Rasha Ta Tarwatsa Mafi Yawancin Tankokin Yakin ” Abrams ” Na Amurka A Kasar Ukiraniya
Published: 9th, June 2025 GMT
Majiyar sojan Rasha ta sanar da cewa; Tun daga watan Febrairu na 2024, zuwa yanzu ta tarwatsa tankokin yaki samfurin ” Abrams” kirar Amurka da ta bai wa kasar Ukiraniya har guda 26. Ya zuwa yanzu adadin wadannan tankokin da su ka rage a tare da sojojin Ukiraniya ba su wuce 5, ba domin adadinsu 31 ne.
Kamfanin dillancin labarun ” Sputnik” ne ya bayyana cewa; adadin tankokin yakin na Amurka da su ka saura a tare da sojojin Ukiraniya ba su wuce 5 ba.
Tun a watan Janairu na 2023 ne dai tsohon shugaban kasar ta Amurka Joe Biden ya sanar da bai wa Ukiraniya tankokin yaki samfurin Abrams a karkashin taimakon kayan yakin da take bai wa kasar.
Dama dai shugaban hukumar leken asirin kasar Ukiraniya Kyrylo Budanov ya sanar da cewa; Wadannan tankokin na Amurka ba za su iya jurewa a yaki ba, sai idan za a yi amfani da su ne a cikin wasu wurare kadan.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Trump ya dakatar da kamen baƙin haure a wasu wurare na Amurka
Shugaban Amurka Donald Trump ya umarci jami’an hukumar kula da shige-da-ficen-kasar da su dakatar da aikin samamen kama baƙin-haure ’yan ci-rani, a gonaki da otal-otal da ma gidajen sayar da abinci na fadin kasar.
Jaridar New York Times ta Amurka ta rawaito ma’aikatar tsaron cikin gida na tabbatar da samun umarnin, wanda aka mika shi ga hukumar kula da shige-da-fice da kuma ta yaki da fasa-kwauri, to sai dai kamfanin dillancin labarai na Reuters bai kai ga tabbatar da sahihancin umarnin ba.
’Yan bindiga sun kashe mutum 100 a Benuwe Wutar lantarki ta kashe mutum 5, ta jikkata 13 a GombeTun a lokacin yakin neman zaben shugabancin Amurka zango na biyu ,Mista Trump ya alkawarta korar bakin-hauren da suka shiga kasar ba bisa ka’ida ba.
To sai dai wannan mataki ya fuskanci kakkausan suka sakamakon yadda ake kame mutanen da ba su taba aikata laifin komai ba, musamman wadanda ke aiki a gonaki da sauran wurare, lamarin da ya janyo barkewar zanga-zanga a wasu sassan kasar.
Rahotanni sun tabbatar da cewa kawo yanzu an shafe kwanaki ana tarzoma a birnin Los Angeles na Jihar California ta Amurka, inda masu zanga-zanga ke dauki-ba-dadi da dakarun tsaron kasa da Shugaba Trump ya tura tun farko domin kwantar da zanga-zangar da ta barke sakamakon kamen bakin haure.