifukan da ‘yan mamaya suke tafkawa akan Gaza da gaggawa a kuma shigar da kayan agaji zuwa yankin. Ministan harkokin wajen na Iran wanda ya je kasar Italiya domin tattaunawar bayan fage da Amurka akan Shirin kasarsa na Nukiliya, ya ziyarci fadar Vatican, inda ya gana da ministanta na harkokin wajen Cardinal paul Gallagher, ya mika sakon ta’aziyyar rasuwar Fafaroma Farancis sannan kuma da murnar zabar sabon Fafaroma Leo na 14 Abbas Arakci ya yi wa shugabannin fadar ta Vatican bayani akan matsayar Jamhuriyar musulunci ta Iran dangane da shirinta na Nukiliya na zaman lafiya, da...
An dai fara goyon bayan tazarcen Tinubu a wurin taron lokacin da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin, ya ce babu wani gurbi a fadar shugaban kasa a 2027. Barau ya ce, “A bayyane yake a 2027, za mu sami gagarumar nasara, In Sha Allah. Don haka, mu ci gaba da hanyar da muke kai. Mu hada kai da juna, mu yi aiki tare da shugaban kasa, mu yi aiki tare da kowa, mu hada kai a tsakaninmu don samun nasarar da ake bukata.” Sanata Barau ya ci gaba da cewa sauya shekan wasu shugabannin jam’iyyun adawa zuwa APC ya kasance sakamakon aikin Shugaba Tinubu a cikin shekaru biyu kawai da ya shafe a kan karagar mulkin Nijeriya. Kazalika, Ganduje...

Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Kara Haske kan Batun Inganta Sinadarin Uranium Da Zamanta Da Amurka
Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta bayyana sabbin ci gaban da aka samu a tattaunawar da aka yi a birnin Roma Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’il Baqa’i ya jaddada cewa: Ana gudanar da zagaye na biyar na tattaunawa ba na kai tsaye ba tsakanin tawagar Amurka da na Iran a cikin yanayi na kwarewa. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya bayyana a yau Juma’a cewa: Tattaunawar tana gudana cikin kwarewa da kwanciyar hankali, yana mai cewa abin da ake yadawa a kafafen yada labarai hasashe ne da baya da tushe ko inganci kuma baya da bambanci da shaci fadi. A yau Juma’a da yamma ne aka fara shawarwarin da ba na kai tsaye ba karo na biyar...
Dakarun sojojin Najeriya na Operation Haɗin Kai da rundunar sojin sama sun daƙile wani harin haɗin gwiwa da ‘yan ta’addar ISWAP suka kai a garin Damboa, inda suka kashe mahara 16 a wani ƙazamin faɗa da suka yi cikin dare. Mai sharhi kan lamarin tsaro Zagazola Makama ya samu labarin cewa, harin ya afku ne a ranar Juma’a, inda aka kai harin da misalin ƙarfe 1:00 na tsakar dare da wayewar garin ’yan tada ƙayar bayan sun kai hari a kan gadar Azir da kuma runduna ta 25 da ke Damboa. An kama jami’in Hukumar NRC da laifin satar waya 2027: ’Yan Najeriya sun yi watsi da takarar Tinubu, sun koka kan tsadar rayuwa Majiyoyin sun ce dakarun da ke...
Daga Bello Wakili Dukkan ‘yan majalisun tarayya daga Jihar Katsina sun bayyana goyon bayansu ga Gwamna Umar Dikko Radda domin ya sake tsayawa takara a wa’adin mulki na biyu karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben shekarar 2027 mai zuwa. An bayyana wannan matsaya ne a lokacin wani taron hadin gwiwa da ‘yan majalisar suka gudanar, inda Honourable Sada Soli, dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Jibia da Kaita, ya yi magana a madadin takwarorinsa. Ya bayyana cewa wannan shawara ta samo asali ne daga nazarin hadin gwiwa da suka yi kan nasarorin da gwamnan ya samu da kuma goyon bayan da al’ummar jihar suka nuna daga kowane bangare. ‘Yan majalisar sun yaba da irin salon shugabanci na Gwamna...
Dakarun sojojin Najeriya na Operation Haɗin Kai da rundunar sojin sama sun daƙile wani harin haɗin gwiwa da ‘yan ta’addar ISWAP suka kai a garin Damboa, inda suka kashe mahara 16 a wani ƙazamin faɗa da suka yi cikin dare. Mai sharhi kan lamarin tsaro Zagazola Makama ya samu labarin cewa, harin ya afku ne a ranar Juma’a, inda aka kai harin da misalin ƙarfe 1:00 na tsakar dare da wayewar garin ’yan tada ƙayar bayan sun kai hari a kan gadar Azir da kuma runduna ta 25 da ke Damboa. An kama jami’in Hukumar NRC da laifin satar waya 2027: ’Yan Najeriya sun yi watsi da takarar Tinubu, sun koka kan tsadar rayuwa Majiyoyin sun ce dakarun da ke...
Mataimakin Daraktan Ayyuka na Operation Haɗin Kai, Kyaftin Reuben Kovangiya, ya tabbatar da kashe ‘yan ta’addan, yana mai cewa Sojojin na ci gaba da kai hare-hare kan ‘yan ta’addan. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Modric, ya lashe kofuna 28 da suka hada da gasar zakarun Turai 6 da Laliga 4 tun lokacin da ya koma Real daga Tottenham a shekarar 2012. “Na zo ne a shekarar 2012 tare da fatan sanya rigar yan wasan da suka fi fice a duniya da kuma burin samun manyan nasarori, Real Madrid ta canza rayuwata a matsayina na dan wasan kwallon kafa da kuma mutum, ina alfahari da kasancewata a daya daga cikin mafi kyawun kulob a tarihi” inji shi. Real za ta bude gasar cin kofin duniya na kungiyoyin kwallon kafa da Al-Hilal ta Saudi Arabiya a ranar 18 ga watan Yuni, sannan kuma za ta kara da Pachuca ta Mexico da RB Salzburg ta...
Arewa Tech Fest, taron koli ne na fasaha da kirkire-kirkire na kwanaki uku, wanda ke tattaro ’yan kasuwa, kwararru masu fasaha, masu zuba jari, da masu tsara manufofi don bunkasa fasahar kere-kere a Arewacin Nijeriya. El-Rufai ne da kansa ya shirya bikin. Minista Tijani, wanda ya gabatar da jawabi mai mahimmanci, ya yi magana a kan sauye-sauye na zamani da kirkire-kirkire a sassan gwamnati da masu zaman kansu na Nijeriya. El-Rufai ya isa wurin taron ne a makare, inda ya nemi afuwar mahalarta taron tare da bayyana cewa ya samu jinkiri saboda wani muhimmin taron siyasa da aka gudanar a yammacin jiya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai...
Ko shakka babu, ba wani tsari ko salon ciyar da al’umma gaba da za a iya cewa zai dace dari-bisa-dari da dukkanin sassan duniya bai daya, amma duk da haka, daukacin kasashen duniya za su iya koyi daga kwarewar kasar Sin, da tsawon lokacin da ta shafe tana gwada dabarunta na ci gaba wadanda suka haifar da da mai ido. Yayin da a nasu bangare sassan kasa da kasa ke da damar tsara manufofi daidai da burikansu da yanayin da suke ciki. Wasu masharhanta na ganin kwarewar da Sin ke samarwa duniya, tamkar sabon zabi ne ga sassa masu fatan gwada wani salo na bunkasa kasashe masu tasowa, wanda ya sabawa na yammacin duniya, don haka sassa daban daban ke...
Nahiyar Afirkan a karkashin tarayyar Afirka ta kafa cibiyar dake kula da sararin samaniya domin tattara bayanai, wacce ke da matsuguni a birnin “alkahira’ na Masar. Sabuwar cibiyar dai ta fara aiki ne a watan da ya gabata,kuma za ta rika musayar bayanan da take tattarawa da cibiyoyin kasashen da suke a fadin nahiyar. Haka nan kuma cibiyar za ta kyautata ayyukanta ta hanyar harba taurarin dan’adam a sararin samaniya da kafa cibiyoyin bibiyar yanayi domin yin musayarsu da kasashen nahiyar da kuma wajenta.
Wani dattijo mai aikin kwashe shara da ya shekara 40 yana tara kuɗin domin zuwa aikin Hajji ya samu cika burinsa a bana. A karshe dattijoin dan qasar Indosauke ya samu damar zuwa sauke farali inda ya isa Kasa Mai Tsarki tare da matarsa. Wanni dattijon wanda ya nuna tsananin juriya da jajircewa ya bayyana yadda kwashe shekara 40 yana tara 1,000 na kuɗin ƙasarsu a kullum, domin tara kuɗin da zai sauke farali shi da mai ɗakinsa. A yayin da ake yake hira da Kamfanin Dillancin Labarai na kasar Saudiyya bayan isarsu ƙasar domin sauke farali, dattijoin ya bayyana cewa tun ashekarar 1986 ya fara tara wannan kuɗi bayan samun goyon bayan matarsa. Dangote ya sake...